← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 62

Sashe 49

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dan ta kirawo mata su little. Babbar leda ta cika musu da tarkacen yara irin wadanda take siyawa su Amrah harda turamena atamfofi da riguna yan kanti se Turarukan wuta da kuma kayan gara data zuba mata a bokiti. Sosai Ammi ta ringa godiya haka ta tafi da jimamin yanda Abdul'ahad ze karbi wannan al'amarin, tana fatan ya karbi qaddarar data zo masa da hannu bibbiyu. To her surprise koda ta gaya masa "Allah yasa hakan shi yafi mana alkhairi" kadai ya fada yana murmushi, da Amin ta amsa masa har zuciyarta taji dadi haka ya tashi ya tafi abinda bata sani ba daurewa kawai yayi, dakyar ya qarasa dakinsa ya kwanta yanda yajeji kamar zeyi hauka. Be taba jin kishin wani abu a rayuwa irin yanzu ba yanzu seda ta auri wannan mutumin, ada ya hakura ko ba komai Abdulmalik baya duniya be kuma bar masa wata sheda da zata sa ya ringa tuna wani ya rigashi saninta ba amma yanzu fa a haka ze aureta wata rana su hadu dashi a matsayin tsohon mijinta. "Da kake iqirqrin zaka aureta ce maka tayi zata fito ko yaya" zuciyarsa ta kwabeshi, se ya miqe a fusace, cikin akwatin magungunan Ni'ima ya bude ya nemi wanda ya tabbatar ze saka shi bacci yasha dan yaga alama shima ciwon zuciyar yana barazanar kamashi. ******************************************* *Muleqa Amarya Hamdah* *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Amarya Hamdah ta tare a gidan angonta da yayi matuqar tsaruwa kai da gani kasan an kashe kudi gurin gina shi. Sama da qasa ne matan gidan suna qasa shi kuma me gida a sama sedai kowacce tana da daki a part din nasa. An gwangwaje Amarci kwanaki ukun nan kamar karsu qare a gurin Abdurrahman dan Amaryar ta zarce yanda yai tunani babu sakat ko yaushe yana manne da ita abinda yake qara rura wuta kenan a zuciyar Uwar gida Hajara. Kwanaki sun fara mikawa Dan gashi har ta share watanni uku cikin gidan Abdurrahman. A cikin wannan lokacib ko sau daya bata taba biyewa Hajara sunyi wani sa'insa ba Dan data fahimci halinta mace ce mai sa ido da tsegumi akan abinda be shafeta ba sannan tana da baqin kishi da neman rigima ta wani bangaren kuma tana da sauqi dan idan akayi katari suka hadu a babban palour data mayar gurin zamanta daga safe har dare dan taji dadin Sa ido wata rana har yar hira suke dan ita Hamdah tafi ganewa zaman daki ko part dinta ka shiga bazaka tarar da ita a plaour ba se in baqi tayi ko ita keda girki to shine zaka sameta a babban kitchen tunda tare suke cin abincin dare gaba dayansu. A bangaren Abdurrahman ko bata da wata matsala dashi Dan tsakani da Allah yake kulawa da ita. A koda yaushe kokarinsa ya kyautata mata Kaman yanda itama take masa, ta fahimci yana da son yan uwa dan hak bata gajiyawa da hidimtawa mahaifiyarsa da kannensa da dukkan wani mutum daya rabeshi abinda yake kara mata kima a idanun yan uwan sa da abokansa kenan Dan su sha banban da Hajara domin ita irin matan nan ne da suka dauki miji kadai zaki kyautatawa duk wani bayansa to banzane koda yake mijin ma se a hankali Ai. Shigarta wata na hudu da Aure sabon shafin KADDARAR ta ya kara budewa. Wata safiyar Lahadi ta tashi da zazzabi tareda ciwon kai kasancewar Yana gida ya sakashi saurin daukarta suka tafi asibiti ganin yanda ta galabaita lokaci daya. Suna zaune a office din likitan daya kasance abokinsa tare sukayi karatu shi yayi specializing a bangaren Psychiatry ko zama sosai bata iyayi seda ya jinginata da jikinsa tukunna. Tambayoyi yake yi mata akan yanayin da takeji tana bashi amsa. "When last did you see your period" Dr Hafiz din ya tambayeta lokaci daya zuciyarta ta shiga bugawa, idan bata bata lissafi rabonta da period tun tana sati biyu a gidan yanzu wata uku da kwanaki kenan cikin rawar murya ta gaya masa. kwalba ya bata yace tashiga toilet tayi fitsari ta kawo masa, karba tayi ta shiga bayan yan mintina ta fito ta bashi, jininta ya dauka sannan ya saka ta kwanta a gadon da yake duba marasa lafiya ya jona mata drip saboda jikinta da yayi laushi kafin ya tafi lab running test din. Bayan fitarsa Abdurrahman daya zuba mata ido tun dazu, dakyar ya bude baki yayi magana "Kina kuwa Shan Antibiotic din danake baki?" kai ta gyada masa kawai bawai dan tana sha din ba. Dukda bata san kwayar ta macece ba saboda seya ballo yake kawo mata da ruwa duk sanda zasu kwanta acewarsa wai zatana kara mata kuzari ne kuma shima agabanta yake shan nasa, a farko farko tana sha, period dinta na farko a gidan tayi wani ciwon mara da rabonta da irinsa tun kafin auranta na farko ta kuma zubar da jini sosai data gayawa Mumcy tace mata kodai tana shan wani supplement ne ta dena sai ta tsorata batare da ta gayawa masa ba ta dena sha in ya bata ma sedai ta makale a harshenta ta faki idonsa ta jefar a gefe da safe tayi flushing dinta a toilet. Suna zaune jugum jugum kowa da abinda yake sakawa a ransa har Dr Huzaifa ya dawo. Cikin Fara'a ya miqawa Abdurrahman farar takardar hannunsa yace "Congratulation Man She is 3 month 8days pregnant". Ai kamar wanda aka saka guduma aka rade haka yaji saukar maganar, how is that even possible? Cikin rudi da subutar baki ya juya ya kalli Hamdah data dora hannunta akan cikinta tana shafawa ta kasa koda magana tsabar mamakin wai ita ke dauke da ciki har wata uku bata sani ba.Allahu Akbar ashe rabone me zafi a cikin aurannan. Itama zata zama uwa, zata haihu kamar kowa, dama haka ake jin irin wannan farin cikin? lokaci daya hawaye ya shiga sakko mata Wanda ya kasance na tsantsar farin ciki da murna. Kallonta takai kan Abdurrahman daya bude baki tundazu sedai maganar ta kasa fitowa tsabar yanda ya rude, seta kama nasa hannun ta dora akan dan tudun cikinta da ada take zaton tumbi ta farayi se tace "Ogajee baby...wai babyn ka a ciki na, we are going to be parents soon". Yanayin yanda tayi maganar dole ta baka tausayi domin kana gani kasan zuciyarta cike take da kuncin rashin samun rabon. Daurewa yayi ya hadiye abinda ya hanasa magana tundazu ya dauke hannunsa daga kan cikin kafin yace "Wai dama kina haihuwa?" Seta bishi da kallon rashin fahimta ta kasa magana tsabar mamaki, dama ance masa Juya ce ita ko yaya? Bata dawo daga wancan tunanin da mamakin ba yasake jefa ta a wani, muryarsa ta jiyo yana cewa "Look Huzaifa duk ba wannan ba please lets leave it to Some other time, you know I'm too young to be a Father now so as usual flush it out I'm willing to pay what so ever amount, zan yi tripling maka kudin dana saba biya amma a cire cikin nan kawai". Tsabar mamaki seta kasa motsi, Baki, hanci, ido haka ta budesu idan ta kalleshi seta kalli likitan daya hade hannunsa biyu yana sauraronsa Dan ita sam bata fahimci inda ya dosa ma yau turancinma dena ganewa tayi gara kalmar Acire ciki daya fada daga qarshe ta ganeta amma tana fata bawai akanta yake magana ba. Kallonsa Huzaifan yayi sannan yace "Are you sure you are ok Dr kodai ka fara shan magungunan da kake bawa patients dinka ne kaima taka qwaqwalwar ta buga dan dai na zata ka sauka daga kan wannan muguwar akidar taka?" Kallonrainin hankali yawa Dr Huzaifa kafin yace "Wow see who is talking ai bansan ka tuba da aikata hakan ba kaine zaka ma wani magana akan zubar da ciki, jarirai nawa ka markade a Asibitinnan?" "What ever i did was between me and my Lord kuma Allah gafururrahim ne na tuba ina istigfari ze yafemin" Huzaifan ya bashi amsa. Tabbas gaskiya Abdurrahman ya fada, shi kansa be san iyakar cikin daya zubarba saboda a lokacin yana qoqarin yin kudi kota halin qaqa kuma a harkar likitanci bangare biyunnan sunfi kawo kudi dan haka suka zabi hanyar Bata suci Haram su sami abin duniya shiya na zubarwa da mata ciki Shi kuma Abdurrahman dayake da asibitin mahaukata me zaman kansa sedai abinda duniya bata sani ba behind asibitin nan Dr Abdurrahman qasurgumin dilan kwayoyine, yanda matasa ke tururuwar zuwa asibitinsa kadai ya kamata yasa ayar tambaya akansa amma dayake yanada daurin gindi babu wanda ya taba koda attempting bincikarsa, haka magani indai da sunansa ya shigo kasar nan babu wanda ya isa ya budeshi. "Malam Matar ka ko mata ta infact kai kayi cikin ne ko ni dan haka in zakayi abinda nace kayi kawai in kuma bazakayi ba bakai kadai ne likita kwararre a wannan fannin ba ka sani" yayi maganar cikin halin ko in kula kamar ma besan tana zaune a gurinba. "Ba ko daya a ciki nasan kaima zaka iya Amma ka sani ni na tubarwa Allah tuni na dena bazan kuma kara taimakawa wani wurin aikata sabo ba dan haka bazanyi ba kaman yanda kace akwai likitoci dayawa da aikinsu kenan Abortion you can take her to them". Se a lokacin ta dawo hayyacinta daga hutun rabin gadin data tafi, Ai zumbur ta Mike jin kalmar ABORTION wato dama duk wannan drama akan cikin jikinta sukeyi wae shi za'a cire to meya tsarewa wani daga cikinsu? Hannunta ya kama a fusace suka fice daga office din Huzaifa ya rakashi da "A sauka lafiya" ya kulle kofarsa. Kamar wawuya haka ta ringa binsa har suka zauna a cikin motar se a sannan ta samu damar yi masa magana "Abdurrahman wai maganar me naji kunayi ne nifa ban ganeba" kallonta yayi yana wani mayaudarin munafukin murmushi kafin ya riqo hannunta da dayan hannunsa yana murzawa, se ya mayar da hankalinsa sosai kan titi yace "Cikin jikinki mana Baby a cireshi kawai ko tunda har yanzu ba mu girma ba fara tara yara yanzu ze iya zamar mana cikas cikin jin dadin rayuwarmu ko ba haka ba". "Tunda ya fara magana take maimaita kalmar Innalillahi wa inna'ilaihi raji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni kairan minha" shi take maimaitawa cikin zuciyarta har
Chapter 49 · 0% Book details