← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 62

Sashe 35

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

daddare seda Hajja ta shiga tayi mata cin mutunci hade da zagi na tsamar nama akan rashin halartar ko daya daga cikin shagulgulan bikin da akayi musamman dinner da suka gabatar jiya da daddare wadda ita duk abinda akai ma batasan inda Abdulmalik din ya tafi ba dan ya mata sallama wai ya tafi dinner dama dai daga yana yin shigarsa beyi kama da me zuwa wani abu me muhimmanci ba har ta zauna tana risgar kukan kishi yana can tare da wata ashe shi bawan Allah hidimarsa kawai ya tafi bata ma san sanda ya dawo ba tana bacci se da Asuba ta farka ta ganshi manne a jikinta. Hawayen tausayinsa ne suka shiga sauko mata ganin yanda duk ya fita hayyacinsa sam bazakace Malik bane ne tashen gayu, kyau da Aji. Bayan sun idar da sallah suna zaune zugum, gajiya da zaman shirun tayi seta mike ta shiga wanka dan tasan babu wani aiki da zatayi a lokacin. Tun daran jiya bayan taro ya watse Yan uwa da abokan arziqin da suka zo mata suka gyara mata ko ina tsaf kamar ba'ayi komai a gidanba sannan ga Hamidah kanwarta da Amal, Shukra da Ni'imatullah yaran Munubiya data bari su kwana su tayata aiki da safe. Harta fito daga wankan yana zaune inda ta barshi kamar gunki, kallo daya tai masa gabanta yai wani mummunan faduwa ba shiri ta furta "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" da karfi da har saida ya juya a hanzarce ya kalleta "Babe lafiya?". Bata amsaba swma gefen gado data samu ta zauna zuciyarta na ci gaba da bugawa kamar wadda tayi tsere. Wani irin tsoro ne yake shigarta tareda fargaba Wanda bata taba jin irinsu ba, meya ke shirin faruwa da ita ne? Wai dama haka mata sukeji idan mazajensu zasu qara aure lallai kishi babban abu ne, seta shiga share hawayen daya fara zubo mata zuciyarta na mata quna. Kusa da ita ya koma ya riko hannunta cikin nasa sannan yace "Babe please menene?" Duk yanda taso ta daure seta kasa kawai ta fada jikinsa ta ida sakin kukan me sauti tana cewa "Maleek dan Allah karka juyamin baya kar giyar Amarci tasa ka wulaqantani ban san ya zanyi da raina ba". Bubbuga bayanta ya shigayi yana dan murmushi kafin ya dago fuskarta yace " Babe kishi, keda kika ce mayi hudu ma ina ruwanki shine har kin karaya a guda daya". Boye fuskarta tayi a jikinsa taba sauke ajiyar zuciya shi kuma yana ci gaba da tsokanarta har seda tayi dariya sannan ya taahi da ita a jikinsa. Dakinta ya kaita ya ajiyeta akan Stool shi kuma ya koma kan gado ya kwanta idonsa akan duk wani motsinta. Murmushin Yake kawai takeyi duk sanda suka hada ido. Se tace masa " katashi kayi wanka dan Allah kaga kowa laifina yake gani banaso yau a samu matsala Dan bakaga irin abinda sukayimin ba jiya saboda bakaje gurin dinner din nan ba" se tayi rau rau da ido tana shirin fashe masa da sabon kuka. Murmushin gefen baki yayi yana kada kansa, se ya mike ya isa inda take ya mata peck akan lips dinta sannan ya fice daga dakin. Nasa dakin ya koma ya shiga wankan. A sanyayae take komai har ta gama shiryawa cikin wata hadaddiyar atamfa shareton Pink datai bala'in yi mata kyau dinkin riga da Skirt. Dakin da su Hamida suke ta shiga har sun gama hada breakfast sunyi wanka suna zaune suna hira, fita tayi daga dakin bayan sun gaisa ta koma nasa ta zauna a gefen gadon tana wasa da zoban hannunta har ya fito daga wankan.Ita ta taimaka masa ya shirya in banda kallonta ba abinda yakeyi dan kwalliyar tata ta birgeshi sosai batai auneba se ji tayi ya janyota sun fada kan gadon gaba daya. "Jaan 9:30am fa tayi....." "Shiiiii..." ya katse ta yana ture daurin Dan kwalin dake kanta. Wata irin soyayya yake gwada mata wadda zata iya cewa a zaman auransu shekaru Hudu bai taba kwatanta mata ko kusan irin taba. yanayin surutai da maganganun da yake se suka fara bata tsoro sun wuce ace na shauqi ne. Sun dade cikin wannan halin kafin ya rabu da ita sai ajiyar zuciya da yake saukewa wata na bin wata ya dauki kusan minti goma sannan ya Mike tareda daukanta tamkar yar baby suka shiga toilet din, shi yai mata wanka sannan shima yayi haka shiryawa dakansa ya shiryata tsaf cikin wani hadadden Lace maroon da akaiwa kwalliya da zare golden dinkin riga da skirt. Sosai tayi kyau saboda yawancin lokaci tare sukeyin komai yasa duk wata kwalliyar mata ya iya. Tana zaune tana kallonsa da alokacin bata da karfin tsinana komai se kallo da ido har ya saka Farar shadda kar dinkin babbar riga da tayi bala'in karbarsa, setaga ya qara mata kyau na musamman ga wani kyalli da annuri da fuskarsa take futarwa. Daure duk wani kishi tayi ta karbi hular dayake qoqarin saka wa ta saka masa sannan ta daura masa Agogo. durqusawa tayi ta saka masa baqaqen takalmi sau cikin daya dakko sannan tashiga fesheshi da turare.Wani abun mamaki ko kadan yau seta nemi kishi tarasa gaba daya zuciyarta ta juye inbanda wani azababben tsoro da fargaba da suka cikata (kishin kenan Lol), rungumar dayai mata ce ta dawo da hankalinta sannan ya janyo wayarsa kirar IPhone 11pro max ya shiga daukansu pictures dasukayi bala'in kyau kai kace yaune daurin auransu. Suna tafe yana uploading pics din akan Instagram dinsa da whatsapp tuni mutane suka fara commenting Dan dole su bigeka. Hoton da ya dauketa ita kadai bayan ya sakata yafa mayafi ya uploading tareda yin rubutu akasanshi *_You are my dream come true. I have loved you ever since the day I first met you. Forgive me for days when I fail to make you feel appreciated. Thank you for making me feel like the luckiest man in the world every single day. You never cease to surprise me with all that you can do and all that you can achieve. Thank you for making our married life all that I dreamed it would be. Thank you for filling our home with love and happiness_* *_I love you with all my heart matata yar Aljannah_* *_Ubangiji yayi miki albarka Aishatu Allah ya faranta miki yanda kika Faranta min a duniya da lahira. See you again"_*. A babban falon suka tarar da Ahmad da wasu abokansa guda uku cikin shigar daurin aure nan suka shiga tsokanarta wai uwar gida ran gida ta basu ango haka karsu makara it dai murmushi take tayi suka fita. Har ta juya taji ya riko hannunta wata irin runguma yai mata ya shiga sakar mata hot kisses a kowanne bangare na fuskarta batareda kalmar I LOVE YOU ta bar bakinsa ba. Lamarin nasa yafi kama da na zautacce seta shiga janye shi daga jikinta tayi saurin barin gurin Dan alokacin ji tayi tamkar zuciyar ta zata fado tsabar fargaba ga wani kuka daya taho mata. Bata san tsiyar da suka tafka a bangaren Hajja ba ita dai zata tuna lokacin da taji fitar motarsa cikin wani matsanan cin gudu abinda yake nuna yana cikin matukar bacin rai kenan lokacin suna waya da Mumcy take gaya mata yanayin da takeji a jikinta, murmushi Mumcy tayi sannan tace "Ho Hamdahna wannan ai shine kishin Amma naji dadi da kika iya dannewa kici gaba kinji Allah yana tareda masu hakuri Insha Allah zaki ga ribar hakan a gaba Allah yai muku albarka Allah ya hada kanku ya baku zaman lafiya."Haka tayi ta jero masu addu'oi fitar motar tasa ce ta sakata katse wayar daga nan ta koma dakinta ta kwanta Dan huta gajiyar daya saukar mata aranta tana fadin "O ko ya zaman mu ze kasance oho Allah dai ya bani ikon cinye wannan jarabta" da haka bacci yai awon gaba da ita. Wurin 12pm Su Anty Zahra da matansu Yaya Abubakar da sauran danginta suka karasa gidan. Gaba ki daya layin a dinke yake da jama'a kai kace anan gidan ake daurin auran ko hanyar da zaka ratsa da kafa ma se kayi da gaske. Lokacin da suka isa daidai gate din gidan su Abdulmalik din abun ya daure musu saboda kuka da kururuwar mata dasuke jiyowa daga ciki ga wasu maza da yawa. Se tunaninsu ya basu ko wa rigimarce dai bata kareba tunda halinsu ne masifa da bala'i Dan haka Humaira yar kanwar Abba taa tabe baki tace "Me za'ayi da wannan jarababbun mutane ni wallahi in nice Yaya Hamdah nagama auran haba mutane Kaman dangin shedan" harararta Anty zahra tayi dan haka tayi shiru suka qarasa cikin gidan. Abangaren Hamdah kuwa a gigice ta farka daga baccin data fara saboda wani mummunan mafarki datayi. bugun zuciyarta ne ya kara tsanan ta har tana jin tamkar zata bar kirjinta bashiri ta diro daga gadon ta shiga kiran wayarsa sedai harta tsinke be daga ba, kita taci gaba dayi tana cigaba da maimaita Innalillahi wa inna ilaihi raji'un a wannan halin suka tarar da ita. Tana ganinsu ta saka kuka, Anty Amna ce ta riqeta tana cewa "Ya kuma kuka Hamdah ki bari dan Allah". Seta rungumeta tana ci gaba da kukan, " Anty ku kiramin Abdul dan Allah na kirashi baya dagawa ni shi kadai nake so na gani yanzu". Lallashinta suka ci gaba dayi har tayi shiru daga baya. Suna zaune jugum babu me cewa komai Alhaji Kabiru babban yayan su Abdulmaleek yayi sallama tareda wasu manya daga cikin Familyn, bayan sun basu izinin shiga ne ya kalli Hamdah da harta fada lokaci daya yace "Am in ba damuwa kuzo cikin gida muna son magana dake" suka juya kowa da irin abinda yake cikin zuciyarsa. Dankwalin kanta ta zame sannan ta zura dogon hijabinta har kasa suka nufi cikin gidan. Tundaga kofar data raba parts din suka san ba lafiya ba, kururuwar mata da iface iface ne ke tashi daga cikin gidan se tashin kabbarar da Mazan suke tayi a haka har suka karasa cikin Babban Falon da taraddadin abinda zasu tarar. A tsatstsaye suka taddasu, Munubiya na tsaye akan Hajja tana kuka tana cewa "Hajjah kingani ko kinga abinda nake fada miki kika biyewa Su Hajia Hauwa gashi yanzu sun kaimu sun baro" ta karasa
Chapter 35 · 0% Book details