← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 62

Sashe 52

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya tabbatar da Alkari" "Amin Ammi" ya amsa mata sannan sukayi sallama shidai yasan ya fada mata hakanne kawai Dan taji dadi bawai zeyiba Dan anan kusa bashida plan din komawa Nigeria, shirye shiryen yanda Ni'imah da Little ma zasu biyo shi yakeyi bai saniba ko a gaba kadan. Tafiya ya ci gaba dayi har ya karaso wani garden karami inda yawancin mata dalibai na makarantar masu goyo suke zama da yayansu idan babu lecture "HAMDAH " yajiyo wata mata daga bayansa tana fada. A figice ya juya zuciyarsa na bugawa da sauri a ransa yana fata Allah yasa itace sedai koda ya juya wata yar yarinya yagani fara dagani ta hada jinsi da larabawa ko indiawa kodan yanayin mamanta dake yi mata wasa tana kara kiran sunanta HAMDAH love. Lokaci daya komai ya sake dawo masa, yayi kokari ya goge wannan memoryn daga kansa sai gashi yana dawo masa tamakar wanda akeyiwa restore. Ya dade da goge babin soyayyata rayuwarsa ya yarda zuciyarsa Dan mace daya akayita kuma ya rasata Dan haka bashi da wani shiri akan kara karbar wata. Dukda yayi nisa da kowa da komai nasa daya danganci kasarsa ta haihu inda cikon farin cikin nasa take yadai samu rangwamen kashi 40% cikin dari a dole yabar london zuwa China dan gujewa abokansa dasuka san tarihin soyayyar tasa da suke dakon jiran ya dawo tare da Hamdah kamar yanda ya musu alqawari. dukda yasha wahala kafin kuma ya dangana yaci gaba da har kokinsa. A hankali ya dauke idonsa daga kan yarinyar yaci gaba da tafiya saima ya juya da baya kawai Dan yasan koyaje in da zashin baze iya aikata komai ba saboda tunaninta daya addabeshi. *********************** Seda Hajia ta raka su har gida ta qara da musu nasiha sosai sannan ta tafi. Hajara taji dadin dawowarta dan dan sabon da sukayi kafin ta tafi tayi kewarta. Tayi tunanin chanzawar al'amura bayan ta dawo amma ina sema qara lalacewa da sukayi. Tun daga wannan rana Gaba daya rayuwar gidan tayi mata kunci ga kuma azabar laulayi datake fama dashi. Akullum ta Allah se sunyi tashin hankali dashi Dan be haqura ba har gida ya qara dauko wani likitan daban da zeyi aikin Amma taki yarda dama tuni ta dena yarda dashi bare abinda yafito daga hannunsa. Duk wannan zama da sukeyi babu wanda ya sani Dan bata fada ba haka shima to ta Ina ma ze fara fadar wannan ta'asa. Kaman yanda Anty zahra ta saba takan turo mata su Amrah duk qarshen wata wani lokacin ma anan sukeyin weekend wannan watan ma sunzo. Dukda kasancewarsu yara Amma seda suka fahimci akwai matsala tsakanin Antyn tasu da Abokin Daddynsu dan haka da suka koma gida Afrah data fi yar uwarta kaifin hankali da lura, suna zaune bayan sun gama nuna mata kayan da Hamadah ta basu harma da Hajara dan wannan karan tayi abin arziqi ta basu 10k wai su siya sweet ta fara gaya mata "Ummy, Mamy fa bata da lafiya kuma kin san me se uncle yai tayi mata fada kuma fa ita ma cikinta yayi babba kaman naki" se tayi shiru tana karantar yanayin yarinyar, tabbas itama ba tun yauba ta fahimci kamar Hamdan tana da damuwa. Dukda sun kwana biyu basu hadu ba ta fara shanshano matsalar tun lokacin da Aka ce taje gida tayi kwanaki kuma Kwana biyu Hamdah ita ma bataje mata ba haka bata ko kiranta a waya yanda suka saba to Shima Abdurrahman din ya dade beje ko gurin Abban su Amrah. Da wannan tunanin ta kwana washe gari kuwa da sassafe tana kai Yara makaranta ta wuce gidan yar uwar tata maganar cikin da Afrah tace tana dashi ya tsaya mata a rai. Tun kafin ta shiga cikin dakin ta ke jiyo irin bala'in dayake surfa mata hade da cin mutunci, kalmar shi be shirya wahal tawa kowanne shegen Da ba dan haka tunda ta nace seta haifa to ga guri nan Amma karta kuskura ta alakantashi da cikinta ba shiri ta afka cikin dakin cikin tsananin tashin hankali. Abinda ta gani shi ya qara firgita ta, Hamdah na durqushe a kofar toilet cikin Aman da tayi shikuma yana zaune kan gado kamar da kudinsa aka siya yana tijara, bata ko bi ta kan saba ta karasa gurin yar uwar tata tana mata sannu ta shiga qoqarin dagata bata damu da Aman dake jikinta ba. Ko kadan beyi tsammanin zuwan kowa ba duba da lokaci, kamar kazar da aka tsoma a ruwan zafi haka ya miqe yana kame kame ya kasa koda kallonta Dan wata muguwar kunya ce ta kamashi Kaman ya nutse a gurin haka ya ringa ji. Duk da haka be haqura ba se ya fara kame kame "Sannu Bae bari na taimaka miki ki gyara jikinki wallahi amai take tayi na bari ne ta gama sena wanke mata gaba daya" ya nufeta da niyyar dagata. Hannu Zahra ta daga masa tana jifansa da mugun kallo tace "Bata bukatar taimakon ka muda muka damu da lafiyarta muke son cikin jikinta zamuyi mata komai" sum sum ya juya ya fice daga dakin. Ita ta taimaka mata tayi wanka ta hada mata tea me kauri tasha sannan ta kwantar da ita kanta akan cinyarta wani irin tausayin kanwar tata ke shigarta. Cikin kuka Hamdah tashiga bata labarin abinda ya faru "Anty wai seya zubar min da ciki Abdurrahman bashida tausayi. Abinda akan rashinsa na fuskanci wulakanci da cin zarafi rashinsa ya jefani cikin halin da nake ciki a yanzu da ban aure shi ba, akan sa na Rasa Abdul dina sannan yanzu na samu a rabani dashi.....Anty Abdurrahman baya sona tunda bayason haihuwa dani....." Kuka takeyi dagaske dole ta baka tausayi wannan wace irin KADDARAH ce take bibiyarta haka acan an qita saboda bata haihuba anan kuma saboda zata haihun, ita ma Zahra kuka takeyi babu mai rarrashin wani a cikinsu, dakyar tayi shiru ta shiga bata haquri. A gidan ta wunar mata tana kwantar mata da hankali sai dare Abbansu Amrah data kira yazo gidan. Kallo daya yayiwa matar tasa yasan ba kalau ba bai kai ga tambayarta ba cikin kuka tashiga labarta masa duk abinda ya faru da Wanda ta gani. Hankali tashe yake maimaita Kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wannan wace irin masifa ce haka, ashe haka Abdurrahman yake yasa ya wuce masa gaba aka bashi aure a gidan surikansa da suke ganinsa da mutunci wannan ai shi ya shafawa kashin kaji, shi wanne ibtila'ine ya fada masa ma Ace wasu na neman haihuwa da kudinsu shi ya samu ya ki Allah dai ya kyauta. Haka yaringa bata hakuri kamar, roqonsu ya ringayi akan karsu sanarwa kowa a gida insha Allahu zasuyiwa tufkar hanci dan shi besan da wane ido ze qara kallon Surukansa ba idan har wannan magana ta fito, haka suka mata sallama suka tafi. Abu dai kamar wasa se gashi qaramar magana ta zama babba, tun tana jurewa har ta kasa. Tuni magana taje kunnan Maman Abdurrahman din. Ranar kamar zata ari baki tsabar fada, "Wato zama da mahaukata sun washsheka kaima ka haukace ko, ba a haihuwa kai aka haifeka ni dama na dade ina zargin haka ban dai tabbatar bane shi yasa nayi shiru amma yanzu na tabbatar ka haukace yanzu" haka ta ringa sababi data gaji tashiga nuna masa rashin dacewar hakan sedai Kaman ta karawa wuta fetur haka ya koma gida yaringa surfa masifa ranar ba Hamdah ba Hajara ma ta karbi rabonta dan yace ita tavkaiwa Hajiyarsa Gulma, to ko Alhaji zasu gayawa bega uban da ze hanashi abinda yai niyya ba. Ganin kamar ta'ammali da mahaukata yasa shima ya fara taba haukan yasa ta tattara shi ta watsar, in ze kwana yana ihu bazata kulashi ba se tayi kwana uku bata ko leqo palour ta ba bare waje. Ta dai daura aniyar haife ko mene a cikinta koda kuwa duniya zata taru akanta Abdurraan dai Wanda yayi nisa bayajin kira. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Cikin Ikon Allah da ana so da ba'a so Cikin Hamdah dai yashiga wata na biyar kuma zuwa yanzu ta samu saukin laulayi se dan abinda ba'a rasa ba. Tayi kyau kwarai haka cikin yai mata kyau ga jikinta daya qara murje har wani kyalli take yi. Yanzu kam Tsakaninta da Abdurrahman sedai kallo Dan gaba daya ya fita harkarta kwatakwata anata bangaren ita hakan ma yayi mata dadi dan har mantawa takeyi da zamansa a gidan in dai ba haduwa sukayi ba yaringa kallonta kuwa kenan yana hadiyar yawu tareda hararar cikin dayai girma kai bakace wata biyar ne ba, ita dai sedai tace "nan gani nan bari wannan ciki se na haifeshi ya shaqi iskar duniya daga nan nasan inda dare yaimin Dan dama zamansa nakeyi, banzo da ciki ba bakuwa zan koma gida in rainesgi ba" Abdurrahman kam baya tankata sedai yayi murmushi Dan shi kadai yasan abinda yake kullawa zuciyarsa dan bafa wai ya haqura bane, shifa bakin da Hajiyarsa tace zata masa akan cikin ne fa yasa ya daga qafa amma jira yake ta manta ya aiwatar da nufinsa. Tsakanin Dan Adam da zuciyaraa se Allah ana haka a farkon watanta na bakwai a gidan kuna cikinta ya shiga wata shida wata rana tana zaune ya sameta fuska cike da nadama akan abinda ya aikata, cikin lafuza masu taushi ya ringa bata haquri yana cewa "kiyi hakuri Wife wallahi sharrin shaidan ne, dazu ina office naji wani wa'azi da wani malami yayi akan falalar rainon Yaya nima naji ina kwadayin ladan yanzu nayi nazari na gane cewa baiwa ce babba Allah yai mana kuma nagano Gaskiya kiyafemin ina son abi da yake cikin ki zamu raineshi tare insha Allah" haka yayi ta lallabata. Dukda dokin zuciyar data hau da irin tarin haushinsa datake ji akace zuciya bata da qashi sai gashi ta sakko ta kuma yarda musamman yanda ya marairaice yana mata rantsuwa akan ya tuba, nan da nan suka koma normal komai ya wuce tamkar babu wani abu daya taba shiga tsakaninsu. Yanda yake bata kulawa kuwa abin se ya baka mamaki, seda ya tabbatar ya wanke duk wani laifinsa a idon kowa dan har Kano ya dauketa suka je bayan sun dawo ya shiga nema musu Visa akan Dubai
Chapter 52 · 0% Book details