← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 62

Sashe 53

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zasu tafi acan zata qarasa rainon cikin har ta haihu. Idan ya fita kuwa komai ya gani naci ko wanda ya shafi kayab jarirai seya siyo ya kawo mata. Akace kishi kumallon mata nan da nan se Shaidan ya shiga zuciyar Hajara yake kitsa mata cewa abinda take gudu ya faru Hamdah ta kwace mata miji tunda gashi tun ba'a je ko Ina ba hankalinsa duka ya koma kan ta Ina ga ta haihu ai ita tata ta kare a gidan, seta chanza mata gaba daya, yar hirar da suka saba da girkin datake kawo mata duk ta dena. Datayi mata magana seta ce yanzu ai taga tana da me debe mata kewa shiyasa ta ja baya ta basu fili suci soyayyarsu da tsinke, murmushi kawai Hamdah tayi bayan dataji wannan furucin nata tasan kishi ne zallah yake damunta dan haka bataga laifinta ba ita ma setayi baya da ita kawai tunda wanda ya hada ya raba. Wata ranar Tuesday da safe tana zaune Abbah yaje gidanta. Wannan shine Karo na farko tun auranta gidan Abdulmalik daya kaita da kansa be qara zuwa ba sefa ranar da Abdulmalik din ya rasu se yau kwatsam gashi a Kaduna gidanta. Ranar har kuka seda tayi dan dadi ganin mahaifin nata haka tashiga masa hidima duk abinda hannunta yakai kai seta dakko masa ta ajiye har seda ya gaji yana ta murmushi zuciyarsa fal farin ciki ganin ta kwantar da hankalinta. Sun dade suna hira, sosai ya kara mata nasiha akan dai hakuri sannan ya dan taba duk abubuwan data masa dan zama tayi zatayi kuka wai seya ci komai haka ya dinga yafitarsu kadab kadan yana ci. Se yamma ya tafi yabarta da tulin tsaraba da kuma kewarsa. A yanzu bata da wata damuwa tunda ta samu kwanciyar hankali da nutsuwa a gidan auranta. Cikinta Dan kimanin wata bakwai ya fito yayi girma sosai a jikinta kamar wani wata tara yai bala'in yi mata kyau. Kamar kullum tana zaune acikin falonta sanye take da doguwar riga dinkin kasar Oman blue wadda ta bude sosai daga kasa hakan yasa bata takura ta ba, kankarar madara ce tuli a gabanta wadda Yusra kanwar Abdurrahman tayomata take ta faman dirka dadi da sanyin madarar ya dauke mata hankali har bataji sallamar da Abdirrahman yake ta famanyi ba seda ya janye kwanon Qanqarar sannan ta dago kanta a shagwabe tana jifansa da wani kallo. Murmushi me kyau yake mata yana qare mata kallo a ransa yace "God I love this girl amma tayi fuck off ko wa yace mata seka haihu kake samun farinciki a rayuwa oho" seya zauna a kusa da ita bayan ya janye kwanon yana dubawa "Sannu madam me kika samu haka babu tayi?" Ya fada yana kai hannunsa kan qanqarar, seyayi saurin daukewa yana harararta cikin wasa kafin yace "Wato sanyin dana hanaki sha ne ko". Seda ta cire katuwar kankarar da ta tura abaki tana cije hakori saboda yanda sukayi sanyi sannan tace "kankarar madara ce fa kawai nagani a gidan Yusra shine ta aikomin da ita dazu" "Bana hana ba La la banyarda ba salon ki sa yarona yazo da mura ko to ba dani ba karna qara ganin irinta a gidan nan ita dai data qulla qawance da asibiti tayi tayi kina kallo dukka yaranta Pneumonia ne dasu" ya karasa yana kwashe qanqarar ya zuba a cikin wata baqar leda daya gani a gurin. Kukan shagwaba dake kara narkar dashi ta shiga yi masa tana cewa "yanzu fisabilillahi Dan bakasan zafin da ciki na yakeyiba ka hanani shan ice cream yanzu kankarar ma ka kwace". " An zo gurin" ya fada a zuciyarsa sanda wani tunani ya bullo masa sharp sharp, a fili kuwa se yace "To yi hakuri indae Ice cream ne zan kawo miki roba daya dai amma ba da yawa ba kin yarda" kai ta daga masa alamar ta yarda da haka ya samu tabar shan kankarar. Ya kwashe dukka ya fita da ita sannan ya dawo suka ci gaba da hira yana mammatsa mata kafafuwanta da suka kumbura sosai, wani lokacin yakan tausaya mata ganin yanda cikin duk ya chanza ta lokaci daya duk ta kumbura dukda se yaga kamar kyau ma take qarawa. Se bayan magrib ya fita Kaman yanda yai mata alqawari kuwa tun daga ranar kullum da daddare se ya siyo mata Ice cream guda daya jal ya kawo mata haka suka ci gaba da rayuwa. Kasan cewar girkin Hajara ne gashi har 9:30pm tayi bai kawo mata Ice cream din ba kamar yanda ya saba se tayi tunanin tayi tsiyar ne dan wata rana haka take ranar girkinta in ya dawo tun magribar nan bata barinsa ya ko leqa kofar gida se da safe, abin me ciki seji tayi ranar tafi kwadayinsa akan ko wanne lokaci. Dukda tana da dab sauran guntun na jiya amma ba flavour take so ba, ita Chocolate flavour take so yau yawunta har wani tsinkewa ya ringayi. Agogo ta qara kalla goma saura yan mintina seta yanke shawarar kiransa kawai a waya dab bazata iya haqura ba. Ringing biyu ya dauki wayar yana cewa ."heartbeat me ya faru kuma ko Baby yana Missing Dady ne?" "D sweety baby yaki bacci yana jiran Ice cream" Seya dafe kansa kamar yana gabanta kafin yace "Oops I'm sorry wallahi wasu abu suka sha kaina, Baby yayi haquri i will bring it to u right away" ya tashi jiki na rawa aransa yana cewa "this the right time" ko takan Hajara dake qorafin an shiga haqqin ta beni ba yayi waje abinsa. Bayan da ta kashe wayar se zaman shirun ya dameta nan ta shiga kiran mutane dukda taga dare ya farayi, Maryam ta fara kira suka danyi magana sama sama dan har tafara bacci sannan ta kira Aysha, Mijinta ne ya dauka yake shaida mata Ayshan na bacci, an kuma gamuwa ta kuwa samu ciki me dan banzan wahala yau gida gobe asibiti. Dariya ta ringayi bayan da ya gama mata bayani cikin sigar tsokana tace "kace Dan baba yayi tsiya shikenan in ta tashi ka gaya mata na kira" sannan sukayi sallama. Har ta ajiye wayar ta tuna da Anty Hadiza abokiyar aikinta a poly data haihu Dan haka ta kirata. Kaman yanda tayi tunani da korafine ta fara In da take cewa "haba Anty Hamdah shikenan kuma tunda kinbar aiki zumunci kuma ya kare sedai muji labarinki gurinsu Sadiya" kunya ce ta kamata ta shiga bata hakuri daga nan ta mata barka "Amma dae kema mun kusa zuwa suna ko?" Ta tambayeta. Dariya ta shiga yi hakan ya tabbatarwa da Anty Hadizan tunaninta gaskiya ne nan ta shiga jero mata addu'oin Allah ya raba lafiya. Shigowar Abdurrahman ce ta katseta tayi mata sallama ta kashe wayar. Turo baki tashiga yi ta juya masa baya tana kunkuni a dole ita tayi fushi dan har abin ya fita akanta. Wani irin kallo yake binta dashi Wanda ta kasa fassara ma'anarsa kafin cikin sanyi sanyi yace "is ok nasan fushin na me nene gashi na kawo ayi hakui na sanki yanzu ina iya kawowa ki maidani dan haka na siyo miki dukka flavour din da suke dashi". Seda ta harareshi cikin wasa sannan tace "Ai na yafe baka kawo min ba tun dazu se Dana cika ciki na da youghout tukunna". Nan ya shiga lallabata akan tasha sedai duk yanda yayi da ita keme me taki karba tasha din har abin ya bata masa rai cikin fada yace "kin san baza ki sha ba kika tasheni a daren na fita na siyo miki to gashi nan in kin ga dama ki dauka" a cikin fridge din dake dakin ya aje mata yayi waje fuuu abinsa. Bata ko bita kansa ba ta shiga wanka sannan tayi shafa'i da wururi, seda ta gama dukka shirinta na bacci, har ta kwanta kuma zuciyarta ta kwadaitu da Ice cream din sekuma ta sakko ta dauko roba daya ta bude tana mita a ranta nan da nan ta sha. Seda ta shanye shi tas harta bude wata wata robar tasha rabi sannan ta kwanta tana jin wani farinciki a zuciyarta. **************************** Cikin bacci taji kaman ana tsikarar ta a mararta, kadan kadan ciwon yaringa gaba harta farka daga baccin babu shiri, lokaci daya mararta ta kulle mata kamar mejin fitsari ga kuma Dan cikinta da ya tsananta motsi kamar wanda yake wrestling. Dakyar taja jikinta ta Jingina kanta da Allon gadon tana Jan numfashin daya fara yi mata wahala. Ganin ciwon dagaske yake yasata diro da kafafunta kasa sai dai mikewar sam ta gagareta, Addu'oi tashiga karantawa a zuciyarta tana fatan Allah ya kawo mata dauki lokaci daya ta saki wani marayan kuka jin Dan cikinta na barazanar barin jikinta. Dole ta yunqura dakyar ta Mike jin kamar fitsari na Neman kufce mata ta fada toilet din. Wani Abu mai dumi da take da tabbacin ba fitsari bane ya shiga zubo mata, cikin tunanin abinda zata gani ta leka dan taga ko menene sedai abinda ta gani din yayi matuqar daga mata hankali. Jini ne ke zuba daga jikinta kamar Wanda aka yanka wata qaramar dabba ba shiri ta miki bata ko damu da murdawar da cikin ya keyi ba ga kuma jinin dake zuba ta nufi part din Abdurrahman. Bugun kofar take bana wasa ba abinda yai sanadiyyar farkawar Abdurahman da Hajaran a kusan tare. kiran sunansa take cikin daga murya da azabar ciwo "Dear kaman fa Sunanka ake kira kodai Dan wata bakwai za'a haife mana ne" Hajara ta fada tana kokarin yaye bargon dasuka rufa dashi, Abdurrahman daya gama ayyana abinda ke faruwa ya mike yana cewa "yes she might be the one kinsan sha'anin masu ciki kilan dai wani abu take da buqata" yayi waje abinsa sai kuma maganar tasa tayi mata zafi har ta fasa binsa da tayi niyya ta koma ta kwanta. Da sauri yaja da baya ganin ta kwance male male cikin jini. Hankali tashe ya dagota ya shiga jijjigata ganin kaman bata motsi saboda ta zubda jini ba kadan ba. Kwantar da ita yayi ya koma dakin da gudu ya dakko mukullin mota, shigarsa da kuma jinin da Hajara ta gani a hannunsa ya sakata mikewa ba shiri suka fito a tare har suna kusan cin karo
Chapter 53 · 0% Book details