← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 62

Sashe 11

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

there for you, you can leave now in da flash a hannunki kiyi copying in babu ki tafi da system din but make sure you return it dan ke ba'a baki aron abu ki dawo dashi". Kasakasa ta harareshi sannan tace "Ai wancan ma ba ara nayi ba" "Sata kikayi kenan" ya bata amsa. Bata tanka ba illah mayafinta data ware ta yafa ta suri Laptop din dan bata shigo da flash ba "Ji mana" ya tsaidata. "I like your Dress" kallon kanta tayi, doguwar riga ce Jallabiyya ta mata kirar Oman a jikinta me colar Neck da buttons a hannun kaman links na Maza, rigar ta boye komai na jikinta haka ma kafarta lofers ne Silver dan haka tafin hannunta da face dinta ne kawai a Bude, se kawai ta maida masa da "Thank you, you Look Good also". Ta juya ta fita. Kamar soko yaringa murmushi, he is seeing progress in the relationship Allah dai ya ida nufi. Gida ta wuce kai tsaye ta kwashe komai a System dinta, haka nan ta shiga ta ringa masa bincike pictures dinsa dana familynsa, Friends da dai sauran Hotuna. Babu hoton Single mace in banda na wadanda tasan kannensa ne se kuma wata yarinya daya dataga pics dinta da dan yawa. Ba laifi tana da kyau sedai ba fara bace, to ko ita ce budurwar tasa? To ma ina ruwana? Ta tambayi kanta. Seta koma kan videos, latest movies ta gani ta kwafi son ranta. Bata da abinyi a school ta san kuma ba da wuri ze tafi ba dan haka se karfe hudu ta koma makarantar. A kofar office dinsa ta tarar dashi suna magana da wani Mr Bayero, bayan ta gaishe su ta nemi gefe ta tsaya ya hade rai tsaf yanda ya saba. "shi kuma haka yake, minti kadan yayi dariya minti Kadan Hada rai matarsa ta shiga uku" bata san a fili tayi maganar ba seda taji yace "Thank God kin sani seki shirya". Kallon gurin da yake tayi already Mr Bayero ya tafi dan haka ta bude front sit dinsa ta aje masa Laptop din. "Care for a Ride" ya fada dan yaga sanda me Napep ya ajiyeta. Ba gida tayi niyyar zuwa ba, daganan Hotoro zataje gidan wata kawar Anty Zahra zata karbo ma yaranta kayan da tayi order kuma yau kawai a Adaidaita take son yawo, seta ce "Aa ba gida zani ba ai na gode". "Get in " yai commanding nata, dole ta shiga ya tada motar suka bar cikin Makarantar. Seda yaje Gate sannan ya kalleta "Ina zakije" "Hotoro" ta bashi amsa. "Wacce a ciki" ya qara tambayarta "Maiduguri road wurin Excel Collage". Har suka je dai dai inda ta kwatanta masa ba wanda yayi magana, time to time yakan kalleta ita ma haka. A kofar gidan ya tsaya ta shiga, bata jima ba ta fito da babbar Leda a hannunta. Yana zaune akan moyar yana waya ya hangota, sauka yayi ya karbi kayan ya saka a back seat sannan ya bude mata motar ta shiga suka dauki hanya "se ina kuma" ya qara tambayarta. "Aminu Kano zaka ajiyeni, Hamida tana school bata dawo ba babu kowa a gida gara in je wurin Mumcy mu tafi tare". Dungure mata kai yayi yana murmushi yace "Sannu yar yaye wato gurin Mumcy to bazakije ba gida zan kaiki". Daga nan suka fara yar hira kadan, daidai Alpen store ya tsaya "Amm please Hamdah girlfriend dina ce zatayi birthday so ni gaskiya bansan duk girly girly abubuwan ku ba so i don't know if you can help me choose for her". Bata musa masa ba suka shiga gurin, "ki dibar mata duk abinda kike ganin ya dace dake she is just like you in terms of taste". Kaya ta jida ba kadanba tunda yace Money is not a problem, tun daga kan cosmetics, perfumes, jewerries, chocolates, buscuits babu abinda ta manta. "Harkin gama" ya tambayeta "Aa ka tambayesu inda suke aje shoes da bags da Jallabiyya" murmushi yayi ya kira wani ma'aikacin gurin ya kaisu Sama inda kayan suke. Da "To da Ok" yake binta dan surutu take masa ba kadanba. Duk abinda ta dakko seta nuna masa tayi masa qarin bayani har suka gama. Data gama masa siyayyar yace ta dibar ma kanta taqi se Icecream kawae data dauka Babbar roba daya da Chewing gum Orbit. Trolleys sunyi hudu ta ciko da tarkace shidai ATM dinsa ya bada aka cire kudin aka Loda musu a bot suka tafi. Yana ajiyeta yai mata sallama ta shiga gida shi kuma ya juya dan Magriba ta kawo kai. **************************************** 03 March At exactly 12 o'clock Message ya shigo wayarta "Happy birthday Hayatiii Allah ya mallakamin ke a karkashin inuwar Aure, banida sauran burin daya fi wannan. Enjoy your day have fun to the fullest". Shine abinda message din ya qunsa. Tasan ba Abdulmalik bane dan baya nan then who could it be? Ita shaf ta manta da yau birthday dinta m koma dai waye ta gode. Daga nan kira ya ci gaba da shigo mata dukka na well wishing, seda tayi sallar asuba sannan ta kwanta bacci. Karfe tara take da Lecture Sir Guru, ranar kwalliya sosai tayi kodan its her special day. Bata makara ba course mates dinta nata wishing nata da tambayar ina cake dinsu a haka ya shiga ajin ya samesu. Ranar he seems happy. Class rep ya tambaya meya ke faruwa ya gaya masa that Hamdah Ammani ke birthday kuma bata siyo musu cake ba. Kallonta yayi sannan yace "Lallai kam we need to celebrate daga yau ma ya zama doka duk wanda ke birthday ajin nan ze zo ya kawo mana cake muci tunda bata yi ba i will take responsibility ina zuwa". Fita yayi about 20mins se gashi da katoton cake wani Baker yana binsa a baya harda stool, haka aka Dinga shigo da drinks da snacks kafin kace me class ya zama wani mini joint dan Harda Jam box a ka kunna kida a class din. Duk lecturer daya zo dan yayi magana dayaga Guru seya koma, masu irin halinsa suka joining aka ci gaba da sha'ani sosai. Anci ansha celebrant ta yanka cake da taimakon Sir Guru haka aka tashi taro lpy lecture da baayi ba kenan. Wannan abu yai publicizing relationship dinsu a cikin makaranta duk inda kabi gulmarsu akeyi, wasu suce sun dace yan hassada kuma su kushe. Ranar Da murna ta koma gida to see another surprise waiting for her. Kayan da ta dibarwa Guru a matsayin budurwarsa zatayi birthday su ta gani a gidan wai wani ya kawo mata birthday gift. Tambaya kama ta shata gurin yan gidansu har ta rasa ta wanda zata amsa. Hamida ce tace "Lah yah Hamdah da alama an kusa ture Gomnatin dan Lele". Nan da nan hankalin ta ya tashi, she felt like tana cin Amanar Abdulmalik ne a lokacin tayi wa kanta alkawarin fita daga harkar Sir Guru amma ina washe gari data je office dinsa da niyyar taka masa birke se labari ya sha banban, muqus ya kashe mata jiki da irin kallon da yake mata, se rufe kofar tayi ta koma inda ta fito tana jin haushin kanta da kanta. *************************** Satittika nata tafiya abubuwa da yawa suna ta faruwa, tuni suka fara project dinsu kuma luckly Dr AA ne supervisor dinta dan haka abubuwan sun zo mata da sauki. Shi ya zabar mata topic din on Genetics sannan ya bata duk abinda yasan ze taimaka mata a aikin nata wannan karon yace baze mata ba amma duk inda ya shige mata duhu ta zo ta same shi. A cikin hakan sabo ya shiga tsakaninsu bama Sabo ba dan takanji kaman she fall for his love. Dukda ba wai ta yarda bane tana ta'allaqa hakan da rashin Abdulmalik a kusa da ita dan sati biyu kenan yayi tafiya, ya tafi wani course ba 8 weeks a Morocco hatta wayar ma ba sosai suke samun yinta ba. Ita da Sir Guru be taba furta mata kalmar So ba amma all his actions shows. Yanda yake kula da ita da kaffa kaffa da ita ya isa ya nuna maka nufinsa akanta. Duk wannan zafin kan ya ajiye a gefe duk da halin miskilancin yana nan amma dai da sauki yana sakarwa mutane fuska. Shirye shiryen Exam suke yi, sosai ta dage dan wannan karon tana so ta qarasa shiga first class ne and tasan zata iya. Ko a da dinnan bata so bane but yanzu with Guru's influence tana so tayi. Ya dage akan karatunta shiyake mata tutorials na kowanne course da bata gane ba, tuni Gulma ta fara yawa acikin School Saboda yawan zuwanta office dinshi. Wasu suce Ai soyayya sukeyi wasu ma sunce kawai Yaudararta yake yi yana rage lokaci da ita, a bangarenta ko sau daya bata taba damuwa ba tunda tasan duk rashin kunyar mutum be isa ya tareta ko shi ya fada musu ba sedai a bayan kunnensu. Her First semester result was very successful Ta samu strong 4.89 CGPA dinta 4.75 tasan duk irin wasan da zatayi she will make it to her finals. Allah Allah takeyi ta turawa Abdulmalik dan yana mata bragging da first class ya fita daga university, yace ze gayawa yaransu that Momy ta Kasa Shiga first class ta maqale a 2.1 to dai se dai ya bada labarin wata ba ita ba. LOL Daren ranar suna waya da Abdulmalik, kwana biyu ta rasa me yake damunsa bashida magana seta ta tayashi da addu'a Allah ya bashi ita. Ya ce mata wani lokacin yana ji a jikinsa kaman ze rasata seta ce masa "Haba Abdul kadai san ko mutuwa in tazo bazata dauke ka ta barni ba dan tasan halin da zan shiga na rashinka kama dena tunanin akwai wani abu fa ze raba mu a cikin duniya ko kana da kokwanto a cikin soyyar da nake maka ne?". Ya kan bata amsa da "Ko daya Hamdah na amince kina sona amma kiji tsoron *_RUBUTACCIYAR QADDARAH_* Ubangiji kadai ke iya sauyata. Ina sonki bana fatan Allah ya jarabceni na rasaki na tabbata daga ranar bazab qara moruwaba. Yanzu haka gangar jikina ce a Morocco amma ruhina yana tare dake Hamdah. Wallahi kece rayuwata" kukan Abdulmalik ne ya biyo
Chapter 11 · 0% Book details