← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 62

Sashe 20

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata irin matsanan ciyar faduwar gaba ce tazo mata daidai lokacin da Goggo Suwaiba matar Baban Mumcy ta rangada mata guda a tsakiyar kai hakan ya tabbatar mata da cewar tazama matar Abdulmalik, wayarta dake gefenta ce da dauki kara alamar alamar kira Malik din ne' yake kiranta kuwa jiki a matukar sanyaye ta kai wayar kunnenta bayan ta amsa ta mike dan gujewa hayaniyar gudar da suke ta rangadawa da Addu'ar zaman lafiya. Sallama tayi masa ya amsa cikin tsananin farin ciki "Hamdah ta a yau kin zama mallaki na kin zama matata Hamdah Allah ya amsamin addu'ata burina na duniya sun cika Hamdah banqi ko a yau Allah ya dauki raina ba nasan na taba mallakar ki a matsayin mata, Allah ya sada ni da dukkan alkhairan da suke a tare da ke Hamdah, Ina fatan Allah ya azirtani da zuri'a dake Hamdah inasonki bansan irin farin cikin da zanyi a yau ba i still can't believe it kin zama tawa". Haka kalaman Abdulmalik masu kama da feshin wuta suka ringa dukan kunnanta. Be damu da shirun data yi ba ya kashe wayar gaba daya babu ko digon damuwa a ransa Dan a yau jin kansa yakeyi he is the happiest person on earth to shi meze dameshi bayan Allah ya mallaka masa autar mata? Jiki babu kwari ta isa jikin window dakin ta janye labule tana kallon harabar gidansu har zuwa kan titi mutane tamkar ana hawan sallah ga kade kade da bushe bushe harda Jiniya ta ko ina. Ko kadan bata kula tsokana da wakar Tazama tazama da cousins dinta da suka biyo ta suke tayi mata ba dan kwakwalwarta ta tafi hutun wucin gadi ne a lokacin. " Hasbunallahu wani'imal wakeel" ta fada tana dafe kirji, indai ba gizo idonta keyi mataba Abdul'ahad ta gani shida yusuf mijin Maryam suna kokarin shiga mota. "Yaushe ya dawo? Dama har yasan ranar daurin aurenta amma beyi komai akai ba? Kenan maganar Yah Abubakar gaskiya ce daya ce in har da gaske yana sonta baze barta na kusan shekara daya be waiwayeta ba ashe ita take yaudarar kanta da cewa yana sonta" se kawai ta fashe da kuka, ture daurin kanta dayai bala'in yin kyau tayi ta kwanta akan gado tana kuka me ban tausayi. "Allah na tuba ka yafemin da yanzu na cutar da bawan Allah me sona dagaske, yanzun dana rabudashi na kama bilhu kenan? Abinda take saqawa aranta kenan ya qara sakata kuka. Ba irin rarrashin da ba suyi mata ba Amma taki shiru abin har ya bawa su Aysha haushi " Se kace akanki aka fara aure kome yau ko auran dole akai miki ai iya kacin abinda zakiyi kenan Hamdah tunda aka fara auren nan kawai kin bi kin dagawa bawan Allah hankali Kaman ba ango duk a rikice yake, sekiyi dagaske Allah ya bada sa'a tunda ke baki jin magana". Mumcy ce ta ke mata fada bayan da itama tayi aikin rarrashin ta gaji haka suka kyaleta kowa ya fice daga dakin ya barta. Ango Abdilmalik ya shiga gidan da zugar abokanshi. Masha Allah yayi kyau sosai cikin Sky blue Babbar rigar daya saka bakinnan kaman ze yage tsabar dariya. Haka suka ringa ratsa mutane ana gaggaisawa se wulla ido yake yana neman ta dan bashi da burin daya wuce ya rungumeta a jikinsa a lokacin ya kirata da "Zauji". Wa cousin dinta ce ta lura dashi, yana durqushe gaban Goggo dake masa tsiyar ita ce amaryar ba wacceb babyn robar ba tace " Goggo ki kyaleshi an riga an rudeshi da farar fata da dogon gashi tashi in kaika inda Amaryarka take ka rabu da wannan tsohuwar" kamar wanda yake a kan qaya haka ya mike ba ko kunya yabi bayanta mutanen palour na ta masu tsiya, shidai be tanka ba dan a lokacin bashida wani burin daya wuce yaga Hamdah. Kukan ya tarar da ita tanayi abinda baze taba iya jurewa ba yaga hawayenta yana zuba, tuni ya aje duk wata surukuta a gefe, babbar rigar jikinsa ya cire da hula sannan ya haye kan Gadon ya dagota gaba daya ya rungumeta a jikinsa "To ya isa haka haba duk kin bi kin gogemin kwalliya tun ban biya kudinta ba" ya fada yana kallon tsakiyar idonta. Hanky yasa yana goge mata hawayen Kaman wadda yasawa stop haka tai shiru tana kallonsa a zuciyarta tana tunanin da yanzu ta rasa shi, da yanzu ta rasa wannan masoyin ita kam wace irin sagegesuwa ta kusa tayiwa kanta? Ya mata kyau matuka dan tunda aka fara bikin beyi kyau irin na yau ba kayan sun matuqar amsarsa. Setaga kamar har wani haske ya qara amma kuma ya rame a sanin da tayi masa. "Hey stop looking at me like this kar kisa nayi abin kunya a dakin surukata". Dukda mood din datake ciki seda ta harareshi sannan tace " In naqi fa me zakayi?" "Let me show you" ya fada yana qoqarin juyata qasa setai tsalle ta tashi daga gadon tana dariya tace "Look at you bako kunya". Mikewa yayi daga kan gadon ya nufi gaban mirrow yana murmushi, at least he made her laugh, alkawari yawa kansa baze qara barinta ta zubda hawaye ba. Powder ya dauka ya qarasa gurinta har lokacin tana tsaye, shafa mata ya shiga yi tsaf ya gyara mata fuskarta harda qara mata lip gloss ya kama hannunta yana cewa "Ina dankwalin ki da veil muje ana jiranmu kar wadancan su ganemin gashin mata". Murmushi kawai takeyi ta nuna masa inda ta wullar da dankwalin se veil a kan bedside drower, gaba daya ji tayi damuwarta ta yaye wani irin sanyi yana shiganta sai ajiyar zuciya data ringa saki a hankali. "Nidai na kasa Amma bari inyi miki irin Wanda naga kinyi ranar nan" ya fada bayan ya gama kiciniyar daura mata dankwalu ya kasa. Sosai taringa dariya kai bakace itace tagama shan kuka dazu dazu ba. Daurin ture kaga tsiya yai mata ya tsaya a gaba goshi kamar me tafiya dambe ya yi mata kyau sosai. "Haba Jaan yanzu se na fita da wannan daurin a yau" ta fada kalmomin a rarrabe. Seya bude idonsa yana kallonta, baze iya tuna rabon data kirashi da Jaan ba lallai ta fara komawa Hamdahnsa ta baya. Mayafin ya yafa mata har kai sannan yace "Eh mana duk Wanda yai magana kice masa Angon ki ne yai miki haka yake so ya ganki" dahaka ya riko hannunta suka sauko kasan. Masha Allah kowa yake fada bayan sun gama hotunan ne angwayen suka wuce gurin reception. A daki kannen Mumcy da kawayen ta suka sakata kowa da kalar tata nasihar kafin yar Sudan ta shiga aikin shirya Amarya Dan da wuri za'a kaita saboda gidan su Ango sun shirya Dinner da daddare. *************************** Durkushe take a gaban Abbah, wani farin lace ne a jikinta dinkin riga da skirt dayai matukar karbarta ya fito mata da shape sosai. Tsaf aka lullubeta cikin wata hadaddiyar laffaya fara me adon duwatsu golden fuskarta babu ko digon kwalliya hakan ya qara fito mata da ainihin kyanta kana kallonta sak Amaryar me cikakken gata. kafatanin yayyenta na zaune sun a falon shiru bakajin komai se shashshekar kukanta. Abbah ne ya katse shirun ta hanyar cewa "Akwai me sauran magana ne?" Gaba daya suka amsa masa da "Aa". " Masha Allah Zahra zo ki kama yar uwar ki kuje gurin Mommynku Nidai nagama nawa Allah ya sa Gidan zaman ki kenan Ina mai karayi miki nasiha da hakuri, karki gaza kiyi hakuri akan dukka lamuranki insha Allahu bazaki tabe ba". A gefen gado suka tarar da Mumcy Haj zainab Aminiyarta da Anty Amna sun sakata a tsakiya suna magana Wanda shigowarsu ta saka su yin shiru. Hannunta Haj zainab ta kamo tana cewa "Ai Zahra dama kun wuce kawai baki dawo da ita ba". "Mama Abbah ne yace a kawo ta suyi sallama Ai" cewar Zahra. Zaunar da ita tayi a kasa daidai kafar mumcy da taki koda dago kai ta kallesu tace "Toh Maryam ga yarki tazo miki sallama". Wani bangaren daban ta kalla dan ji take kaman kukan datake dannewa ze fito tace sannan tace "Ai nagama gaya mata duk abinda zan fada aje ayi Hakuri Hamdah Banda kai kara ko gayawa kawaye sirri bani ba ba Zahra ba kar inji maganar mijinki a gun kowa Allah yayi miki Albarka ni dai na yafe miki duniya da lahira....."kuka ne ya kufce mata tai saurin mikeqa ta fada toilet. Ai nan sabon daru ya barke Dan Hamdah ta dage Idan Momynta bata fito ba bazata tafiba da kyar Abbah da yaya Abubakar suka fita da ita tana kuka kamar wadda zasu kai kabari, fasa saka ta A motar daukar Amaryar yayi ya ce "Saddiqu dauko mukullin mota ta kawai da kaina zan kaita". Tana jikin Yah Abubakar tana kuka har suka dauki hanya, tana jin lokacin da Abbah ya kirshi akan ya jirasu a gidan gaahi nan zuwa. Sun isa gidan nata dake kusan hade da gidan su Abdulmalik din duk cikin unguwar ta sharada NNDC. Har kan katafaren gadonta Abbah ya zaunar da ita sannan ya kalli Abdulmalik da kamar anyi masa bushara da Aljanna yace "Abdulmalik ga Amanata nan basai nagaya maka matsayinta a gurina ba ina fatan zaka rike min ita dakyau kaman yanda nayi tunani daga gareka". "Insha Allah Abbah zan kula da ita sama da yanda zan kula da kaina". Cewar Abdul din yana sosa kai. Gajeriyar nasiha ya qara yi musu gaba daya duk akan hakuri sannan yai musu sallama suka tafi abokan ango se yaba dattako suke irinna sirikin abokinnasu. Se bayan tafiyarsu yan rakiyar Amarya suka karaso kowa nata santin gida. Su Haj zainab ne da wata yar Abbah suka shiga da ita cikin main house din dan dama abinda suka so yi kenan badan da kansa ya kawota ba, sun samu kyakyawar tarba daga dukka matan gidan da dama suna jiran zuwansu daga nan suka mayarda ita gidannata. Se Bayan da suka idar da sallar magriba tasake wanka me kwalliyar da aka dakko ta shiga zayyana duk wata fasaha da Allah yai mata akan fuskar Hamdan daga nan kowa ya fara shirin Dinner Ango kansa yana can yana tsatso nasa kyawun dan yace baze yarda kullum ta fishi
Chapter 20 · 0% Book details