← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 62

Sashe 32

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ga wasu mutane Hajja tace a bude musu gidab zasu zuba kaya kuma dai ba yan uwan Anty Hamdah bane. Wannan wace irin rayuwa ce ace wai namiji za'ayiwa auran dole wai shi wane irin iyaye Allah ya bashi ne? Shi dama Alhaji Ba'a maganarsa Dan tunda magana ce ta kudi tuni an wuce gurin a bangarensa. Wani irin buguwa zuciyarsa tayi ganin motarta ajiye a harabar gidan yasan yau karyarsa ta kare bashida wata kalmar daze iya kare kansa a gurin Hamdah. Se yau yake Dana sanin boye mata da yayi tunda farko daya sanar da ita abinda yake faruwa kilan da abin yazo masa da sauki. Be ko bi takan matan dake palour ba duk da yanda suka shiga tsokanarsa wai ga Ango. Shidai ya dade bega marasa zuciya irinsu ba, har gida yaje ya kaftawa Ita Amaryar da uwarta warning akansa amma basuji ba to zega ubanda ze shigo masa da ita cikin gida a matsayin mata. Badan akwai abinda yafisu muhimmanci a gurinsa yanzu ba da babu abinda ze hanashi tsayawa ya musu rashin mutunchi se sun kwashe duk abinda suka kawo. A corridor suka ci karo da ita tana kokarin fitowa shi kuma ze shiga yanayinta kadai ya tabbatar masa da cewa aikin gama ya gama. Da dakyar ya lalubo miyau ya jika makoshinsa sannan ya nufeta da niyyar yarike ya lallasheta yanda ya saba amma ina yau kam ya makaro. Cikin wani irin zafin nama taja da baya tana masa mugun kallo har lokacin hawaye basu dena fita daga idonta ba. Kara kusantarta yayi cikin muryar tsawa ta dakatar dashi "Don't you dare lay your filthy hands on my body". Se ya tsaya cak zuciyar sa tashiga double flipping, wani irin tashin hankali da fitina ya hango a cikin kwayar idanunta Wanda be taba saninta dasu ba. Yasan za'ayi haka se yayi saurin ja da baya ya sakawa kofar key tayanda ba yanda zata iya fita sannan ya nufota cikin kasa da murya yace "Please Hamdah kisaurareni kiji wallahi ki yarda bansan komai akan maganar auran nan ba yanda kika gansu nima haka nagansu......" "Kai dallah rufe min baki munafukin Allah ni zaka yaudara da roman baki? To wanda kayu a baya ma Allah ya sakamin a tunaninka har Akwai wata kalma taka da zata kuma yin tasiri akaina ne? Never" Ta katseshi. Ko kadan beji haushin maganar ta ba dan yasan he deserve morethan that kokarin sa kawai ya isa gareta ya rike ta ajikinsa ya rarrasheta Amma taki bashi damar hakan. Gaba daya ta birkice masa ta tashi daga Hamdah daya sani takoma wata daban, jifan sa ta shigayi da duk abinda yazo hannunta bakinta be gaji da fadin Allah ya saka mata ba abinda yake qara dugunzuma hankalinsa kenan dan yasan tabbas ya zalinceta. Hamdah nada zafin kishi amma tana da fahimta. Bakowacce mace bace zata iya saurararka a wannan yanayi dan haka kawai ya kai zuciyarsa nesa yana jin yanda take jifansa da kalmomin da ya tabbatar in a hayyacinta take bazata kirashi ko da makamantansu ba. Kokarinta kawai ta kai ga kofa ta fita Dan Ta rantse bata kara kwana cikin gidansa. Dambe suka shiga yi ganin zata bata masa lokaci yasa mata karfi ya riqeta kam a jikinsa sedai fa a banza dan ayau duk wata dabara tasa da wani salo baiyi tasiri akan ta ba dan taki responding in banda duka da yakushi ba abinda take kai masa tana kuka kamar ranta zefita."Ka sakeni Abdul ko in kashe ka in kuma kashe kaina". Babu shiri ya saketa ta zube a gurin tana ci gaba da kukan. "Nace maka ka budeni na tafi wallahi gidan mu zani na gama auranka" ta qara fada cikin muryarta data dashe tsabar kuka. Gefen gadon ya zauna ya rike kansa dake barazanar tarwatsewa, wannan shi ake kira da goma da ashirin wai shin Ina ze saka kansa? Yabarta ta tafi gida tace me? Kawai ta dawo ta tarar ana jerwa Amarya kaya acikin gidanta? Me yan uwanta zasu daukeshi ya gaza sauke amanar daya karba kenan. Kallonta yayi yanda ta hada kai da guiwa tana kuka mai ban tausayi, tabbas yasan be kyauta mata ba Amma yaya zeyi? Haka nan ko a tunani be taba kawo zuwan irin wannan rana a cikin rayuwarsu ba Amma yaya zeyi da *_RUBUTACCIYAR KADDARAH_*? Wayarsa dake aljihuce ta shiga ringing amma ya shareta dan ayanzu bayajin ze iya magana da kowa ganin me kiran ya nace ya sakashi zaro wayar abin haushima unknown number ne dan haka ya danna kawai ya dora akunnansa batareda yayi magana ba "Hello dear ya zakayimin haka Dan Allah gashi ance ko kayan dakinma basu gama samun guri ba bayan ita Matar ka dakuna nawa ne da ita agidan da ni zaka bani wannan Dan akurkin meyasa bazaka sakani a upstairs din ba aini Amarya ce.." Wani tuquqin bakin ciki ne ya taso masa, wato duk kashedin daya mata be shiga kunnenta ba kenan shine zata kirashi. "Se kizo ki fitar da ita ai kisaka naki kayan Idan ubanki ne ya gina min gidan mahaukaciya kawai" kit ya kashe wayar tareda yin cilli da ita ta fashe. Sororo tayi da waya a hannu Hajia Hauwa dake gefenta kuma duk taji maganar tasa tayi saurin tareta da cewa "Karki damu kidai bari a daura daga shi har Matar tasa se sunyi bayani Dan bakida bukatar wata mai aiki ita kadaima ta isheki shiyas nace mubarta a gidan kar a fidda ita daganan kinga bakin ciki seya yi ajalinta. "Amma Momy kina ganin abun nan ze yuwu kuwa kiga fa uban aikin da akayi akan mutumin nan amma kullum kamar dada ingizashi akeyi" ta tambayi uwar tata. "Kiji ki da shirme in aiki be ci shi ba ai yaci Uwarsa ko bagashi ta daga hankali an saka lokaci ba, ai takanta zamubi tunda yaba mata biyayya ayita ingizata tana sakashi yayi ita kuma kinsanni zan iya yin komai Dan ganin nasiyo miki mutunchi a gidan aure" shewa suka dauka kamar wasu kawaye daga nan suka cigaba da shirye shiryensu. **************************** Duk yanda Abdulmalik yayi zaton lamarin nata ya zarce haka Dan yanda sukaga rana haka suka ga dare a gidan haka nan suka kwana tana surfa masa tsiya duk kuwa da irin nasiha da fadan da Mumcy da Abbah suka ringa mata ta waya sannan suka ce ahir dinta suga qafarta a gida. Tayi kuka har ta gaji tayi alqawarin shida zaman lafiya kuwa sedai a labari haka ta ringa caza masa kwakwalwa hatta da gadon da ze kwanta yayi bacci ruwa ta debo bokiti guda ta juye masa aka yana kwance, dole ya koma cikin mota yabarta bayan ya kulleta ta waje. Bayan ya dawo daga masallaci ya lallaba ya shiga gidan, tana kwance daidai kofar idanuwanta sunyi fada ta rame lokaci daya. Kokarin dagata ya shigayi a hankali dan karya tasheta sedai ya makara karaf ta bude ido ta kalleshi. Bude baki tayi daniyyar yi masa rashin kunyar data saba yai saurin matse mata bakin yana aro duk wata jarumtarsa ya bata fuskafa. " Wallahi kika kuskura kikamin shirme sekinga abinda zanyi miki ke bar wannan ma kika qara magana ban yafe ba". Se kawai ta saki kuka, muguntar har ta kai haka ya cuceta ya kuma hadata da Allah. Har suka isa toilet ya direta sannan ya shiga hada mata ruwan wanka. "Kiyi maza kiyi wanka ki yo alwala na baki minti goma ki qara akan hakan ki gani" ya fada fuskarsa babu alamar wasa. Haka tayi wankan ta fito tana sallah tana kuka a wurin sujjadar karshe kuwa tafi minti goma yanajin yanda shashsheqarta take qara karfi, hankalinsa ya qara tashi kardai Yarinyar nan qararsa take kaiwa Allah? Se ya mike ya isa inda take, cikin wata raunanniyar murya yace "Hamdah dan girman Allah kiyi hakuri abun zeyimin yawa in kika kaini gaban Allah. Ki bani dana na kare kaina Dan Allah". Durqusawa yayi a gabanta tamkar me neman gafara. Harta Sallame sallarta ta ninke sallayar ko kallon inda yake batayi ba. Bude baki yayi da niyyar sake magana yaji ana dukan kofa k mar za'a karyata. Hajja ce ta doko musu uban sammako Dan tun a daren jiya Hajia Hauwa ta shaida mata abinda Abdul din yayi da karin gishirin yan jere. Jin bugun bana hankali ba ya sakashi fita ya bude kofar yana addu'ar Allah yasa wanda ze iya duka ne. "Toh shanyayye wato Har ka isa in kiraka a waya kaki dagawa sannan kazo ma kaji dalilin kiran ban isa ba koh, kai har kayi tsaurin idon da zaka cewa Haula bada kudin ubanta ka Gina gida ba to ita wannan kodaddiyar data barbaza kayanta a ko ina nawa nata uban ya baka lokacin da kake ginin eye to wallahi ka fita daga idona in rufe tun wuri Idan ba baki kake so in maka ba toh kashiga hankalinka tunda wuri kasanni sarai". Bakinta har kumfa yake tsabar bala'i. Wani irin suya ranta yakeyi tana kara tsanar Hamdah a kowacce dakika. Cikin palour ta shiga tana karewa ko ina kallo dan bata san sanda aka qara gyarashi ba ko nata Albarka, seta tabe baki sannan tace "Ina ita isashshiyar sabuwar uwar taka take.." "Gani nan dena bata bakinki kina daga murya Hajja ki kuma kwantar da hankalinki base kinyi wa dan ki baki ba dan ke zakiyi asara yanzu zaki ga filin gidan nan dan zan bar masa abinsa in yaso ki auro masa Haula da uwarta da wadannan kannen nata guda biyu su cike masa hudubi". Se ta bude baki cike da mamaki tana kallonta, yanda take gaya mata Magana kai tsaye batareda tsoro ko shakka ba kamar ba wannan surukar tata ba me mata biyayya tamkar zata bauta masa. A bangarenshi kuwa beyi wani mamaki ba Dan dama yasan irin wannan ranar na nan tafe kuma ya kwana da sanin halin mutuniyar tasa. Lokaci da yawa har mamaki yake ina tsiwa da rashin kunyar ta suka tafi take bari suna takata a gidan. Abu daya ne ya daure masa kai d jin cewa wai ita Hajja ce zatayi asara kuma ita gidansu zata tafi to kodai Hamdah tadena sonsa ne? Innalillahi ya shiga nanatawa a cikin ransa in kuwa haka ta kasance ya jefa
Chapter 32 · 0% Book details