Sashe 45
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yace "To bari nima naci abinci" kallonsa tayi cikin rashin fahimtar abinda ya fada sannan ta kalli Momyn ta "Eh kinji me yace ai kika tsareni da idonki kamar na mage" seta tabe baki kamar zatayi kuka dan bilhaqqi ita fa bata jin Hausa shiyasa taqi yarda da kowa indai ba turanci kayi mata ba wai tana tsoro kar a sace ta wai wadannan mutanen masu speaking foreign language. Tsiya sosai Ammi take mata taci zata ci gidansu zata ga foreign language bayan Hausar ita ce yaren uwarta da ubanta amma take gudunta "Rainon Inji akw gayamiki Ammi ta ina ta hadu da hausa dama wannan kina ganin kalarta ma duk tafi mu haske da alama Yaya kun manta baku saka mata Melanin ba" cewar Amina ranar dasuka zo musu sannu da zuwa kememe taqi yarda ta tabata wai saboda she is black. Seda yaci ya qoshi dan baya wasa da cikinsa sannan ya shiga wanka duk tana zaune tana jiransa a palour, wayo ya mata suka koma part din Ammi dan yau babu inda zeje anan suka wuni duk yana lura da duk wani motsin Ni'ima. Besan me take shiryawa amma yana suapecting kamar bata da gaskiya,har wayarta ya dauka ya duba dayaga tana ta waya amma bega komai ba se number mamanta data sister ta sukayi waya dan gobe a gidansu zata wuni abinda be sani ba ta goge Number Hamda ta haddaceta akanta dan tasanshi da bincike bataso ya samu wani clue da ze zargeta. Dan haka take taka tsantsan sosai akansa fatanta Allah yasa ta samu nasarar abinda take shirinyi. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Bayan sallar magriba ya shirya tsaf cikin Shadda cream dinkin riga iya gwuiwa, hularsa ya kafa ta zaunu sannan ya feshe jikinsa tsaf da turaruka masu kamshi da ka ganshi kaga me zuwa zance. Ni'ima na kwance akan gadon tana binsa da kallo kishi na nuqurqusar zuciyarta dan wannan kwalliyar da alama akwai dalilin yinta amma seta dtace "Yah Abdul kayi kyau wai ina zakaje ne" "Allah ko zance zani gurin kanwarki" ya bata amsa yana gyara zaman hularsa. Se da ta danne abinda ya taso mata sannan tace "Kai amma naji dadi kam ai daka gayamin ma dana tayaka shirya wa da gayun yafi haka dukda yanzun ma na san bazata iya resisting wannan kyan naka ba" ta karasa maganar tana dan haki saboda wani daci da zuciyarta taji tanayi a alama kishine, se ya aje comb din dayake taje gemunsa ya nufeta "Baki jin magana Ni'ima kiyita magana bayan kinsan it is not good for your health at all". Kwata kwata bama tajin maganar dayake fada se lips dinsa datake kallo yanda suke motsawa. "Do you want some" ya tambayeta bayan ya lura da irin kallon da take masa, kai kawai ta daga masa nan ya shiga kissing nata passionately, ko minti biyu ba ayiba yaji bugun zuciyarta ya qaru se yai saurin pulling out ya dora kanta a shoulder dinsa yana dan bubbuga bayanta a hankali yana jin yanda take jan numfashi a wahale kafin wani lokaci bacci yayi awon gaba da ita. A hankali ya shimfideta badan fitar ta zamar masa dole ba da babu inda zeje, wayarsa ya dauka ya kira Farida akan tazo ta zauna da ita ze fita karta farka babu kowa a gurin ko zata buqaci wani abun tunda Bangaren Faridan ne itace dama me kula da ita ko can a UK. Yana tafe a hadaddiyar Benz dinsa duk inda ya wuce se an kalleshi, tuqi kawai yake amma hankalinsa ya kasu gida biyu, daya yana kan Ni'ima daya bari a gida daya kuma yana kan Hamdah da besan dame zata tare shi ba. Cikin girmamawa Sa'idu ya gaishe shi yana tambayarsa bayan rabuwa shekaru da yawa basu hadu ba, kudi masu yawan gaske ya bashi yakuwa zube yana masa godiya kafin ya shiga cikin gidan ya kira masa ita. Yanda ta fito tayi bala'in tafiya da Imaninsa, Atamfa ce a jikinta dinkin skirt and blouse da suka dan kamata kadan sabida kibar data danyi kwana biyu. Dinkin ya amshe ta sosai bata daura dankwali ba mayafi data yafa har kanta kalar Atamfar hakan ya bashi damar hango tulin gashin kanta data daure da ribbon daya ta cukwuikuyeshi dan wai Da Kitso wata Goggonsu zata mata aka fasa. Hannunta riqe da lemon Cocacola guda daya se glass cup ta zauna akan kujerar datake fuskantarsa fuskar ta dai babu yabo babu Fallasa. Lemon ta tsiyaya ta mika masa dan tasan shine favourite dinsa a da bata san yanzu ko ya dena sha ba se ya karba yana ci gaba da binta da kallo fuskarsa dauke da murmushi. Kallo sa ita ma tayi, yayi kyau sedai Hassada amma a fili seta tabe baki sannan tace "Next time ka ringa saka perfume kadan please wannan yayi yawa har ya fara hawamin kai karshe ma yasaka mutane mura". Seda ya ajiye kofin hannunsa sannan yace " Don't worry inada wani a cikin mota bari sena dakko miki dama naji kin cewa Maryam kina so" seta harareshi bata dai ce masa komai ba. Shiru ne ya ratsa tsakaninsu, ita ta sunkuyar da kanta tana wasa da zoben hannunta tanajin yanda idanuwansa suke yawo akanta gaba daya sr takejinta uncomfortable amma ta dake kawai. "Hamdah Gani Abdul'ahad na qara dawowa a karo na biyu neman auranki ina fatan zaki amincemin a yanzu". A bazata taji maganar tasa, seta saga kanta dan ta tabbatar shi dinne ko wani daban. Yanda ta ga fuskarsa ya tabbatar mata that he mean what he said nan da nan zuciyarta ta shiga tsere har yayan cikin ta suna hautsinawa. Ina ma yazo a lokacin daya dace, ina ma yazo sati biyu kafin wannan ranar da babu abinda ze hanata karbarsa da zata yarda ta aureshi kodan ta samar wa zuciyarta abinda take so amma yanzu its too late. Bazata rushe abinda ta faro ba kai bama ze yuwuba. "Hamdah ke nake sauraro kinyi shiru" ya sake fada yana kallonta. Seta dago idanunta da suke burgeshi, irin kallon nan dayake so takeyi masa, kallo ne daya nuna tsantsar kaunar da takeyi masa wanda ita kanta bata san tana hakan ba seta fara magana A hankali "Sir...." "No call me by my name, call me Abdul'ahad i prefer that mothan anything ban taba jin sunana a bakinki ba dan Allah ki fada na tabbata se kinfi kowa iya fadin sunan". Murmushi kawai tayi a ranta tana cewa " kaman yanda kafi kowa iya fadan sunana ba" a fili kuma seta ce "Abu Hamdah dafarko zan fara da gode maka akan son da kace kana yimin, i know you have loved me from the beginning sedai kamar Destiny have other plans for us. A wancan lokacin kazo a lokacin da muka rigada mukayi alkawarin aure da wani, duk da da ace kai din ka nuna dagaske kake da abubuwa zasu iya canzawa kilan da yanzu.." Se tayi shiru. Gaba daya ya tattara nutsuwarsa akanta jin tayi shirun ya saka shi gyara zamansa sannan yace "Da yanzu me ina jinki" seda ta danyi shiru na wani lokaci sannan tace "Kilan da yanzun ni na haifa Little Hamdah" ta qarasa maganar in a low tune. Se yayi murmushi sannan shima kasa kasa kamar yadda tayi tata maganar yace "They were so many complications in Hamdah's existence ni ma i wish you were the one nasan da banyi undergoing all that i went through ba, nasan da dakanki zaki haifarmin Hamdah kaman yanda ake haifan kowanne Da a duniya". Kallon rashin fahimta take yi masa, ta fuskanci ya qara birkicewa gaba daya yanzu se ya ringa wasu irin maganganu da ake kasa ganewa amma koma yaya wannan ba shine matsalarta a yanzu ba, yana zata fahimtar dashi akan basu da sauran chance kawai shine a yanzu. " Hamdah nasan zaki so kiji abubuwan da suka faru dani a cikin wadannan shekarun, bana buqatar sanin naki dan dukkanain wani motsinki tamkar a gaba kikeyins. Kiyi hakuri Banyi miki gaisuwar Rasuwar mijinki ba naji duk abinda ya faru kuma nayi masa Addu'a insha Allah ya dace da rahamar Allah dan ko ba komai ya kula dake, ya kyautata miki kwatankwacin abinda nima zanyi miki amma bazan boye miki ba Naji dadin yankewar zamanku, na kuma yi farin cikin barewar cikin jikinki dan nasan wannan ze iya maida ki a ahalin gidansu. Nasan zasuyi amfani da abinda zaki haifa daya daga cikinsu ya aureki dukda nasan ke baki san manufarsu akanki ba. Bayan faruwr wadannan al'amuran Nayarda ubangiji ne ya dubeni ya kuma amsamin roqona ya dawo dake cikin duniyata, nasan zakice meya hanani dawowa tun lokacin da kika gama iddah, Uzurine babba. Matata Ni'ima tana cikin wani hali da bazan iya tsallaketa a wannan lokacin ba saboda tana matuqar buqata ta a kusa da ita. Na zauna da yaqinin zaki jirani tunda katangar dake tsakanin mu ta rushe amma kawai sena samu labarin shigowar wani daban cikin rayuwarki da har kin bashi damar zamowa miji a gareki. Hamdah Abdurrahman be dace dake ba kwakwata bakuma dan inasonki bane yasa nake fada miki hakan karkiyi tunanin kamar ina so in batashi ne a gurinki ko daya nasanshi tun ba yau ba. Tare mukayi karatu dashi a UK. Nasan Abdutrahman baya Shan giya bakuma ya neman Mata amma yana da aqidojin da suka fi wannan muni, boko ta ratsashi yanda baki tunani badan qarfin addu'ar iyaye ba ina Tabbatar miki za'a iya wayar gari ma yace ya bar duk wata ibadah saboda tsabar yanda Yahudawa suka shiga jikinsa. Base na tsaya miki wasu dogon baya nai ba Kije kiyi tunani akan abinda na gaya miki ki kuma dubawa kanki abinda yafi, karki maimaita kuskuran da kikayi a baya". Doguwar ajiyar zuciya ta sauke kafin ta janye tagumin da tayi, mutum biyu kenan, Anty Zahra ma bata son auran nan dukda ita tunaninta Matarsa ne bawai shidinne yake da matsala ba amma mene gaskiyar abinda Guru yake gaya mata a yanzu? Ita dai a sanin da tayiwa Abdurrahman bataga wasu dabi'un yahudawa daya fada ba yanzu. Ita har mamaki ma takeyi kamar yanda yace yayi rayuwa ne cikin turawa tsahon 15 years amma babu wani abu dayake nuna hakanc a cikin halayyarsa. Se