← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 62

Sashe 39

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gaisa yanda suka saba a shekarun baya dayake abokin mijinta tana tambayarsa Ummi matar sa da kuma yaransa Shuhuda da Shahida. Yanayin yanda ya kasa sakewa se ya sa Mumcy ta tashi dan ta basu gurin bata san meya kawo shi ba a lokacin, gaba daya sukayi shiru bakajin komai a falon se karar Tv da Ac dasuke aiki ita tana jiransa yayi magana shi kuma ya rasa ta ina ze fara mata maganar. "Haj Hamdah ashe kinzo gari seda jiya naje gaida Hajjah Kausar take gayamin sunzo gaisheki jiya wai Kina Kano". Dan murmushi tayi sannan tace "Eh wallahi ai na ma kwana biyu da zuwan". Wani shirun suka sakeyi, agogo ta kalla sannan tace masa " Yaya dai in babu wani abu ina so in koma akwai dan aikin da nake qarasa a ciki". Seda ya tattaro dukka jarumtarsa sannan ya fara magana cikin qarfin Hali "Am nasan zakiyi mamakin ganina da kuma jin abinda nazo miki dashi sedai ba wani abu bane inkika yi laakari da alakata da marigayi..." sai kuma yayi shiru yana tunanin ta yanda ze sanar da ita abinda ke zuciyarsa. "Ya kayi shiru kuma Ina jinka" ta fada tana tsareshi da ido, sai kuma ta sakeyi masa kwarjini nan da nan ya duburburce ya fara in ina "Toh dama dai na samu Hajjah munyi magana inji ko cikin yan uwan shi marigayi Akwai Wanda zai nema to ta tabbatar min da babu kuma ta nuna goyon bayanta sosai Dan itace ma tace inzo Dan kuma kar a samu sabani "tun kafin ya dire maganar fuskarta ta fara chanzawa zuwa matsanan cin fushi da bacin rai jikinta har rawa yake tace "sai akai yaya kuma" seda ya hadiyi wani yawu sannan yace "Dama inaso ne idan zaki amincemin in maye miki gurbin Aminina tunda dama ance ko Dan uwa ko Amini ma......" "kai dallah Malam dakata" ta katse shi ciki tsawa sannan ta miqe tsaye tana nuna masa qofa. "Tashi ka fita kuma kar na qara ganin kafarka a gidan nan, yanzu kai ko kunya baka jiba ka kalleni kake gayamin wadannan maganganun wai zaka maye gurbin abokinsa kai bame tayashi kishi da kare mutuncina koda wani kaga yana kokarin hakan bazaka hanashi sai kai da kanka zaka debo wasu munafukan ledojinka to bari kaje wadanda kake kawo wa ma shekara daya ban taba ko da duba abinda suke ciki ba dan ni koda Mijina ya Mutu be barni da tsiya ba yabar min komai najin dadin rayuwa ka kuma san da haka shine zakace kana sona wato dama jira kake ya mutu kenan ka aureni" ta karasa tana mai fashewa da kuka, se ya mike a kidime yana cewa "Subhanallahi Hamdah me yayi zafi wace irin magana kikeyi haka s ganina wannan ai shine kadai abinda zanyi masa na aureki na riqe masa ke amana". "Tashi Malam tunda ka gama abinda ya kawo ka, ka tabbatar kuma kafarka karta kara tako gidannan in ba haka ba you will regrate my action" bashida sauran bakin magana a dole ya tashi jiki a sabule, Mumcy data gama jin duk abinda suke fada ta fito da sauri tace "Dan Allah Ahmad kayi hakuri kaji kar abinda taimaka ya bata maka rai kasan yanda al'amarin nan ya kasance har yanzu bawai tagama komawa daidai bane" se yayi saurin tareta da cewa "A'a wallahi Hajiya ai babu komai nine ma ya kamata in bada hakuri gashi daga zuwana na sakata kuka, sai anjima Allah qara hakuri" ya juya ya fice daga palour. Fada sosai tashiga yi mata "Fisabilillahi Hamdah sai kace akanki a ka fara mutuwar miji da zakibi ki tsangwami rayuwarki daga an miki magana ki hau kuka ke ga Matar Mamaci ko, nida na rasa uwata da ubana ma da babu madadinsu amma nayi hakuri se ke da mijinki ya mutu idan baki saurare kowa ba taya zaki samu wanda hankalinki ze kwanta dashi ko kuwa haka zakiyi ta zama muna kallonki." "Ni Mummy bazan iya cin Amanar Abdul zan jira nima har mutuwa ta daukeni inje na tarar dashi muci gaba da rayuwar mu yanda muka fara ta". Se kawai ta buda baki tana kallonta da mamaki, lallai abin nata yayi nisa bata ko jin kira tasan ko me zata fada bazata ji ba ayanzu dan haka kawai ta gyada kai tana ayyana abinda zata mata a ranta a fili kuwa se tace "toh Allah ya sawwaqa yanzu tashi ki dora mana Abincin dare dan Yau Abbanku ze dawo duk da nasan ba da wuri ze shigo ba", kitchen din ta shiga har lokacin bata dena share hawaye ba, zaman shekara daya ace har an gaji da ita a gidan ita da ba sabgar kowa take shiga ba dole ta nemawa kanta mafita, zaman nan baze kaita ba dole ta nemi abinyi taga alama harda shiru shirun da takeyi yasa aka fara rainata dan haka ta daura aniyar komawa Ainihin Hamdan ta. Tun daga wannan rana ta sake sabon babi, ta koma Hamdah Ammanin ta matsiwaciya da bata barin ko ta kwana. Ya zuwa yanzu ta rage damuwa sosai tayi kiba abinta duk wannan ramar ta cike, dole ta birge ka yanda ta qara zama wata classy Babe, dama ya lafiya kura bare yanzu da take juya kudin kanta gayu se wanda ya qaru abinda yake qara rudar maza akanta kenan kwalliyarta. Idan kaganta bazaka taba mata kallon wadda ta taba aure ba a shekaru ko a yanayin jiki dan ta qara zama wata yarinya danya in suka jera da Hamida ma seka dauka ita ce qarama dan Hamida tafita tsahl da girman jiki in ba ka kalli idonsu ba ko kuma a magana, sosai take Fafatawa yanzu Har su Maryam na tsokanarta wai zawarcin ma me lasisi takeyi se dai kawai tayi murmushi dan qarfin hali kawai takeyi ba wai har zuciyarta ba. Taga alamar in ba ta sake da walwala ba baza'a dena takura mata ba. Acikin maneman nata Abdurrahman Dan anace ne ya kafe Dan shi wulakanci datake masa baya damunsa seya ce wai ba'a samun abu me daraja da sauqi, ya kwallafa rai akanta ya kuma tabbata seya sameta dan se a yanzu ya gane ita ce irin macen dayake so. Shi jin ta taba auranma wani qaunar ta ya qara masa be dauki hakan a matsayin wata matsala ba ko kadan dan haka ya liqe har seda ya fara samu karbuwa a gurin mutanen gidansu ta silar Nazir mijin Zahra. Su Malam Ahmad dai tun tijarar da tayi masa be kara dawowa ba duk da ada yaso auran Hamdah saboda mace ce ta kwarai da kowanne namiji zeyi fatan samunta ko ba komai yana so ya kwatanta bata kyakykyawar rayuwar da Amininsa kullum yake fatan samar mata. A lokacin yana raye bashida wani burin da ya wuce na Hamdah taji dadi Hamdah tayi walwala yana so ko bata fi kowacce mace sa'a ba to a sakata a layin farko se gashi beyi dadewar da ze cika mata dukka burikanta ba. A kace mahaqurci mawadaci se gashi a hankali juriya da naci irin na Abdurrahman sun fara masa amfani dan har ya fara samun galaba akan ta, ba laifi yanzu tana amsa wayarsa dukda gaisuwa ce kawai komai ze fada bazata tankashiba se yaci Sa'a zata bishi da Eh ko Aa haka ko gida yazo wani lokacin tana fita kuma ta dena kukan da takeyi Amma fa hakan bawai yana nufin zata aure shi bane Aa sedan Fadan da ake mata kullum akan wulaqanci babu kyau. Ita dai ta qudure a zuciyarta fa ta gama aure. **************************** Yau da wuri ta kwanta saboda Mararta data dameta da ciwo. Cikin baccin ne tayi mafarki dashi da shi karo na farko tun bayan rabuwarsu.Tafiya takeyi cikin wani katon fili fetal da bata iya hango karshensa lokaci daya tsoro ya rufeta ganin ita kadai ce a gurin babu kowa Kamar daga sama taji an kira sunanta sannan wani hannu me laushi ya riqeta ta baya seta juya a tsorace, Abdulmalik ne cikin kyakykyawar shiga ta fararan kaya fuskarsa na fitar da wani irin kyalli da haske yana yi mata murmushi daya sace mata zuciya dashi. Cikin tsananin farin ciki ta kankameshi tareda fashewa da kuka da kuka se shima ya rungumeta a jikinsa yana buga bayanta alamar rarrashi har lokacin beyi magana ba, seda ta tsagaita kukan nata sannan cikin muryarsa da bazata taba mantawa ba yace "Hamdah ta Nagode Nagode kwari tabbas kin cika masoyiya ta Hakika a kullum kyawawan addu'oin ki suna tarar dani ga lada dana ke ta samu duk ta sanadiyyarki Amma me yasa kullum kike kuka bana so". Seta share hawayenta sanna tace masa " Abdulmalik na kasa sabawa da rashinka, kullum bani da burin daya wuce in sake ganinka nayi jiran wani yazo yace min da wasa ake min baka mutu ba zaka dawo amma ban samu ba, bani da wanda ze rarrasheni a lokacin da nake kuka amma kaqi ko a mafarkina ban taba ganinka ba" ta qarasa tana sakin wani qaramin kukan. Murmushin ya kuma yi mata sanna yace "Hamdah kin taba ganin wanda ya mutu ya dawo? To kiyi hakuri na tafi na barki har abada a zahiri amma zan dawwama cikin zuciyarki har zuwa lokacin da Allah ze qara hadamu amma kin san mene" seta girgiza masa kai alamar A'a. Se ya cigaba "Banji dadin yanda kika qiyin aure ba akwai wani abu daya wuce kasan cewarki cikin gidan aure" "Abdul bazan iya cin amanar ka ba bazan iya zama da wani ba kaiba" Hannayenta biyu ya riqe sannan yace mata "In dai Dan ni ne kiyi aurenki kinji shine cikar mutuncinki bazanso ki tarar dani a haka ba Hamdah kamar yanda na Mutu Ina Mai aure haka kema nakeso ki samu wannan rabon kinji in ba haka ba zanyi fushi dake ba zan kuma kara zuwa ba". Cikin zubar da hawaye tace masa "Kar kayi fushi dani zanyi Insha Allah". Hawayen ya shiga goge mata sannan yace "Yawwa yar albarka Kaman yanda kika zamarmin jari a duniya kema Allah ya baki Wanda ze yi miki Hakan a bayan ranki kalli can ki gani" wani guri ya nuna mata dan nesa dasu, wani mutum ta gani a zaune ya juya musu baya bata iya
Chapter 39 · 0% Book details