← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 62

Sashe 37

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yanda lokaci daya rayuwarta ta chanza daga farin ciki zuwa akasinsa, ta rame ta fige tamkar wacce ta shekara tana ciwo se uban Haske data qara. Hajjah dai akwanakin ta suma yafi sau dubu Allurar ma ta dena daukarta ga jininta yayi mugun hawa. Aranar kwana uku Khaleefa ya dawo kasar cikin tashin hankali a Instagram yaga labarin mutuwar yana ta trading a farko besan waye ba seda yaga hoton sannan ya shiga dimuwa haka yaita neman Ticket har se yau kwana uku sannan ya dawo yana kuka ya isa gidan yayar tashi nan ya tarar da halin da take ciki abinda ya kara tayar masa da hankali kenan. Anyi sadakar bakwai zaman karbar gaisuwa ya watse, Abbah ya nemi da sursu su tafi da ita gida tayi takaba a acan ganin yanayin da take ciki, Alhaji kamalu da duniya tayiwa karatun Kurma ya yarda cewa babu tabbataccen abu ne ya nemi alfarmar suma da abarta a dakinta zasu kula da ita insha Allahu, har lokacin akwai sauran darajar Abdul a idonsu dukda qasa ta rufe masa ido dole suka barta anan gidan suka bar mata Hamidah da wata kanwar Mumcy da suke cewa Adda Maimu itama mijinta ya rasu ta dan manyanta amma bata taba haihuwa ba su tayata zama. Se a ranar ta koma gidan ta dan Tun bayan Rasuwar anan bangaren take kwana. Dakinsa tashiga, gadon yana nan yanda suka barshi tun waccen ranar haka Daurin dankwalinta daya cire mata batareda ya warware ba yana nan a ajiye akan Bed side drower. Idon tane ya sauka kan brown din hularsa dake ajiye akan mirrow take abinda ya faru a lokacin ya fara dawo mata, lokacin da tacire masa hular tana cewa "Haba Jaan wannan hula ai bata hau ba kwata kwata kalli fa aikin kayanka da kalan takalmin ka koda yake dama naga gayun ya fara sakinka duk ma ka fara tsufa" ta cire sannan ta saka masa Black kalar aikin rigarsa, muryarsa takeji akunnenta lokacin daya ce "Bakomai dama ai ke nakewa gayun nasan kuma kodashi ko babu shi kina sona a haka to bani da wata damuwa ni kam". Seta zauna a gefen gadon a hankali ta rungume hular a kirjinta, A yau ta tabbatar ta rasa mijinta me matukar Sonta da kaunarta, ta yarda Abdulmalik ya Barta bari na har abada se kuma a Darussalam ita dashi, wani kuka ta saki me cin rai da ban tausayi Wanda bata samu damar yinsa ba sai yau. Dole tayi kuka tasan ta rasa jigo a rayuwarta, ta rasa Abdulmalik shekaru hudu da kwana goma da auransu. Lokacin mutuwar ta dawo mata sabuwa. Kukan da batayiba yanzu ta take yinsa. Tafi wata uku cikin wannan halin, damuwa da yawan kukan data keyi ga rashin cin abinci suka haddasa mata ciwo mai tsanani da yai sanadiyyar barin cikin wata uku da batasan tana dashi ba alokacin saura kwana biyar ta fita daga takaba. Sabon tashin hankali wannan karon Hajja seda ta kusan samun paralyse, surutai ta ringayi tana cewa " Allah na tuba, meyasa baka bar mana cikin nan mun samu magajin Abdulmalik ba, Allaj ko baka yarda da nadamar danayi bane kake qara hukuntani haka wayyo Allah na likita kasan abinyi dan Allah" fita da ita sukayi daga asibitin ba shiri ganin tana neman tara musu Jama'a ga sabon da take qoqarin tafkawa. Hamdah kanta tayi kuka data san tana da cikin nan da batayi wasan da zata rasa shi ba, shikenan bata da komai na Abdul se hotonsa kawai. Haka akayi ta bata hakuri qarshe ta dangana dama ba rabon ze taka qasa bane. Kwananta uku aka sallameta bayan dogon jan kunne da gargadin da likita yayi mata akan yawan damuwa, gida Mumcy ta tafi da ita tace sakacine ya jawo har cikin ya zube basu san dashi inda a gabanta take ai da bata barta cikin damuwa ba ko ba komai zata ringa ganin yan uwanta suna rage mata damuwa. Kwananta uku a gida Afeeya tazo mata gaisuwa dayake mijinta ya samu chanjin aiki zuwa kasar America can suke zama yanzu mutuwar kuwa ta dakeshi bana wasa ba, koda suka zo kasa hada ido da ita yai haka ya ringa share hawaye kamar mace. A Maryam da Aysha ma sukaje, haka suka wuni suna aikin kuka babu mai rarrashin wani har dare sannan kowacce ta tafi gidanta Abdulmalik dai ya shude sedai a bishi da fatan samun rahamar Allah. A yanzu bata da wani aiki daya wuce na zaman daki in ba Sallah ba to tana jan carbi ko ka sameta ta rabka tagumi tana tunani Wanda ya zame mata jiki sai anyi dagaske take fitowa cikin mutane saukinta tana Dan cin abinci haka takan danyi magana da su Amrah da Afrah da aka kawo mata hutu ko sa ringa debe mata kewa. Kusan ko yaushe yan gidan su Abdulmalik nakan hanyar zuwa dubata harda Alhaji kamalu da yayiwa kansa karatun ta nutsu da sauran kishiyoyin Hajjah dan mutuwar ta zamar masu ishara. Cikin week end Alh Kamalu ya samu Abba akan maganar rabon gado, be musa masa ba saboda sauke nauyine sun gama tattara komai na Abdul din dan babu me binsa bashi wadanda yake bi ma dukka sun dawo dashi. Ranar Monday sukaje gidan harda Hajja da wasu daga cikin kannensa se Amininsa guda daya bayan sun gaisane Alhajin ya fara yiwa Abba magana akan abinda ya kawosu dan Harda lauyan Abdul din suka taho. Hamidah aka aika ta kirawota suna zaune Anty Bilk isu mayar Yaya Baffa ta tasa ta a gaba akan dole yau se ta danyi kwalliya ko yayane tunda ta gama takaba tuntuni. Bakar Abaya tasaka data kara haska farar fatarta dama ta kara kodewa, batayi kwalliyar ba se lip balm kawai ta saka dole ta baka tausayi Dan gaba daya ta susuce ta fita hayyacinta dakyar take tafiya har ta karasa falon Abbah. Kanta a kasa ta gaida su "Hamdah ya karin hakurinmu?" Hajjah ta tambayeta zuciyarta na Mata kuna gefe daya tana share kwallar data zubo mata na tuno da irin abubuwan data shuka "Alhamdulillah Hajjah" ta amsa mata cikin rawar murya. Shiru sukayi kafin Alh Mansur kanin baban su Abdulmalik ya katse shirun da cewa "Wato abinda ya kawo mu dai bai wuce maganar rabon gado ba domin zartarda umarnin Allah dakuma saukewa Mamaci nauyi Alhamdulillah a tsahon wannan lokaci kuma ya kasance an samu tsautsayin rasa cikin da kike dauke dashi wanda be riga da ya zama Da ba dan haka bashida Gado, kuma mun gama tattara komai mun kuma samu babu wanda yake binsa bashi haka nan duk wadan da yake bi sun dawo dashi. Sannan mun samu wasika rubutacciya acikin aljihunsa wadda ya rubuta da kansa akan cewa Akwai gidansa da yake gimawa a cikin Nasarawa kyautace ke yake ginawa haka motarki dakike hawa da duk wani abu da ya kasance kina amfani dashi nasa to baya cikin kasafin gado kyauta ce yayi miki" daga nan Lawyer ya dora kan yanda rabon ya kasance. Allah sarki dukda kasancewar Abdulmalik yaro matashi saidai ya kasance mai zuciya domin ya mallaki abubuwa da dama nasa na kansa, a ciki ta samu gidaje biyu Banda Wanda ya mata kyauta da fili guda hudu se motocin hawa biyu harda favourite car dinsa sai kudi kimanin Naira Million 9.7 Har suka gama magana kanta yana kasa in banda hawaye babu abinda takeyi ayau ta kara tabbatarwa ta rasa Mijinta Har abada rayuwa kenan abinda bata taba koda a tunani ba yau gashi Abdul yabarta. cikin kuka ta kallesu sannan tace "Abbah na yafe bana bukatar komai Mijina kawai nake so kuma yabarni". "Hakuri zakiyi Hamdah Allah ya fimu sanshi bayanda zamuyi" itama Hajjah kukan take sai gashi mutuwa na neman ta dawo musu sabuwa. Da haka taron ya watse bayan ta danqa komai data samu a hannun Abba shi kuma ya bawa Yaya Baffa. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Addu'ar data dage dayi ta taimaka mata sosai wurin raguwar damuwarta segashi A hankali har ta fara sabawa da rashinsa. Su Malam Hadiza ne suka dameta akan ta koma bakin aikita hakan ze kara sa ta sake da mutane Amma Mumcy tace ta bari se wannan ramar tata ta ragu tukunna. Akace babu abinda ya gagari addu'a sai gashi a hankali al'amuran Hamdah sun fara daidaita ta fara samun nutsuwa a zuciyarta Dan har tana fita waje. Addu'a dai ba fashi kullum cikin yiwa Abdulmalik ta keyi aikin ma ta ajiye acewarta karatu zata koma yanzu ko zata cigaba da aikin bayanzu ba Dan haka Abbah da kansa ya nema mata gurbin karatu a Abu zaria ta fara Masters dinta, saboda yanayin karatun yasa ta komawa Kaduna gidan Anty zahra da zama dan ta sami sauqin zirga zirgar Kano to Zaria hakan kuwa ba karamin taimaka mata yayi ba Dan Hayaniyar yaranma bata barinta yin wani dogon tunani se karatunta data saka a gaba. Shekara kwana tuni ana lissafin wata takwas da rasuwar Abdulmalik. A cikin kudin gadonta ta ware wasu kaso ta gina masa Boreholes, sannan ta cire fili daya daga ciki tayi Foundation ta taimakawa Marayu da fatan ladan ya jewa Abdul din. Ana haka watan azumi ya riskesu dan haka Abbah ya shirya musu tafiya zuwa umara ita da Anty Zahra, Hamidah, Mumcy, Junior se Yaya Abubakar da Matarsa. Sunyi ibadah sosai, rabin addu'ar Hamdah ya tafi gurin nemawa Abdulmalik gafara a gurin ubangiji sai kuma fatan Allah yai mata jagora a rayuwarta ya bata dangana dan ita ko kusa ko alama bata tunanin zata qara sha'awar yin wani auran, acewarta zata zauna ta jira cikar nata lokacin. A duk lokacin da tayi irin wannan maganar se Mumcy tayi murmushi kawai tace "wasa kike yarinya masu Yaya ma suna dan gana suyi auransu bare ke da kike ke kadai" ita sedai ta zumburi baki kawai amma ta sakawa ranta babu wani aure da zata sakeyi. Bayan Sallah da kwana uku ranar wata Alhamis suka dawo Nigeria, a Abuja jirginsu ya sauka kafin suka karaso kano. Tun a cikin jirgi take lura da irin kallon da wani mutumi yake mata da kuma murmushi a duk lokacin da suka hada ido, ko bayan sun sauka a Abuja tana kallon yanda ya ringa binau har seda sukayi
Chapter 37 · 0% Book details