← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 62

Sashe 24

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ce se hawaye tace "Dan Allah Jaan ko ka bani mota, Driver ne kasa ya kaini" hade rai yayi yace "wasa ma kike Driver zansa ya kaiki kinyi wannan kwalliyar yaji kamshinki to baze yuwu baki jira kawai inna dawo da wuri se muje in ba haka ba kuma gobe". Se ta fashe da kukan gaske tana" Ni wallahi ko ma Napep ne sena shiga Dan Allah karka hanani zuwa" janyota jikinsa yayi da sauri yace "Shish wasa nake miki kiyi shiru dan Allah" shi ya riqe mata jakarta ya bude mata motar ta zauna, har lokacin gani take kaman ze ce mata wasa yakeyi. A gate din gidansu ya tsaya yace su shiga su gaida Hajja yau basuje da safe ba, "Ai tamayi hakuri har 4 weeks bata fita ba amaren yanzu da ko sati basa rufawa suke fara garari a titi" cewar Hajja bayan daya gaya mata gida ze kaita sannan sukayi mata sallama suka tafi. Seda ya tsaya suka yi musu tsaraba sannan suka nufi gidan. Sun hau titi sosai ya kalleta yace "Ni a wa in hana fitar nan nasan yau baccina ragaggene". Murmushi kawai ta masa hankalinta naka titi ji take inama tana da fukafiki ta tashi sama. Ko bari ya gama parking batayi ba ta fice daga motar da gudu tana kwalawa yan gidan nasu kira ko saurarensa bata yi ba taji kiran da yake mata ba dan ba karya tayi missing dinsu garama su Hamida sunje mata sau biyu amma mazan ba wanda ya je. Da khalifa ta fara cin karo daya bude mata kofar falon Baki sake yake kallonta dan suna cikin maganarta ne sukaji knocking din. Tun kudeshi tayi ta shiga palour tana raba Idanu ta na neman inda zata ga mumcyn dan ta tabbatar tana gida lokacin chan ta hangota tana binta da kallon mamaki itama aiko da gudu ta fada jikinta " Mummy" se kuma ta saki kuka. Gaba daya ta sanyayawa Mumcy jiki Dan haka ta shiga tambayarta "Hamdah lafiya daga Ina kike cikin daren nan ina Abdulmalik din". Ganin hankalinta ya tashine yasa ta tsagaita tace mata "Mumcy daga gida nake kuma tare ma muke da shi yana waje". Se a sannan hankalinta ya kwanta tace "To Shi kuma kukan na magani da menene ke da Baki kaunar a zauna lafiya". "Bazaki gane ba Mumcy kawai na yi missing dinki ne dan Allah kema haka kikaji lokacin da kika auri Abbah". Rankwashin wasa Mumcy ta kai mata sannan tace "kedai kin fiya shirme wallahi harkinsa hankali na tashi to inbanda abinki kukan kuma maganin me zeyi bagaki kin ganniba?" "Oh su kuruf anzo kuma yau dama gobe nake tunanin inzo inga chakwakiyar da kike aikatawa naga an ja lokaci ba'a kawo kararki ba" cewar khalifa nan suka fara Dan dama an dade ba'a hadu ba. Sallamar yaya Baffa ce tareda Abdulmalik ta katse su. "Amma dai kedai wannan anyi shashashar yarinya dama be tafi ba kika barshi a waje" Mumcy ta fada tana kokarin gyara zamanta. Baki ta zumbura gaba sannan tace "Nifa Mumcy nima bansan ya tsaya ba ai kona sani dan Allah Jaan?" Girgiza kai kawai Mumcy tayi tace "Kyaci gidanku ai wato baki dai chanza ba har Ina murna kin karo hankali ashe sema abinda yai gaba ko". "Aa fa Mumcy da na ce mata zanje na dawone shiya sa" Abdulmaleek ne ya tarewa matarsa. "To ai shiikenan" cewar Mumcy suka shiga gaisawa bayan hamidah ta kawo masa kayan motsa baki. A gidan sukayi magriba da isha har gurin goma basu tafi ba Dan seda Abbah ya dawo ya ji dadi sosai yanda yaga Hamdan tasa sannan ya karayi musu nasiha sosai Mumcy ta kara bata wasu kayayyaki sannan sukayi sallama. Zata shiga motar kenan idonta ya sauka kan BMW din Guruin da ke ajiye a gefe, lokaci daya komai daya faru ya dawo mata a kwakwalwa, ranar da ta dau kota har zuwa haduwar su ta karshe. "Ko yana wace duniyar kuma oho" ta raya a zuciyarta nan suka nufi gida ranta fal da kewar yan uwannata. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 Rayuwa da masoyi me dadi, Abubuwa dayawa sun faru cikin zaman Auran Hamdah da Abdulmalik. Tana wata na biyu da Aure Maryam ta haihu tasamu ya mace sun sha suna yarinya taci sunan kakarta Maman Yusuf din wato Ruqayyah suna kiranta Amal. Tuni ta koma aikinta da Sabuwar motar ta da Yah Abubakar ya Siya mata lokacin auranta Dan haka bata da matsalar transport. Kamar yanda ta saba duk ranar juma'a takan raba wuni a cikin gidannasu Abdulmalik din saboda bata zuwa aiki ranar yau ma haka ta kasance, suna kicin tareda Anty Amarya kamar yanda suke kiran last wife din Alhaji Kamalu suna taya ta girki, A babban Dining me cin mutum 16 kamar wani conference table tana jera kayan abincinne ta jiyo sallama daga cikin palour. Yammata ne zakada zakada har su hudu se Babbar mace da akalla atayi sa'ar Hajja, kallo daya zakayi musu kasan jininta ne saboda kamar da sukeyi sosai. Gaba daya su ukun suka gaisar da Anty Amarya data fito daga kitchen din haka itama mahaifiyar tasu ta tsaya suka gaisa sama sama banda guda wadda kuma da alama itace babbarsu data dauke kanta gefe tana danna waya da taunar chewing gum. Part din Hajja suka nufa ita dai Hamdah tana tsaye tana kallon ikon su dan babu Wanda ma ya lura da ita cikinsu. A falon Hajja suka baje nan da nan aka cika musu gaba da kayan makulashe bayan sun Dan taba ne su ukun suka shiga dakinsu Khausar se dayar data kame a kujera tana ta muzurai. Kallonta Hajja tayi aranta tana kara karantar halin yarinyar. Haula kenan uwar jiji da kai da takama ita tsabar nata isar ko gaisuwa ma se an roka inbanda son cimma wata manufa tata Ina Abdulmalik Ina wannan kodaddiyar yarinyar? Muryar Hajia Hauwa ce ta katse mata tunani tace "Bari na shiga bangaren Amare haryanzu fa banga surukar tamu ba". Haula dataji kaman mahaifiyar tata ta daba mata wuka tayi saurin jifanta da kallon wani kallo, inkiya tayi mata da ta nutsu sannan taci gaba " Ai naso inzo bikin wallahi hajia amma kinsan lokacin muna tsaka da campain ne ba dama se dai naga hotunan biki Amarya kam masha Allah". Murmushi hajja tayi dan tasan wannan magana ba har zuciyarta takeyinta ba se tace mata "Amarya ai tana nan cikin gidannan ma nazata ma kun ganta kafin ku shigo tana taya Halima girki". "Toh kila tunda kinsan ba saninta mukayiba Amma dai babu ma wata bakuwar fuska dana gani gaakiya sedai ko tana cikin kitchen ne". "Ok bari to a kira miki ita" cewar Hajja sannan ta shiga kwalawa Rufaida kira taje ta kirawo Matar Yayansu. Tunda suka shiga palour Hajia Hauwa da yarta Haula suka zuba mata ido kowanne da abinda take kissimawa aranta. A bangaren Hajiya tsantsar kyau da gayu irin na Hamdah ne ya rudata, Ita kuwa Haula zuciyarta ce ta shiga tafarfasa wani irin bakin kishi yana taso mata, babu hadi Matar Abdulmaleek ta mata fintinkau nisan bana wasa ba. A she Momy cutarta tayi datake cewa wai farar fata kawai Gareta. Harta karaso ta zauna kusa da ita bata sani ba se kamshin turarenta da ya cika mata hanci. Faram faram suka gaisa da Hajiya Hauwa ta tambayarta ango da zaman kadaici acewarta, "Ai babu ma wani kadaici dan ita ma tana fita aiki dan zaman da take ita kadai bashi da yawa" cewar Hajja ita dai Hamdah murmushi kawai tayi. Juyawa tayi tayiwa Haula da kiris ya rage tayi bindiga inkiya da ido nata gaisheta, iya wuya ta shaqa dandai bata san manufar Momyn tata ba yasakata ce mata "Sannu dai yakike"." Yawwa sannunki" Hamdah amsa mata a ranta tana jin haushin irin kallon data kafeta dashi kamar wata mayya dan haka seta mike tareda kallon Hajja tace "Hajja bari na wuce zanyi girkin dare lokaci ya fara ja". "Toh ba damuwa kema dai ke kike biyewa rigimar Abdul in ba Haka ba ga abincin anan girkin me zakiyi". Murmushi tayi tana tafiya tace Aa Hajja kinsan shi daga girkin ki se nawa yake ci gara dai nayi masa". "Haka nada kyau kuma shima ya ringa cin girkin matarsa Ai" cewar Hajia Hauwa da zuciyarta ke tafarfasa kaman zata fashe dan gani take kamar da gayya Hajja Fattu ke jan surukar tata a jiji ba, bata zaci cewar ta sake har haka da ita ba ganin irin kai ruwa ranan da akayi da ita kafin ta amince da auran, idan kuwa hakane ashe dole ta tashi a tsaye ta sake shiri Dan zama be gantaba, da ganin idanun wannan yarinyar ba karamar kissa zatayi ba amma ai in tasan wata bata san wata ba. Kwafa taja aranta tana ayyana abinda ya kamata tayi dan bazasu taba bari ya kufce musu ba, bokanta ya gaya mata shi din dai shine mijin Haula kuma aure ne irin wanda take so dan yaron yana da Nasibi a rayuwa sedai har yanzu ta kasa hango mummunan abin daya ce ze faru a gaba tunda har tayi sakaci Ya auri wannan yarinyar, koma dai menene tawa kanta alqawari seta raba auran nan ta maye gurbin sa Haula koda zata rasa komai data mallaka. Sun jima suna tattaunawa da kawar tata sedai ko kadan taki bata fuskar da zasuyi magana akan hadin Abdulmalik da Haulan, suna shirin tafiya ya shiga gidan dawowarsa kenan daga aiki ya shiga ya bawa Hajja wasu saqo daya karbo mata a tasah. Kasan cewar Juma'a ce yayi kwalliya cikin wata shadda cream se daukar ido take. Cike da girmamawa yagaida Hajia Hauwan se qara daure fuska yake saboda wani kallo da Haula ta kafeshi dashi kamar zata hadiyeshi. Gani tayi ya qara mata kyau na musamman kodan ta dade bata ganshiba ga wani qasumba daya tara tasha gyara ji take kamar ta tashi ta rungumeahi. Kallo daya yai mata ya dauke kansa, yaganeta sarai Amma seyai biris da ita. ya tsani mace marar Aji se wani lanqwashe murya take wai tana gaishe shi, seda ta maimaita kusan sau goma sannan ya amsa mata da "lafiya" yayi wa Hajjan sallama yai waje. Zungurinta Hajia Hauwan akan ta bishi kamar
Chapter 24 · 0% Book details