← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 62

Sashe 28

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nayi alkawarin kulawa dake iya karfin iko na ko akwai ta inda na gaza?" Seta girgiza masa alamar Aa kanta jkinta yayi matukar sanyi, "To karki qara saka wa ranki zan saba wannan alkawarin, ko mata dubu na kawo gidannan kece shugabarsu dan kece zabina. Ke na fara aure, dan haka ko wata zata zo a bayanki take dukda ni banida tsarin mace sama da daya kin sani". Nan gurin take so yazo, setayi saurin damke hannunsa cikin sanyin murya tace "Jaan kishiya fa" kallon rashin fahimta ya mata Dan Haka ta kara cewa "Jaan promise me baza kayimin kishiya ba duk tsanani". Murmushi yayi me ma'anoni da yawa san ma yace "Hamdah, I can't promise you that saboda Bansan KADDARAR da Allah ya RUBUTAMIN ba sedai na miki alkawari for better for worst Ina tareda ke". Yana kaiwa nan ya saketa ya mike dan tuni an kira sallar la'asar. Ita ma sallar ta shiga dakinta tayi, bayan ta idar ta sake wanka dan kayan jikinta dukka sun dameta. Shiru shiru har magriba babu Abdulmalik babu dalilinsa gashi tun yamma aka dauke wuta kuma ba'a kunno Generator ba kaman yanda aka saba. Hijab dinta ta saka har kasa ta leqa inda me gadin su yake zama. Baba me gadi na zaune da yar radio sa a bakin gate yana jin labaran Dare. Cikin matukar girmamawa ya gaisheta dukda ya kusa yin jika da ita, yanda mutumin yake mata har kunya yake bata baya taba bari ta gaishe shi ze fara. " Kiyi hakuri hajia nasan maganar rashin zuwan murja ne yau wallahi ita Maman tasu ce ta tashi da jiki shine ta zauna da dan kula da ita dazu babanta yazo har nan ya gayamin kar aga shiru bata zo ba. Murja Yar Baba me gadi ce. Yarinya ce me matukar nutsuwa. Ita take taya ta ayyukan gida duk wata suna biyanta dan Abdul yace bayasan me aikin kwana yafiso tazo da safe tayi aikinta ta tafi. Se tayi murmushi tace "Ayya Allah ya bata lafiya dana sani ai da tunda rana na shiga na dubata kilan shima baka gaya masa ba nasan da zeyi maganar. Bama zuwanta bane dana naga har yanzu ba'a kunno Gen bane shine na leqo naji ko lafiya". Se ya rike baki yace " Au dan Allah hajia tuba nakeyi, tun da safe Uzairu yazo ya katse wayar dake kawo wuta daga can cikin gidan ban dai masa magana ba na zata ko Alhaji Karami (yana nufin Abdulmalik) ne yace ayi hakan, to kuma yau bamu hadu ba gaskiya naji shigowarsa ina kewaye kafin na fito kuma ya fita sedai in ya dawo ki sanar masa". Cikin gidan ta koma da mamaki, to meya faru aka ciresu daga wutar Injin? Saboda tasan basa matsakar haske dan haka a gidan ko fitila me chaji bata da ita. Se wayarta ta kunna haske tana zaune duk tsoro ya isheta. Kazar data gasa musu tun da rana basu ci ba yace tayi warming base tayi girki ba ze taho musu da fura gashi yanzu babu wuta. Dabarar gashin Foil paper ce ta fado mata ta tashi ta shiga kitchen din ta qara shafe kazar da kayan hadi sannan ta nadeta sosai a cikin foil paper ta zuba ruwa a Pan ta dora. Tana tsaye tana jiran kazar tareda dan jujjuyata dan ko ina yayi zafi a ranta tana takaicin da standard Cooker gas gareta ba wadannan table stove din ba bata da matsalar oven. Duk iyayin Anty zahra ne wai 21st century Gas din ma soft touch. Har ta gama ta sauke ta hada musu duk abinda zasu buqata a kan dining sannan ta tada sallar Ishah. Gaba daya ta gaji da zaman, wayarta ta dauka ta shiga kiran Afeeya dan ta debe mata kewa. Sun dade suna waya kafin sukayi sallama karfe 9pm babu Abdul babu alamarsa se kawai ta shiga game a wayarta tana mamakin ina ya tafi tun la'asar ga shi in ta kirashima se wayar tayita ringing ba'a dagawa. A bangaren Abdulmalik tun bayan daya dawo daga masallaci yana Palour Hajja a zaune. Kansa a kasa ya irga Tiles din dakin yafi sau cikin kwando dan tunda ya gaisheta ta amsa bata kara ce masa ko yaci kansa ba. Seda ta mula dan kanta bayan kusan awa guda sannan tace "Shanyayye sena biyo ka na tambayi result din test din naku kenan zaka kawo min". Beyi magana ba salin alin ya zura hannu a aljihu ya ciro brown envelope din da ko budeta beyi ba tun bayan da Nasir ya bashi ya miqa mata. Seda ta harareshi sannan ta karba ta bude sannan ta warware farar takardar dake ninke a ciki. Tsaf ta karance rubutun ciki bayan wasu yan mintina ta dago ta kalleshi sannan tace " Na gani amma be gamsheni ba dole ka qara aure dan mu tabbatar da lafiyar ka in dagaske ne". Tamkar saukar aradu haka yaji maganar ta, shikenan ta faru ta qare wai anyiwa me dami daya sata. Babu abu daya daya tsinta a cikin babatun data ringayi har ta gama tace ya tashi ya tafi. Kodaya fita daga dakin tsohon dakinsa na Boys quarters ya nufa dan baya jin ze iya tunkarar Hamdah cikin wannan yanayin, gani yake kaman zata gane abinda Hajjan ta fada. Shi taya ma ze fara ce mata wata Hajja tace yayi aure ai abin ma ya zama kamar da hadin baki. Komai na dakin yana nan yadda yake hatta da gadon a gyare yake tsaf se yar qura da gurin yayi, bed sheet din ya yaye ya kwanta kawai ya rasa wanne tunani zeyi a cikin kwakwalwarsa. A cikin dakin yayi magriba da isha duk kiran wayar da takeyi akan idonsa ne amma bashida kwarin gwuiwar dagawa. Har karfe goma yana dakin, Usman dayaji motsi a dakin ne ya leqa yana mamakin waye a dakin Yayan nasu dan sunsan babu wanda yake shiga dan dama Aliyu ne yaso komawa can din to yanzu yana turai karatu. "Yah Abdul kaine a ciki ashe" Usman ya fada cikin Mamakin me Abdul din ya keyi a dakin a wannan lokacin. "Yh nine fita zakayi ne?" Ya tambayi Usman din. "Aa ba fita zanyi ba sedai in akwai wani abu da kake so sena karbo maka". Kudi ya ciro a aljihunsa ya mika masa " Please Fura zaka siyomin in ka dawo ka kai mata gida". Hannu biyu yasa ya karbi kudin musamman daya ga yawansu yasan ragowar nasa ne. Shi yasa yake son Yah Abdul akwai shi da kyauta. "Sallama yayi a kofar palour ta amsa minti daya a tsakani ta leqo dan seda ta dakko hijab dinta a daki, "Yi hakuri Yaya Sadiq" ta fada daidai lokacin data bude kofar. "Au Usman kaine senaji muryar kamar ta Sadiq". Gaisheta yayi sannan ya mika mata ledar Furar. Da mamaki ta karba sedai bata nuna masa hakan ba. "Anty ya akayi baku da wuta inaga dai yaya be sani ba bari na duba ko hanya ce ba'a chanza ba". " Aa Usman base ka wahal da kanka ba connection din Gen din ne ya katse se gobe za'a kira me gyara" Ta fada har lokacin tana mamakin dalilin ciresu daga kan Gen din. "Ok amma da tun dazun ma kika aika ai Uzairu ya iya gyara se yazo ya gyara muku amma bari inna shiga se na turo shi ya duba". " Nagode" ta amsa masa tana murmushi, halayyar Usman sak Khaleefa kaninta shiyasa suke shiri dashi. Sallama ya mata har ta juya ta jiyo muryarsa "Am Anty nace ba" seta juyo tana kallon yanda yake sosa kai. Dariya tayi "Ya akayi?" Ta tambayeshi. "Nace yaushe Hamidah zata zo ne na kwana biyu ban ganta ba kuma ko last week da kika aikeni gida bata nan". Setayi yar dariya, dama tasan baze wuce zancen Hamidah ba dan tunda ya ganta shikenan Usman ya rasa sukuni a dole sonta yakeyi. " Hamidah na Kaduna inaga ma se bayan sallah zata dawo kano tunda sun gama SSCE". Seya bata fuska, "Nidai zan karbi number ta please Anty bari naje na turo miki Uzairun dare yana karayi"." Ok idan ka hadu da Yayanku kace ina jiransa". Sanarwar ganin wata dayaji ce ta sakashi mikewa babu shiri ya nufi gidan, shaf ya manta da wai gobe za'a tashi da azumin ramadan. Shopling din da sukayi niyyar zuwa ma ba a jeba. Har ya gama uzurinshi tana zaune akan gado tana kallonsa. Furar kadai ya iya sha ita ma kadan dan dai kawai zeyi azumi ne. A nata bangaren ido ta saka masa tana karantar yanayin fuskarsa sedai bata ce masa ko kanzil ba har yazo ya kwanta ya juya mata baya tana jinsa se tsaki yake wai zafi. Se kawai ta saka masa kuka dan tunda sukayi aure be taba juya mata baya ba. Kullum a cikin jikinsa yake kwantar da ita koda kuwa ba bacci zasuyi ba. Tashi yayi ya fice daga dakin dan yaje yaga koda abinda ze iyayi ya maida connection din dukda ance masa wai order Hajja ce ta a ciresu daga kan Injin gidan cikin ikon Allah yana kaiwa tsakiyar palour aka kawo wuta. Ruwa ya dauka sannan ya juya dakin. Har ya dawo tana nan inda yabarta tana aikin kuka, tsaki yaja ya dire ruwan kai tsaye ya wuce toilet Dan gaba daya haushin kowa yakeji wai me ma aka mata? Yanajin yanda ta karawa kukan nata volume ganin ya wuce ta dolensa ya juyo cak ya dagata, cikin minti biyu tayi shiru se numfashi da take saukewa. Ranqwashinta yayi ta dafe gurin tana masa kukan shagwaba, get up jor in ba so kike mu rasa azumin ba tashi muyi wanka. A tare suka fito lokacin har wasu masallatan sun fara kiraye kirayen sallah dan haka da sauri suka sha ruwa sannan suka fara Nafila har aka kira sallar asuba suka gabatar. Addu'a suka duqufa yi tundaga wannan dare akan Allah ya biya musu buqatarsu. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Sun shiga watan Ramadana da cikakken yaqinin yayewar damuwarsu. Babu abinda ta fasa kamar yanda al'aar ta take a duk watan azumi, zatayi girki da yawa takai cikin gidan tunda gaba dayansu tare suke shan ruwa. Hakan da takeyi yasa sauran surukan
Chapter 28 · 0% Book details