← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 62

Sashe 46

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kawai zuciyarta ta raya mata yana gyara tasa kasuwar ne kawai bawai dan haka abin yake ba dan haka ta dago ta kalleshi sannan tace "Nagode kwarai ina ma ace ina da yanda zanyi sedai ka makara ko nace mun makara, maganar da mukeyi yanzu Jibi ne daurin aurena da Abdurrahaman taya kake tunanin zance na fasa..." Seya dakatar da ita ta hanyar cewa "Aa Hamdah karki aikata abinda zakizo kina dana sani daga baya karki maimaita the same kuskure da kikayi dan a yanzu sedai a kirashi da ganganci". Mikewa tsaye tayi dan tasan inta ci gaba da zama tabbas zeyi galaba akanta, in har taci gaba da jin muryarsa to kuwa ze rusa duk wata dauriya tata a yanzu se ta shiga girgiza masa kai tana cewa " Ba kuskute nayi ba na auri Abdulmalik saboda ina sonsa shima yana so na, rabuwar mu daga Allah ce wa'adin zamanmu ya rigada yaje qarshe ban ta ba daukar tsangwamar da ahalinsa sukamin a matsayin wani abu ba, na dauketa kawai a qalubale da kowacce mace take samu a zaman auranta. Idan kuma na Auri Abdurrahman kwatankwacin haka ta sake faruwa dani" seta dakata tana kallon yanda ya birkice lokaci daya shima ya tashi tsaye. Kallonta yakeyi yana haddace duk wata kalma da take fada se yace "In hakan ta sake faruwa me za'ayi?" "Zan dauki hakan a Matsayin _RUBUTACCIYAR QADARAH_ ta da ban isa na kauce mata ba zan kuma rungumeta hannu bibbiyu na biyata akan yadda aka rubutata ta". Cikin tsananin tashin hankali yace " Aa Aysha karkice haka dan Allah ni kuma fa menene makoma ta a wane matsayi nake a gurinki". Seda ta mayar da hawayen da yake shirin zubo mata sannan tace "Ka jirani, inaji a jikina qaddarar mu daya zamu rayu qarqashin inuwa daya wata rana komai zahon lokaci indai muna raye" tana kaiwa nan ta shige gida ta barshi a tsaye kamat bishiyar da aka shuka. Kwakwalwarsa ma taqi yadda da abinda ta fada taqi bashi damar yin tunani akai, se ya zame hular kansa ya shiga fifita da ita saboda zafin da yake ji. Beji sallamar da Yaya Baffa yake tayi masa ba seda ya taba shi tukunna. "Abdul'ahad Galadima is this you? dama kana nan or wait me ma kakeyi a gidanmu" Yaya Baffa ya jero masa tambayoyin, Abdul'ahad was his childhood friend tare sukayi Nursery da primary school a Cairo. Karfin hali kawai yayi suka gaisa da Baffa amma ya kasa amsa masa tambayar meya kawoshi gidan se kawai yace masa wata yarinya ya gani ta bashi wrong address seda yazo yaga ba a gidan take ba, sallama ya masa bayan sunyi exchanging contact ya tafi yana shiga motarsa wasu hawaye masu zafi suka fara zubo masa. Meyasa bashida sa'a a rayuwarsa? Meya sa haryau ya kasa mallakar zuciyarta kenan yanzu ma ze qara rasata a karo na biyu? Yana ji yana gani wani ze mallaki abinda yake nasa. Ikon Alla ne kawai ya kaishi gida. Kamar mace haka ya saka Ammi a gaba yana mata kuka "Ammi bata sona, she rejected me for the second time Ammi me na ragu dashi da bazata soni ba? Ammi meyasa bazata gane itace cikon rayuwata ba? Ta kuma zabar wani da be kaini ba a karo na biyu" haka yaringa sambatu Ammi na tausarsa. Ta rasa wannan wace irin jarabawa bace yake fuskanta akan wannan yarinyar. A da tayi zaton ze manta a ita tsahon wadan nan shekarun amma setaga abin kamar Tishi, kodan yanayin dayake ciki ne da Matarsa? Tasani Su Fatima sunyi gaskiya Abdul'ahad ba yaro bane yanzu, ko beyi wa kansa wannan tunaninba ya kamata ita tayi masa. Yana da buqatar macen da zata kula da shi ta bashi farinciki irin wanda ko wanne lafiyayyen Namiji yake so, to Amma wannan auran ma da yaya akayi shi? In ta tuna gumurzun da aka sha kafin ya yarda da auran Ni'ima bazataso a maimaita irinsa ba. Ita dai bata da sauran wani abu Addu'a kadai zata ci gaba dayi masa tasan ita yafi buqata sama da komai. Akan cinyar Ammi yayi bacci, haka ta zauna tsahon dare tana gadinsa kamar jariri cikin zuciyarya tana saqa abinda take gani kamar shine mafita kawai, zata nema masa auran wannan Yarinyar da kanta duk da yace bayason hakan, bayaso wani ya shiga cikin maganarsu yafiso ya samu soyayya da amincewarta da kansa amma bazata biye masa ba dole tasan abinyi. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Karfe 4 na yammacin ranar Alhamis tayiwa Ni'ima a gidansu Hamdah kamar yanda sukayi alkawari. Halinda mijinta kuma yayanta ya shiga a jiya shi ya qara qarfafa mata gwuiwa akan abinda take da niyyar yi. Ita da kanwarta Safeena sukaje wadda batasan menene sukaje yi ba ta dai ce kawai tazo ta rakata gidansu wata friend dinta suka bar little Hamdah acan gidan nasu. Tana zaune ana mata baqin Lalle bayan tacire Ja dayayi bala'in yiwa Fatarta kyau a daya daga cikin dakunan BQ saboda cikin gidan ya fara cika da Jama'a yan biki kamar ba bikin bazawara ba. wayarta ce ta dauki qara, me lallen ce ta daga tareda saka mata wayar a speaker. Bayan sun gaisa ne take shaida mata gata a gate dan haka ta tura Amrah ta shigo da ita. Ko kadan batayi tsammanin ita bace har fuskarta ta kasa boye mamakin, guri suka samu suka zauna Safeena da bata da baqunta tashi ga zuzutun lallen da ake mata "Kai amma yayi kyau sosai se kace Amarya" ita dai Hamdah Murmushi kawai tayi a zuciyarta tana tunanin meya kawo wannan matar kuma. Dambun naman da akayi na gara da soft drinks ta saka aka kawo musu har lokacin Ni'ima batayi magana ba saboda ganin me lallen da kuma Inteesar Matar Yaya Baffa da ita ma aka saka mata lallen. "Kiyi hakuri kinzo kuma ina dan uzuri i thought i will finish before the time i gave you but unfortunately kuma na zarta". Murmushi Ni'ima ta mayar mata kafin tace "Ba komai zan iya jira dukda ina dan sauri nabar yarinya a gida". " Ba matsala we can talk here ai" hamdah ta fada ganin Ni'ima na kalle kalle. Dukda abin be mata ba, she wanted them to have some privacy suyi magana ta fahimtar Juna amma tasan in tace seta jira har an gama zata bata lokaci. Little zata iyayin kuka and shi kansa ze iya kiranta at any time ta dawo gida dan haka tacewa Safeena ta fita waje dan bata so taji maganar da zatayi, tasan ta da surutu zata iya zuwa ta gayawa Mamansu da sauran Sisters dinta, tana qunquni tana komi ta fita dan ita lallen ma taso ayi mata. Bayan Safeena ta fita ne ta koma kusada Hamdah ta zauna suna fuskantar juna, kallon inda Inteesar take ta sakeyi dan batajin ta me lallen sosai kilan yayarta ce dayar ko kuma ita ce Amaryar da ake bikin. "Karki damu feel free to talk we are all family" Hamdah ta fada tana mata murmushin karin qarfin guiwa. Seda ta yi shiru for some moment sannan ta fara magana "Hamdah nasan zakiyi mamakin ganina and you will ask your self on what is so important that i want to discuss with you" se ta danyi shiru kadan. Hamdah data tattara hankalinta gaba daya akanta tace "Yes ina jinki" "To cut it short Hamdah mijina nazo nemawa auranki". Ba Hamdah ba hatta me lalle seda ta saki kwarkwaronta tsabar mamaki karma Inteesar taji labari abinka da Yar jarida seta yi saurin qarasa sabule lallen da takeyi ta matso kusa sosai kodai kunnenta ne bejiyo mata daidai ba. In between dariya Hamdah tace "You must be kidding wane mijin naki kika zo nemawa auran wa?" Seta gyara zamanta cikin son nuna mata da Gaske ta keyi tace "You know who I'm talking about, amma tunda ta haka kika biyo muje a baki sanshi ba Ni Ni'ima nazo Nemawa Mijina Abdul'ahad auranki ke Hamdah". Seta dakata kadan tana kallonta sosai, lallai matar nan ta samu matsala in ba haka ba ita zata zo nema ma mijin nata ma aure? se kawai ta daure fuska dan abin ma yafi kama da rainin hankali, dakatar da me lallen da mamaki ya hanata ci gaba tayi ta gyara zamanta sosai sannan tace " Shine ya aiko ki?" Ta tambayeta cikin tsare gida alamar babu wasa. Seta girgiza kanta "Ba shi ya aiko ni ba nina aiko kaina sabida naga hakan....." "Dakata malama, be it shi ya aiko ki ko ke kika aiko kanki ki koma I'm not interested in your Goddam Husband inda nasan ke ce da tun farko ban answer wayarki ba" Hamdah tayi maganar cikin dacin rai wanda a qarqashin zuciyarta wata wutar kishi ce take ci. Tun asalin Hamdah me zafin kishi ce bare a yanzu kuma akan abinda take so. "Ki tsaya mu fahimci juna Hamdah dan Allah, Yaya Abdul'ahad loves you so much. Dukkan shekarunnan hankalinsa da tunaninsa yana kanki, Hamdah aure kawai nake amma bansan menene soyayyar miji ba, mijina ke yake so ke kadai yake kallo a matsayin mace". Shiru ne ya ratsa palour, ita Ni'ima tayi shiru ne sakamakon wani abu da taji yana taso mata me daci irin yanda takeji duk lokacin da ta tuna mutumin data fi so akan komai da kowa wata yake so daban, ita kuwa Hamdah jikinta ne yayi sanyi qalau da kalaman Ni'iman. Me lalle da Inteesar kuwa sunzama hoto kowa ta bude baki tana sauraron ikon Allah to da alama wannan matar bata san meyake faruwa ba. "Hamdah ki taimaki ne ki auri mijina muna buqatar ki a cikin rayuwarmu auransa ne kadai zesa nima nasamu farin ciki kamar kowacce yantacciyar Mace. Hamdah hatta Yata tafi so da dokin ganinki sama da kowa a duniyar nan, kinsan meyasa? Saboda da sunanki ta fara koyon magana. Hotonki yazamar mata kamar ibadah a kullum shi take fara kallo har ta fahimci shi kadai ne abinda yake saka Babanta farin ciki. Hamdah kinga irin murnar da tayi ranar data ganki as small as she is 3years amma ta iya gane abinda take gani a hoto tun daga ranar kullum kukanta a kawita gurin Namesake bata a sauran magana se taki ko dan ita
Chapter 46 · 0% Book details