← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 62

Sashe 29

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ma suka koya zakaga kowacce da dafo nata kalar abincin ta kawo saboda yawansu yasa suka rarraba kwanakin da kowacce zata ringa kaiwa amma banda Hamdah da hakan ya zamar mata kamar ibadah. A bangarensa shima abokanan sa da wasu daga cikin kannensa duk anan gurinta suke shan ruwa shiyasa take zama busy sosai a watan azumi seta nemi yan tayin aiki dab ma bata da qiwa ko san jiki ko kadan. Tuni ta tsara ma kanta yanda komai ze tafi ba tareda ya kawomata cikas cikin aikinta ba. Ba kullum take zuwa ba dan haka duk randa zata makarantar to kafin ta fita seta tabbatar ta ci karfin aikinta ya rage qarashe kawai. Kwanci tashi babu wahala se gashi har An kai azumi na goma. A al'adarsu a ranar Azumin goma sha daya a cikin gidan suke shan ruwa gaba dayansu mata da Mazansu. Ranar tun safe gidanta yake a ciki dan kusan duk wadanda suke a nesa nan suka taho aka hadu ana ta aikin abinci. Zainab tazo, tana hakimce akan kujerun palour tana binsu da kallo dan bata san sanda Hamdah ta chanza kujeru ba. Gyashi, hassada nata nuqurqusarta amma babu damar tayi magana dan bata manta da kyakykyawan warning din daya mata akan matarsa ba. Dole tayi shiru amma ta qudiri niyyar ko ba yanzu ba seta gaya mata maganar da tayi niyya. Sun gama aikin tsaf an shiga da komai cikin gida sannan suka fara wanka anan part din nata dai. Khausar ce ta shigo kanta tsaye ta nufi daya daga cikin dakunan Hamdah wanda yake a matsayin master bedroom dinsu. Da kallo ta bita har ta qarasa ta murda handle din kofar sedai tajishi a kulle. "Malama ina key din dakin dan uwana zan shiga nayi wanka". Wani kallon takaici kawai ta bita dashi, wato har rashin mutunchin ya kai tace zata mata wanka a dakin miji dan tana taqamar ita kanwarsa ce? Se kawai ta girgiza kanta tana gyarawa Amir yaron Husna takalminsa. " Wai ke bada ke nake magana bane". Idan Hamdah ta kulata to ku da kuke karatun kuna gurin sema daga yaron da tayi ta nufi dakinta dashi in da Mamansa take. Cikim azama Khausar ta shiga gabanta tana huci kamar wata macijiya "Na rantse da Allah se kinsan ni kika yi wa banza ina miki magana zaki ga abinda ze faru". Fuu tayi waje Zainab ta rufa mata ba. Murmushi tayi bayan da ta sauke yaron hannunta. Tanajin yanda Husna ke bala'i wai meyasa bata mari Khausar din ba ita wallahi bazata dauki irin wannan iskancin na kannen miji ba, yanzu in su akeyiwa nasu iyayen zasu zuba ido ne suna kallo basu dauki mataki ba. Babu wanda ya ce mata qala cikin Matan Yayyen nata da kanne dan gara ita Yar gida ce sukuwa dukka auro su akayi amma kowacce ranta babu dadi. Kusan dukansu sun fuskanci irin wadannan matsalolin amma nata yayi yawa. Kwata kwata Yaran basu da kirki musamman wadannan da suka samu daurin gindin uwarsu. Kayan da zatayi amafani dasu ta diba ta tafi dakin nasa dan tayi wanka. Tana saka kafarta a dakin ta jiyo hargowar Hajja ga Khausar dake rusa kuka kamar wadda aka daka Khairiyya da Zainab na take mata baya se Manubiya dake Faman riqe Hajjan. " Na rantse da Allah Munubiya kika qara cemin wani abu sena saba miki shegiya sallamammiya wato har dake aka hada aka kai sunan ku kan tsauni to ni babu bokan daya iya ya rufemin baki". Wannan magana da taji ta saka ta ajiye kayan hannunta ta fito daga dakin. Kallon Su takeyi daddaya kafin ta sauke idonta akan khausar dake cewa "Hajja daga fa ce mata ke kika aikoni in dauko miki abu a dakin yaya shikenan ta hau zagina harda cewa ko ke baki isa ki shiga dakinnan ba bare wata ni Hajja bakiji irin cin mutunchin data ringayi mana ba wadannan na tayata" ta nuna matan yayyenta dake zaune kamar an dasasu tsabar mamakin karyar da take shararawa. Zainab ce ta amshe da cewa "Wallahi Hajja haka akayi nasan in nayi magana yanzu bansan irin sharrin dazata qullamin a gurinsa ba shi yasa kawai nayi shiru". Kanta a qasa tanajin irin cin mutunchin da Hajja takeyi mata ita da iyayenta. Babu abinda yafi baqanta mata rai irin kalmar Matsafa da take jifan su da ita, wai Mummynta ce Matsafiya sun shanye mata jinin da karshema tace Mayya ce dama tunda taga kyanta tasan Mayya ce ta lashe masa kurwa " waya sani ma ko kwayayen haihuwar taki kika bayar aka miki baqin asiri kika mallakemin Da baya ganin kowa da mutunchi se ke to wallahi ahir dinki tun wuri ki kunce wannan qullin in ba haka ba dakaina zan kunce shi. Gani tayi bazata iya ci gaba da jure abinba. A gaban Faccaloli da Kannen miji ga masu aikin gidan duk da suka shishshigo dan Hajja bata magana a hankali. Mikewa tayi daga durqusan da tayi hawaye naci gaba da ambaliya akan fuskarta ta juya daniyar barin gurin, wasu taurari ta gani a idonta bayan da kunnenta yai mata dum na dan wani lokaci, bazata iya cewa ga aihihin abinda ya faruba. Sama sama take jin muryoyinsu akanta wasu na a kawo ruwa wasu kuma suna cewa akaita asibiti. Muryar Abdulmalik ce abinda taji ta qarshe yana cewa "Me kuka mata me kukayiwa matata? Narantse da Allah senayi sharia da dukkanku in har wani abu ya sameta". Kafin ya dauketa yayi waje da ita. Shan ruwan da ba'ayi a gidan ba kenan kowacce ta tattara ya nata yanata ta tafi gida. Hajja ma part dinta ta koma jiji a matukar sanyaye babu ya Zainab da tuni cikinta ya juya. Batasan meya kaita har ta mareta ba, ta manta yanda hannunta yake ko Namiji ta mara seyaji a cikinsa bare wannan Nunar ranar. Wani irin zafin hannu Allah yayi mata, ko bisa kuskure ta daki abu ji zakayi kamar katako a ka buga maka shiyasa ko laifi yaranta suka mata sedai tasa wani ya dakesu badai ita dakanta ba. Khausar ta kalla sannan tace " Ke kirashi muji suna ina". Kiran Abdulmalik khausar ta shigayi sedai har wayar ta gama ringing be daga ba. Haka tayita gwadawa daga karshe ma ya kashe wayar gaba daya. Mikewa Hajja tayi da niyar daukar Mayafinta su tafi asibitin da tabbas tasan suna can lokaci daya taji wata sabuwar tsanar Yarinyar ta darsu a zuciyarta se kawai ta aje mayafin. "Hajja ya naga kin zauna ba Asibiti kikace zamuje ba" Khausar ta tambayeta. Seta tabe baki sannan tace "Ke dallah rabu dasu sekace wata yar gwal karya ma takeyi da zata wani langwabe taje in ma mutuwa zatayi tayi kowa ya huta". Se suka bita da kallo kawai suna mamakin abinda ya canzata lokaci daya kamar ba Hajjan data gama rikicewa yanzu ba. Munubiya ce ta shiga mata magana akan ya kamata taje yanzu in wani abu ya sameta suce me? " Wallahi Munubiya kika qara magana sena tsine miki kindaiji me nace". Seta mike tsam ta dauki Mayafinta da mukullin motarta tai musu Sallama ta fice dan dama ita kadai tazo tuni ta dena zuwa da yaranta gidan indai ba ya zama dole ba. A cewarta yayanta sun fara girma bazata barsu suzo su koyi irin rayuwar da ake a gidan ba saboda Mata ne, duk masifar Hajja haka ta kyaleta yana daga cikin abinda yasa take qara takurawa Munubiyar dan har cewa take badan suna kama a fuska ba da seta ce musanya mata ita akayi a asibiti. ****************************** Har aka sha ruwa Hamdah na bacci bayan Allurar da akayi mata dan firgita ta ringayi. Ba karamin gigitata Marin yayi ba ita a duniyacma sau nawa aka taba marinta? Shafa fuskarta data kumbura suntum yake a duk minti ransa yana kara baci. Ya rasa me Hajja take nufi dashi, me matarsa ta tsare mata a rayuwa? Ko yau da safe seda ta qara masa maganar aure yai mata shiru to namene kuma da Zata saka yar mutane a gaba shida ya aurota ai shi ya kamata su takurawa ba ita ba. Wuyanta ya taba yanajin yanda zafin zazzabi kebin jikinta wani irin tausayinta ya kamashi. Me zata dorar a zaman gidansa in ba wahala da tsangwamar dangin miji ba?. A asibitin suka kwana bayan ya koma gida ya dakko musu duk abinda yasan zasu buqata dama daga gidan Nasir aka kawo masa abinci. Cikin ikon Allah kafin safiya kumburin fuskar ya sabe haka zazzabin ma babu sedai kanta datace yana ciwo har lokacin, beje office ba yazauna da ita har yamma sannan aka sallameta. A hanya ya siya mata abinci dan bata azumi sannan suka qarasa gidan. Suna shiga ta fara masa kuka, gani take kwana dayan da tayi a gidan kamar ta fita daga ukubar bauta ne gashi yanzu ta dawo. Haka yaita rarrashinta ya bata abinci taci ta sha magungunanta kafin bacci ya dauketa. Gadinta yaringayi har seda yajiyo ana kiraye kirayen salla sannan ya fita dan ya nemo abinda zesha ruwa dashi. Kamar karamar yarinya haka ta dasa kuka lokacin data farka bayanan dan har ga Allah yanzu tsoron zaman gidan takeyi. Abincin hannunsa ya ajiye ya nufeta da sauri ta fada jikinsa tana cigaba da kukan "Shish I got you" ya fada a daidai kunnenta. Setayi shiru kuwa tana sauke ajiyar zuciya. "Shine ka gudu kabarni ko" ta fada a shagwabe. Seda yaja dongon hancinta sannan cikin kwaikwayon muryarta yace "To ba bacci kikeyi ba ni kuma bana so na tasheki tun da kin zama cry cry baby". Seta boye fuskarta a kirjinsa tana murmushi kadan. "Muje kiyi wanka se muci abinci" ya fada yana janta zuwa toilet din. Kamar yar baby haka ya nadot a towel sannan shima yayi wankan. Abaki suka ringa ciyar da junan su har suka gama. Zaman kurame sukayi a gurin ba mai cewa kala kowanne da irin tunanin da yake yi a zuciyarsa, kusan tare bacci ya daukesu wanda basuyi aune ba se ji sukayi ana kiran sallar Asuba. Dore yayi ita kuma ya hanata yin azumi ranar a cewarsa ta bari se jikinta ya warware tukunna dole ta hakura. Karfe shida ya shiga gidan bayan sun gama muhawara da Hajja. Tun bayan sallamar Hamdah
Chapter 29 · 0% Book details