← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 62

Sashe 38

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

magana da Yaya Abubakar batasan dai me sukace ba yai masa sallama alamar shi a nan ze tsaya. A take taji kawai ta tsaneshi duk da bata san shi din ko waye ba, mutum kamar maye se wani kallon mutane yakeyi.. Haka tayi ta mita ita kadai har suka sauka a Kano. Sati daya da dawowarsu misalin karfe 8pm suna zaune a falo suna hira khalifa ya shigo "Ke kije kinyi bako a waje" ya fada yana kallon saitin da Hamdah take zaune. Banza ta masa dan ta tsani abinda ake mata, shikenan saboda mijinta ya mutu se akace musu zata saurari kowa ne? Tsabar rashin sanin ya kamata acewarta kenan har wasu daga cikin Abokanan sa ne sukazo wai neman auranta kamar dama jira suke ya mutu su ce suna sonta. Duk ranar da akayi sallama da ita kwana take tana kuka gani take kamar taci amanar soyayyar Abdul in har ta saurari wani namiji bayan shi, taya ma zata yarda wani ya keta Gonar Abdulmalik? "Ba dake ake magana bane Hamdah" muryar Mumcy ta katse mata tunani, seta daga kanta ta kalleshi tareda maka masa uwar Harara kamar idonta ze fado. "Madam ya da Harara daga fadar saqo ai bani na turo shi ba shigowa zanyi na ganshi a compound kin san kuwa yana da matsayi tunda har aka shigo dashi cikin gida ba irin zawarawanki da suke layi bane kike saka Sa'idu yana Fafararsu bane". Kalamansa sun mata daci, wai zawarawanta yanzu fa itama ta shiga sahun zawarawa kenan ko sunan da ta tsana a rayuwarta, nan da nan idonta ya kawo kwalla, seta kalleshi sannan tace "Lallai Khaleefa ka rainani ni zaka kalla kace wai zawarawa suna min layi ina sakawa ana korarsu koda yake ba laifin ka bane, da ace mijina be mutu ba da babu wanda ya isa yai sallama dani" kawai ta saka musu kuka. Duk se sukayi jugum suna kallonta, to shi meya fada da yayi zafi haka har zatayi kuka? Se ya matsa kusa da ita ya zauna sannan ya fara magana "Kiyi hakuri Yaya Hamdah ba abinda kike tunani bane wallahi ni wasa kawai nake miki amma kiyi hakuri bari naje nace masa ya tafi baki nan" ya mike ya da nufin fita daga palourn. Yaya Baffa da shigowarsa kenan ya tsaida shi dan shi ya aiko shi ya kirata. "Hamdah bakiji wani yana jiranki a waje bane kika zauna kinawa mutane kuka kega matar Mamaci ko, to tun wuri ki koma sensea dinki dan babu wanda ze zauna yana kallonki da qananun shekarunki kice bazakiyi aure ba tun wuri ki tashi ki fita tun kafin na saba miki". Tasan halinsa sarai bashida wasa seta mike tana ci gaba da kukan tana kallon Mumcy da taqi cewa komai. " A haka zaki fita kanki ko dankwali babu" ya katseta, seta juya dakinta kawai aranta tana ayya na irin wulaqancin da zatayiwa koma wanene. Kayan jikinta ta cire ta canza da baqar Abaya wadda babu ko dingon wata kalar a jiki duk a son ta quntata wa baqon nata, abinda bata sani ba a duk kalolin duniya babu wadda takai baqi yi mata kyau kasan cewarta fara, hula ta saka sannan ta yafa mayafin rigar fuskarta jeme jeme ta fita tana qissima abinda zatayi masa. Yana zaune a rumfar da suke zama ita da Abdulmalik a lokacin Yammatancinta, tsabar samun guri kujerar da Abdul dinta yake zama wacce take kallon Main entrance din gidan anan ya zauna qafa daya kan daya yana kada Key a hannu sa. Baqi ne Amma ba mai duhu sosai ba haka yana da kyan fuska da kallo daya zaka masa ka gane hakan. Kaftan ne a jikinsa light blue dinkin zamani kansa babu hula hakan ne ya kara fito da zallar Quruciyarsa in ba ma tsaurin ido ba ina ita ina wannan "Kedin nawa kike just 25 fa" zuciyarta ta raya mata. Tana kallon yanda yake yaqe mata baki daya hangota, se mike tsaye yana cewa "Barka da fitowa sarauniyar mata". Wani kallon rainin hankali tayi masa kafin ta tsaya kerere akan sa dan maganar sa haushi ta bata dama zuciya a kusa se kawai ta saka masa kuka. "Subhanallahi Hajia Hamdah me kuma ya faru ko sarauniyar dana fada ne ya bata miki rai". A maimakon ta kulashi se ma qara volume din kukanta data yi kara har seda tayi me isarta sannan tayi shiru, kallonsa tayi taga yanda yayi tagumi ya zuba mata ido kawai Kaman ya samu Tv. "Kar ka kara zuwa gidan nan inma kuma kazo to ka tabbata gurin wani daban badai ni ba saboda ni nagama kula kowanne da namiji a rayuwata in ma baka sani ba to Bazawara ce ni na taba aure kuma mijina ya mutu ya tafi da dukkan wata soyayyaya ta tun wuri kasan inda dare ya maka ka samawa kanka lafiya ka ka rabu dani" tana gama fada tayi gaba abinta ba tare da ta jira jin ta bakinsa ba. Se kawai ya bita da kallo kalmar bazawara data fada tana masa yawo akai dan shi ko kadan be zaci ba budurwa bace ba, koma dai yaya take ya riga da ya fara sonta kuma sonta dada fizgarsa yake musamman ma yanzu daya ganta gata gashi, Kansa ya shafa yana murmushi, a fili ya furta "Dole na same ki yammata Dan ban taba neman wani abu na rasa ba Hamdah" sannan yaja kafafuwansa ya fita yana ta faman doka murmushi kamar sabon wawa. A tsakiyar palour ta zauna kamar karamar yarinya tana kuka tamkar yau Abdulmalik din ya rasu, ido kawai suka sa suna kallonta gefe daya kuma dukka ta basu tausayi Dan ko ba'a fada ba sunsan kukan me takeyi, haka ta kusan raba daren ranar tana yi mutuwa kenan mai tonon asiri badan ita ba me ze hada ta da wani har ya biyota gida wai da sunan soyayyah da haka bacci ya dauketa, Hutun da bata karasa ba kenan ta tattara ta koma Kaduna sedai a banza Dan yanda kasan an budewa samari bama masu mata ba kofar zuwa gurinta haka suke ta tururuwar zuwa gurinta ita kuma tace kuka Salamu alaikum. Sau dari namiji ze mata magana sau adadin haka zatayi kuka a rana duk nacin mutum kuwa haka ze hakura dan bata ko kulasu sedai ka gaji da naci ka tafi in taga mutunchinka sosai nema zata tanka ka harta ce maka tana da Matar aure ce ita. Sun gama lectures se research work kawai ya rage mata hakan yasa kullum tana gida in dai ba wani muhimmin fita ba to zaka sameta a gida tana bacci ko tana karatu. Wata yammacin juma'a suna zaune Yaya Nazir (Mijin Anty Zahra) ya shigo tare da bako, kallo daya tayi masa ta ganeshi wannan mutumin da yaje gurinta a Kano ne me bala'in nacin masifa se a yanzu ta tuna inda ta taba ganinsa ma shine dai wannan mayen me kallon tsiyar da suka hau jirgi daya da Azumu. Yanda suka gaisa da yayar tata ya tabbatar mata Akwai sanayya sosai a tsakaninsu Haka Su Amrah sun sake dashi sosai se murnar tsarabar daya kawo musu sukeyi. A bakin Arif taji sunansa wai Uncle Abdurrahman ga mamakinta ko kadan be nuna wata sanayya a tsaka nin su ba yanda ta basar dashi haka shima ya shareta harya tafi. Bayan da Yaya Nazi ya dawo daga rakashi cikin murna yake gayawa Zahra wai fa Abdurrahman din ya gaya Hamdah kuma yana son ta da Aure bada wasa ba. Cikin jimami tace "Tab Amma dai Daddy kamanta wace ce Hajara ko da har kake tunanin yin jagora ayi mata kishiya koma ba haka ba bana tunanin ma Hamdah zata saurareshi dan kana dai ganin irin tata burzar da ake da ita ta kafe akan ra'ayin bazata sake aure ba". "Ai kinga halin naku tun daga gurinki ma an fara samun matsala yanzu Ina ruwanmu da wata Hajara ita ke iko dashi ko yaya, sannan in ma kina wani tunani duk fada ce ta mutane da ake cewa tafi qarfinsa Amma ba ruwan ta akan fitar da Matan sa sukeyi haline kawai beyi dace ba har yanzu kuma ko zabi aka baki kinsani Hamdah ita ce daidai da tsari da halayyan Abdurrahman". Seda ta danyi Jum saboda kwata kwata ita abin be kwanta mata a rai ba to amma bazaka ja da lamarin Allah na dab basu san meya shirya ba se kawai tace "To Allah ya tabbatar da alkairi Amma nidai ba ruwana karma ka lissafoni a cikin sha'aninku can in sun daidaita falillahi Hamdan". "Yawwa Maman Arif ko kefa Amma da zaki sake mana gwuiwa ko kinawa Aminina bakin ciki samun irin ni'imar da nake ciki ne" pillow ta cilla masa tana cewa "Nidai babu ruwana". Kwana biyu a tsakani Abdurrahman ya kuma dawo bayan doguwar magiya da lallashi aka samu ta fita gurinsa sedai Kaman wancan lokacin yau ma kuka ta tasa shi agaba ta ringa rusawa abin har ya fara bashi tsoro kodai aljanu ne da yarinyar? Haka ya tattara kafarsa ya tafi aransa ko ya kudurce ko kukar bulukiya ce akan ta baze rabu da ita ba. Tun daga ranar ya mayar da gidan wurin zuwansa duk da bata kulashi wataran ma ko fitowa bata yi haka ze gama zamansa ya tafi karshema data gaji ba Wanda ta gayawa se ganin ta sukayi da jaka wai kano zata tafi sanin magiya bazata sakata ta zauna ba yasa suka kyaleta ta tafi. A kanon ma bata sauya zaniba Dan Duk sati yana kan hanya dukda ba fuska yake samu ba Amma bai gajiyawa. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 3 weeks later. Tana kwance daki Dan wunin ranar gaba daya a ciki tayishi, Annur yaron Yaya Abubakar ya shiga da bindigar wasa a hannunsa, kan gadon yayi tsalle ya hau yana mata dariyar sa irin ta yara sannan yace " Mami granny is calling you". Gaba daya Niece da Nephews dinta Mami suke kiranta dan tace bata son Anty Hamdah. Doguwar riga ce me hannun spaghetti a jikinta se ta dora dogon hijabin sallarta har qasa akai ta kama hannun Annur suka fito daga daki. A downstairs ta tarar Mumcy se Ahmad tsohon Aminin Abdulmalik da yazo, cikin girmamawa suka
Chapter 38 · 0% Book details