← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 62

Sashe 16

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tunani ba illah GURU Wanda har yanzu bata san duniyar daya ke ba. A kullum ta kwanta seta yi mafarki dashi sedai ko a mafarkin bata samun damar yin magana dashi. Kuka kam ya aureta dan in batayi da yawa ba tayi na awa 3 a rana ita kadai tasan me take ji a ranta. Ina ma zata qara ganinsa ko sau daya ne ta fada masa abinda yake ranta, ina ma zata samu damar bayyana ma sa asirin zuciyarta, sedai lokaci ya qure mata a yanzu. Magana ake ta saura sati biyu daurin auranta da mutumin dayafi kowa sonta, Allah ya sani tana son Abdulmalik amma kuma shiya jarabceta da son Abdul'ahad. "Me yasa ka shigo rayuwata kuma ka fita a lokacin da nake buqatar ka, ina ka tafi ? A ina zan ganka bamu da isashshen lokaci ka dawo Abdul'ahad ina sonka zan aureka". Kalaman da take ta fada kenan kamar zautacciya tana riqe da waya, ta gwada numbers ya fi sau 50 amma dai amsar daya ce a kashe. Kuka ta keyi tamkar wadda iyayenta suka mutu tana fadar maganganun da suka cunkushe mata zuciya seda tayi me isarta sannan ta wanke fuskarta a fampo ta tashi daga gurin kanta na bala'in sara mata. Cikin gidan ta nufa zuwa lokacin jama'ar da suka taru dazu sun ragu sosai se yan uwa najiki da kawayen Mumcy suka rage. Akwatunan da aka jere a gefe masu azabar kyau guda 24 ta kalla se daukan ido sukeyi. Inda a lokacin bayane tabbas data shiga cikin masu kallon kayan anyi da ita saboda sunyi mata irin designer data gaya masa tana so ne latest design amma a yanzu da me kayan, da wadanda suka kawo da masu kallon dukka ta tsani ganinsu. Ji take da za'a barta tsaf zata iya cinna musu wuta su qone kowa ya huta. Da sauri ta nufi staircase jin wata kanwar Abbah tana cewa " Lah ga Amarya zo nan ki kalli abin arziqi yarinya lallai baki farin banza ba wallahi Abdulmalik ya biya Lefe yayi saura Sadaki" a maimakon ta tsaya seta qara wa tafiyarta sauri karshe ma ta hada da dan gudu dan jin wani kukan na neman kufce mata. Kan gadonta ta fada tareda fashewa da Kukan, ita kam ta shiga uku wannan wace irin masifa ce? "Allah ka kawo min agaji, Allah ka kawomin dauki" shi kadaine abinda take maimaitawa. Haka taci kukanta ta godewa Allah har zuwa lokacin da me mata gyaran jiki ta shiga dakin, kamar yanda ta saba haka ta mata anayi tana kuka se lallashinta take a tunaninta ko irin kukan da amare sukeyi ne sedai abinda bata sani ba ita nata ya banbanta dana sauran. A kan gadonta ta tarar da envelope bayan ta fito daga wanka, dauka tayi ta bude tana bin content din ciki da kallo. Pre-wedding pics din da sukayi shekaran jiyane sunyi kyau sosai Masha Allah. Tsura masa ido tayi tana kallonsa, shin menene laifin Abdulmalik? Ta tambayi kanta. "Bashi da laifin komai" zuciyarta ta bata amsa, jiki a sabule ta shiga shiryawa har an kira sallar magrib dan haka tana gamawa ta tada Sallah, ba ta bar kan abin sallar ba har seda tayi Isha tukunna ta miqe saka makon kiran Da Abba yayi mata. A Palour ta same su kusan dukkan yaran gidan Harda Anty zahra data zo tun jiya, wasu set din akwati ta gani a gefe daban da wadan da ta gani a matsayin na lefenta. "Hamdah ga kaya nan ki bude ki gani idan akwai abinda beyi miki ba se ki fada a kara ko a canza miki". Badan Abbah bane yai magana ba abinda ze sakata duba kayan dan duk abinda ya shafi shirin auran nan bata maraba dashi. Akwatunan suka shiga budewa ita da Hamida kayane nasu kyau da tsada kuma choice dinta, tasan aikin Anty zahra ne dan already tasan irin attire din data ke so ta saka ranar auranta. Babu abinda babu a ciki hatta da undies Abbah ya siya mata na fitar biki tamkar yadda yayiwa Zahra lokacin auranta se dai nata har sunf i na zahra saboda zamani ga kuma qarin budi daya samu. " Komai yayi Abbah Allah ya saka da alkahiri Allah kuma ya qara budi" ta fada kanta a qasa. Nasiha ya shiga yi mata cikin nutsuwa irin tasa, Prof Ammani mutum ne me matukar nutsuwa da sanyin hali. Ko kadan bashi da Hayaniya hakan baya rasa nasaba da ilimin dayake dashi ta kowanne bangare. Hafizin alqur'ani ne kuma masanin littattafai da Hadisi sannan kuma riqaqqen dan boko. Har wurin 11 suna zaune a palour tana kallon wayarta na ta ringing an kira yafi sau 20 times amma taqi dagawa, sallama sukayiwa Abban kowa ya nufi makwancinsa. Tanajin Zahra na mata magana akan ana kiranta a waya ta mata banza dan tasan Abdulmalik ne "wai bada ke nake bane tsabar rashin mutunchi a ringa kiranki ba zaki dauka ba". Seda ta buntsura baki sannan ta daga wayar tana qunquni "Babe ina kika shiga tun dazu ina ta kiranki" ya fada ba tare da ya damu da shariyar da ta masa ba. "Bana kusa da wayar ne" ta bashi amsa a tsaye. "Ok I'm sorry ban kiraki tunda rana ba wallahi aiki ne yamin yawa kinga friday zan dauki hutu so i want to finish all my pending works" "Oh Allah sarki" ta fada with i don't care attitude. Se yai shiru na dan wani lokaci aransa yana mamakin meya sameta haka, me yasa take magana kamar ba Hamdan daya sani ba? Daurewa kawai yayi yace mata "Naga kamar baki jin dadi ne ko dama na kirane na tambayeki an kawo kaya in akwai abinda be miki ba a ciki....." "No ba komai fa ni ban ma duba ba in dan wannan ne se da safe bacci nake ji" kit ta kashe wayar. Sororo ya bi wayar hannunsa da kallo he can't believe it she just hang his call. Ahmad bestfriend dinsa daya gamajin duk abinda ya faru ya dafa kafadar sa tare da cewa "Chill Man is just pressure kasan mata da yawa in zasuyi aure suna shiga damuwa so se su ringa juye anger dinsu akan mijin da zasu aura so just be little patience in a week time zata zama taka" wannan ne ya sanyaya masa zuciya har ya shiga imaging irin abunda ze mata in sukayi aure. ********************************** Yammata iya ganinka a compound kowacce ta isa a kalleta. Amarya Hamdah zaune a tsakiyar au Aysha sub tasata a gaba da tsokana wai dai karshen love story ya kuma Bae da Boo zasuyi aute. Babu wanda ta tankawa a cikinsu a zahiri kallon Dan dashe shen Zanen kunshi Baki da Ja da yar Sudan tayi mata take kallo amma a badini zuciyarta tayi nisa da Nigeria ma gaba daya. Yanda take kyalli da daukar ido dole Idan ka kalleta ka Kara abinka da mai kyau ga kuma ingan taccen gyaran Amarchi data samu Dan Anty Amna (kanwar Mumcy)har ma da Anty Zahra basu yi wasa ba sosai suka kara gyara Hamdan tasu. Hamidah ta tsallako mutanen dake zaune ta qara so gurinsu wayarta a hannunta "Yah Hamdah for my whole life banta ba ganin couples dasuka dace da juna ba irinku wallahi kalli nan ki gani" screen din wayarta take nuna mata tana ci gaba da zuzuta irin kyan da Hamdah da Abdulmalik sukayi a pictures din. Karbar wayar Afeeya tayi tareda dropping pictures din a wayarta nan tashiga sharing ma friends dinsu dake wurin harma da wadanda basu zo ba within few minutes pictures suka shiga flying a social media kafin awa daya #*HAMMALIK* sun zama topic of discussion a ko ina. Haka aka ci gaba da guda nar da Hennah event din cikin kwanciyar hankali. Around 6pm Abdulmalik ya qarasa gidan da few of his friends, yayi kyau har ya gaji kana kallonsa ba se ance maka Ango bane bakinsa kaman ze tsage saboda Fara'a. Allah sarki bawan Allah jikinsa har rawa yake daya ganta dakyar Afeeya da Aysha suka fito da ita dan cewa tayi ita kanta ciwo yake bazata iya fita ba. "Look at My Wife Isn't she looking gorgeous" ya fada yana qare mata kallo. "Ai dai Masha Allah kai dai ka haye saura mu amma nima ina ga fa banyi zuwan banza ba" Sagir daya daga cikin friends din Abdulmalik ya fada yana kallon Afeeya da tun fitowarsu ta dauke masa hankali. Haka sukayita wasa banda Amarya data ka bakinta ta gume tana kallonsu daddaya. "Babe menene" ya fada with so much concern. Kanta ta nuna masa, lokaci daya ya rikice ya shiga jera mata sannu yana fadin ko su tafi asibiti ne? Se kuma ya bata tausayi, tayarda Abdulmalik me sonta ne, insha Allahu zata taushi zuciyarta koda pretending ne ta ringayi in tana gabansa. Sallama suka mata yana qara jaddada mata akan tasha magani in kuma bata ji sauki ba zuwa anjima ta kirashi suje asibiti da haka sukayi sallama. Tana yin sallar isha ta kwanta bawai dan tana jin bacci ba Aa sedan gujewa takurar mutane da suka cika musu gida da sunan bikinta. Tuni yan uwa na kusa da nesa suka gama hallara dan a gobe ne za'ayi kamu. Dangin Mumcy na Yola duk sunzo dukda bashi ne bikin ya da zatayi na farko ba amma sun mata kara kwarai dan Hamdah Favourite din kowa ce babu wanda zeso yayi missing auren yar gata. *WAI INA INA LABARIN GURU*?????? Ku biyoni a next page its all about your favourite *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 WACCEN RANAR. Tun bayan daya sauke Hamdah ya bar kofar gidansu gudu yake shararawa kamar me barin duniyar. Tunda yake a duniya mace bata taba ci masa mutunci irin na yau ba, shi mace zata kalla tace waye ze aureshi? Shi zata cewa wai tana da wanda take so? Har ace yayi lalacewar da mace zata kalli idonsa tace bata sonsa? "Illar kula kananan yara kenan" zuciyarsa ta raya masa. Haka ne dan ya tabbatar inda tasan me takeyi bazata kasa gane matsayinsa a zuciyarta ba, ashe hasashen banza yai dayake tunanin gininsa ya isa yabe a cikin zuciyarta. Gefen titi ya faka motar ya kwanta a steery zuciyarsa kamar zata
Chapter 16 · 0% Book details