Sashe 19
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mata daidai lokacin da feshin turare na farko ya sauka a jikinta, wakar da aka saka mata domin kamun me taken Tazama tazama ita ta kara mata kaimi gurin kukan nata Wanda kowa yadauka a matsayin kukan da yawancin amare sukeyi ne awannan rana sedai a gurinta kukane irin Wanda mace takanyi yayi rabuwa da masoyi. Ta rigada ta cire rai a zuwansa lokaci ya qure mata. Kukan taringayi da tun ana rarrashinta har ta basu haushi suka rabu da ita kowa ya shiga sabgarta ganin babu sarki se Allah yasa tayi shiru tana kallon yanda ake gudanar da shagalin wai duk sabida ita. Masu cin abinci nayi masu rawa sunayi babu wanda ya kuma bi ta kanta.
Zuwan Ango ne yakara ruda gurin nan biki ya dau harami inda ko wanne bangare basuyi wasa ba gurin yiwa nasu ruwan Nairori har ma da daloli. Ranar kam an rubda galan galan na farin ciki, ango yayi rawa ya gyagije ya kuma nunawa duniya yana son Amaryarsa. Ita kanta tayi matukar karfin hali bata sake kuka ba tun bayan da Angon yai mata magana seda Mumcy ta shiga tana mata liqi ne ta samu wannan damar ta rungumeta tareda fashewa da kukan da take sonyi tun dazun, sai bayan isha aka watse daga kamun kowa nawa Amarya da ango fatan alkairi.
Filla filla tayi da kayan jikinta ta shiga wanka ta dauro Alwala, tana idar da sallah ta kwanta dukda baqar yunwar datake ji dan ta manta rabon cikin ta da abinci. Cikin baccinta tayi mafarki daya sakata farkawa A firgice, Abdul'ahad tagani cikin wani mawuyacin hali yana kiranta da ta taimaka masa se miko mata hannunsa yakeyi saidai kafin ta kama hannune Abdulmalik yashiga tsakiyarsu yana ce mata "Haba masoyiyata yanzu har zaki zabi wani akaina bayan tsahon lokacin Dana dauka Ina rainon son ki araina? Ki zo gurina zan baki dukka farin cikin da kike so".
Kallonsa takeyi takuma kalli Abdul'ahad dake fadin "karki gujeni nine masoyinki na hakika HAMDAH kizo" sedai kanta yi yunkurin wani abu Abdulmalik din yaja hannunta suka fara barin wurin. Tana kallonsa ya durkusa a kasa tareda rike saitin zuciyarsa yana numfashi cike da wahala hakan be hanashi kiran sunanta ba. wani irin bakin Amai taga ya farayi Wanda batasan sanda ta fizge daga rikon Malik din ba ta nufeshi sedai kan ta karasa harya cimmata yadagata cak yafara tafiya da ita.
Kiran sunan sa da tayi da karfi tareda sakin kuka ta bude idobta a firgice batasan a fili tayi hakan ba, Zahra da tun farkon fara motsin kanwar tata ta farka tayi saurin rikota tana tofa mata addu'a ganin kaman ba a hayyacinta takeba. Sundauki tsahon lokaci kafin ta nutsu se zufa da take ta sharewa dukda Ac dake kunne har lokacin tana jin sautin muryarsa akunnanta.
"Hamdah meyake damunki na fuskanci tunda aka fara bikinnan bakida walwala Wanda bamuyi tsammanin haka daga garekiba "Zahra tajefo mata tambayar bayan ta bata ruwa ta sha.
"Ba komai Anty me kika gani?"
"Abubuwa dayawa ga kuma mafarkin dakika yi yanzu daya kara sakani a kokonto anya kuwa Baki yankewa kanki danyan hukunciba".
"Kamar yaya kuma Anty?"
"Kaman yanda kikaji na fada mana wai ma sunan wa naji kina kira acikin baccinki?" Ganin tana neman tada zaune tsayene yasaka ta jan bargo sannan tace "Nifa Anty na gaya miki ba komai ni ban ma San abinda kike magana akaiba" ta kara sa tareda rufe har kanta gaba daya. Bata jin zata sake maganar sa da kowa ta daukarwa kanta wannan alkawarin koda kuwa kwana daya zatayi gidan Malik ta mutu zata je. dole badan zahra tasoba ta kyaleta itama ta kwanta ita dai Hamdah baccin da bata koma ba kenan har seda aka kira sallar asuba.
Karfe 11 na safe suka tsaya first transit dinsu, sedai yasan ko tsuntsu ze zama baze isa Nigeria a yau ba Agogon hannunsa ya kalla wanda ya nuna 11am tunowa dayayi da second Transit yakara dugunzuma hankalinsa bashida wani abin daya rage masa Illah addu'a dan yasan a yanayin da ake ciki Allah ne kadai ze iya chanza wannan Al'amari, dole ya tafi inda aka sauke su dan yana buqatar yin wanka da cin abinci. Tunda ya kuma hawa jirgin yake zare ido dan Sosai tafiyar ta kara nisa a idonsa dan gani yake kaman an nunka awanninne sedai abin takaici bayan saukar a Birnin Cairo ya tarar da babu jirgi zuwa Nigeria dole yai jiran awa shida. Kukane kadai beyiba, nemar guri yayi ya zauna yana saka da warwara ganin babu mafita tasa dole yanemi hotel koba komai yarama sallolin da ake binsa kafin ya kara daukar hanya.
A sakko Lafiya Alhaji Abdul'ahad Galdima
A bangaren Handah washe garin ranar suka gabatar da mothers Eve wanda mumcy ta hadawa yar tata. Kwalliyar yau kam Harta fi tajiya kyau wata hadaddiyar Fitted Gown ta saka kalar Blue black me adon silver yayinda angonnata yasaka wata dakakkiyar shadda kalar light Ash dinkin babbar riga. Yau kam yai abin azo a gani dan bakaramin kokari tayi ba ganin ta cire damuwa daga ranta kodan kaucewa kallon tuhumar da Anty zahra take mata se dan har dan qusqua dinnan na Amarya da ango sukayi. Tayi mamakin ganin friends dinta sunsha anko tasan dai ita bata gayya ce su ba, hatta Yan Group din *HAUSA NOVELS DA RUBUTACCIYAR QADDARAH 1 AND 2* yan adawa sunje cin bati suna cin kaza suna bata rai su a dole ba ayi musu daidai ba gashi har wani anko sukayi.
Zuciyar Alhajin su Abdulmalik fa ta danyi sanyi kodan ganin irin dukiyar da Prof ya Narkawa yar tasa tun daga kan furniture dan koshi kansa babu daya daga cikin yayansa data samu irin wadannan kayan duk kuwa da yanda yake zagewa yamusu kaya na bajinta ga uwar Gara treller guda da aka kai aka jibge tsabar sana be harda al'adar fulani ya aro wadda sujewa uwar miji gado uban miji kuma lefe a cewar Prof yayiwa Dr Maryam kara hakan kuwa ba karamin dadi yaiwa Alhaji Kamalu ba, hankalinsa be tashi ba seda yaga yanda harkokin bikin suke ta wakan. Be tsinke da lamarinba se sa lokacin da Excellency Governor yakirshi yake shaida masa zuwan me girma shugaban kasa daurin auran Dan nasa wanda uban Amarya ne ya gayyatoshi da kansa kuma ya amsa tuni ya koma se yan idanuwa ya rainawa kansa aji da kansa. Ashe shi duk burgar banza yake Masu iko na inda suke, a sannan ya kara yarda da lamarin na Prof yakuma yarda base ka nunawa duniya kana dashiba duniyar da kanta take dagaka ta nuna ka in har ka isa.
Wata irin faduwar gaba ta cinci kanta ciki, wai yau wannan dare shine darenta na karshe cikin gidansu a matsayin budurwa wai a gobe ake shirin mikata ga wani a matsayin miji, kawai seta mike da gudu tayi dakin Abbah inda ta tabbatar zata samu Mumcy a lokaci, ko takan mutanen dake tambayarta inda zata batayi ba ta shiga dakin.
Jikin Mumcy ta fada tareda sakin kuka me tsuma zuciya tana fadin "Mumcy na fasa wlh na fasa auran kuma yar musu da komai nasu nidai zan zauna dake" tausayin Yar tata ne ya kamata take itama tafara hawayen dan harga Allah duk cikin yayanta tafison HAMDAH soyayyarta daban ce cikin zuciyarta kodan ance yaron da yafi kiriniya yafi shiga ran mahaifa?
Abbah daya fito daga toilet ya dade yana kallonsu ganin kukan nasu bana kare bane yasashi matsowa yace "toh ya isa haka mana haba Maryam keda zaki rarrasheta kuma seki bige da taya ta kukan uhm"
"Hamdah na bakison mu samu ladan da kowane iyaye ke samu a lokacin da suka aurar da yayansu?"
Sassauta kukan nata tayi ta amsa shi da "Ina so mana"
"Yauwa toh kidena kuka kiyi kokarin gurin amfani da duk nasihar da mukayi miki ki kuma kara da hakuri da juriya Insha Allahu zakiyi Nasara a rayuwarki"nan suka shiga karayi mata nasihohi masu ratsa jiki tareda tsoratar da ita akan masifar dake tattare da sabawa miji.
"Karki amfani da damar cewa yana son ki ki wulakantashi ko ki tsallake umarninsa Allah ba ruwanshi da wannan ze hukun taki dai dai da lefinki" cewar Mumcy tana shafa lallausan gashinta daya sha gyara yana fitar da wani fitinannen kamshi.
"Nidai akarshe zan ce miki rayuwar mahaifiyarku tazame miki abar koyi Dan nasan inhar zaki kwatanta hakan to lallai zaki samu makullin aljannarki tun a duniya Kaman yanda na mallakawa Maryam dita nata "Abban yafada yana kallon Mumcy cikin sigar tsokana daga nan suka cigaba da yar hirarsu har bacci ya dauke Hamdan.zata tasheta ne yace
"Haba Haj ki kyaleta yau daya dai shekaru nawa rabon da ku kwanta gado daya da ita yau na yafe ki kyale yata taji dumin mamanta na yau kafin itama ta tafi inda zata fara bautar nata yayan"
Sai taji sababbin hawaye na zubo mata dole ta gyara mata kwanciya suka kwanta ranta fal da tunani tareda kewar Yar tata.
"Allah ya shigar dake a sa'a ya sa dawwa mammen gidan zamanki ne Yata".
"Amin" prof ya Amsa mata daidai sanda yake gyara pillow akan Sofa inda zai kwanta.
Asuba ta gari iyalan gidan Prof.
*RUBUTACCIYAR QADDARAH*
*By Maryamah*
2020
*PAGE* 1
Karfe shadaya daidai na safiyar ranar lahadi 7th October dubban mutane suka shaida daurin auran *Abdulmalik Kamal Dala da Hamdah Ahmad Ammani* akan sadaki Naira dubu 100 kacal. sanarwar daurin auran tayi daidai da isowar Abdul'ahad a matukar galabaice saboda tafiya beko hutaba saukarsa kenan a Aiport ya garzaya gurin, dakyar ya isa bayan doguwar tafiyar kafar daya sha saboda hanyar a cike take babu ta inda abin hawa ze wuce. Sunan Allah ya shiga kira yana dafe da kansa dake barazanar rabewa biyu yai zaman dirshan a gurin dayake komai yana rabe masa uku uku. "Yah Allah ban butulce ba me yasa ka jarabceni ta haka, Allah meya sa ka hanani ita" kalaman dayake fada kenan cikin fitar hankali tuni hawaye suka gama wanke masa fukarsa. "Yan zu kin tabbata batawa ba shikenan na rasa Hamdah" ya fada da qarfi yana qara rushewa da kuka me ban tausayi. Kallonsa mutane suke wasu da tausayi wasu kuma suna mamakin zallar wautar sa, akan mace zezo da mutuncinsa yana kuka a cikin ja'ama me hakan ze amfana masa bayan aure dai an daura, wasu ne suka shiga dagashi suna bashi baki akan yayi hakuri ya qaddara cewa ba matar sa bace tun usuli kar yayi sabo se Allah ya bashi wata data fita alkhairi. "Babu bana tunanin har akawi wata mace da za'a musanyamin da ita da zata fi Hamdah, ku taimaka k
u roqeshi ya barmin ita na tabbatar da nafishi buqatarta wallahi ku taimakeni". Se kuma suka fara masa kallon zautacce dan sunga abin nasa kuma ya zarta na hankali, ta ya zaayi mutum daga daura masa aure ya sakar maka matar ka aura dan haka kawai suka fara fashewa suka barshi a gurin. A cikin Haka Yusuf ya biyo ta gurin idonsa yasauka kan abokinnasa dake kuka tamkar Ammi ta mutu. Cikin matukar mamaki ya qarasa kusa dashi ya ma kasa bude baki yai masa magana, wai yaushe ma yadawo daga ina yake yanzu wama ya gaya masa ana daurin auran? Tambayar daya ringa wa kansa kenan amma babu damar yinta a lokacin dan haka ya shiga kokarin dagashi subar gurin dan tuni wasu har sun fara video Abin mamaki.