← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 62

Sashe 15

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ringing biyu ta daga "Nikam nayi fushi yaushe rabonki da ki tuna wata Maryam ma" abinda Maryam ta fada kenan bayan sun gaisa. "Wallahi ba haka bane Bestie kinasan service dinnan se a hankali in kika fara zaki fada kema" ta bata amsa. "Haka ne kuma ai dai wallahi ba'a kyautamin ba yanzu duk se kun rigani gamawa ina Afiya mutanen Ondo?" "To bestie in banda abinki ai lafiya tafi komai in ba so kike ki qara mana Asarar Baby ba ki bari ki haife cikinnan in yaso daga baya sekiyi koma mene". Hira suka ci gaba dayi maryam din na mata complain akan irin complications din datake samu da ciki, Karo na uku kenan data samu ciki tun bayan aurenta amma biyun duk basu zauna ba acewar likitan wai saboda zarryar da takeyi ne kuma mahaifarta is not strong enough to carry a baby, dole yanzu suka bata total bed rest Wannan dalilin yasa Yusuf ya hanata fara Service yace ta jira next year. Wannan hirar ce ta dauke mata hankali harta manta dalilin kiran data mata, sun dade sosai kafin sukayi sallama. Ta hakura yanzu, bata da wani aiki illah na kaiwa Allah kukanta Dan shikadai ne ze iya mata maganin damuwarta. ********************** Da ga bangaren Abdulmalik din kuwa dagaske sukeyi akan maganar, kaf yabi Yayyensa Maza da Mata akan maganar ko zasu taimaka masa as he expected Yan dakinsu dukka a against the matter dan gaba daya halayyar su daya, They are all capitalist. Duk da wasu daga cikin yayunsa maza suna goyon bayansa to Amma abanza tunda wadanda ke da say a maganar sunce Aa a yanzu bashida sauran kwanciyar hankali ko nutsuwa, ya kafe yavkuma qudurcewa zuciyarsa komai wuya komai rintsi baze hakura da ita ba. Babban abinda yake damunsa yanta take nuna masa halin ko in kula, yanzu in bashi ya kirata ba bazata taba daukar waya ta kirashi ba haka in zeyi wata beje wurinta ba bazata ce masa dan me ba sedai haka ko dar be saka masa ba, he believes tana sonshi kuma babu abinda ze chanza hakan kai ko ta dena sonsa shifa se ya aureta wallahi dan shi aka halittota. Kwanaki nata tafiya babu kuma wani chanji a bangarori biyun, zuwa yanzu Hamdah ta gama saduda akan lamarin Abdul'ahad domin in bata bata lissafi ba yau wata shida kenan cif rabonda taji ko labarinsa bare ta ganshi, hatta Yusuf data tambaya ce mata yai yayi tafiya amma babu wanda ya san kasar daya tafi hatta kuwa Hajiarsa be fadawa ba. To me ya same shi haka? Me aka masa da yayi fushi ya rabu da kowa? Tunanin haduwarsu ta qarshe tayi ranar daya dawo da ita gida bayan wancan Incident din, zata fita daga motar yarike hannunta yana kallon cikin idonta "Hamdah i'm asking you one more time, will you please marry me?" Bata san meya shiga kanta ba a lokacin, alredy tanajin haushin abinda ya mata earlier dan haka itama seta rama, seta saka shi yaji haushi. Zamanta ta gyara bayan ta bude murfin motar ta murguda masa baki sannan tace "Hey Mr Man, dama tuni na gama gane take takenka and who do you think will marry you ni Hamdah? Allah ya rufamin asiri kadai nema daidai da kai a gaba nimakam I'm already taken". Lokaci daya ya saki hannunta yawa motar key, badan ta yi saurin fita ba babu abinda ze hata faduwa kilan ma yabi ta kanta. Yanda ya fizgi motar kana gani kasan a fusace yake hakan kuwa ya mata dadi koba komai ta rama tai shigewarta gida ranta fes. Lokaci daya ta fashe da kuka, wato ya yarda da abinda ta fada masa kenan shi yasa yai fushi ya bar mata qasar. Me yasa be tsaya ya kara nemanta ta gaya masa wasa takeyi na? Tun farko ma meyasa suka shaqu har haka ita yanzu gata bata ga tsuntsu bata ga tarko, kukan Nadama da dana sanin wautarta ta ringayi. Wannan shine abinda Aysha da Afeeya suke gaya mata ashe akan kartayi wasa da damarta. Baka sakin abinda yake hannunka ba tare da ka kama wani ba, gashi yanzu babu Abdul'ahad Babu Abdulmalik din. Haka taringa kuka har seda ta gaji dan kanta tayi shiru, gaba daya ta chanza baka taba cewa itace wannan me neman rigima da tsokanar, tayi wani irin sanyi ko magana yanzu wahala takeyi mata. Tun chanzawarta yanawa yan gidan dadi acewarsu sun huta da rabon fada har ya zamana su dakansu suke Neman tayi maganar. Mumcy tayi iyayinta ta hakura tasan dai damuwar nada nasaba da guguwar rikicin maganar auranta. Lokacin data sameta akan tayiwa shi dayan Abdul din magana tunda wannan babu shi kuka kawai ta saka mata, take gaya mata ya tafi babu wanda ma yasan inda yake a yanzu, addu'a kawai Mumcy tai mata akan Allah ya fito mata da wanda ya fisu alkhairi. Abdulmalik ne kwance cikin dakinsa, kallo daya zakayi masa katabbatar yana jin jiki dan yau kwanan sa biyar kenan a dakin bayan Yajin daya dakawa yan gidan gaba daya A cewarsa baze kara fita waje ba harse Alhaji da Hajja sun yajanye kudirinsu nayi Masa Auran dole. Abdullah kaninsa ne yashiga dakin dan jin shirun yayi yawa abu har kusan Kwana biyar a nan ya tararda mummunan yanayin da yayan nasa yake ciki. Da gudu yakoma cikin gidan ya shaida musu nan fa hankalinsu ya tashi gaba daya, babu shiri sukai asibiti dashi shidai Alhaji ko a jikinsa Dan lokacin da aka gaya masa ma waya yakeyi da Amininsa akan yanda lamarin biki ze kasance. Asibitin Yayansa aka kaishi. Amenity ward suka kwantar dashi bayan dogon bincike Dr suka saka masa ruwa sannan ya nemi su barshi ya huta dan yana matuqar buqatar hutu a wannan yanayin. Jininsa yayi mugun hawa ga kuma zuciyarsa na barazanar Harbuwa mafita a bashi abinda yake so in dai ba auna so su rasa shi ba. Ba qaramin tashi hankalin Hajja yayi ba dan a duniya bata hada kowa da Abdulmalik na, shi kadai Allah ya bata Da Namiji dan haka bazatayi wasan da zesa ta rasa shi ba. Masifa ta hauyi tanaji tana gani baza'a kashe mata Da ba bashiri ta shiga kiran Alhajin. Duk abinsa yana tsoron Masifarta dan Hajja bata da sauqi in dai akan fada ne. Kamar dan data haifa haka ta ringa balbala masa masifa shi kuma nutsu yana sauraronta gaba da gabanta. Dan indai bala'i ne to Fattu ta dameshi ta shanye duk cikin matansa babu wacce yake shakka irinta Dan haka a dole ya tashi ya tafi asibitin sedai fa ya kudurcewa zuciyarsa wannan karan ze nuna mazantakarsa Dan baza a maidashi kara min mutumba a cewarsa ya gama yanke magana da Matawalle babu me tada wannan zancen. Sedai shi da kanshi yanayin dayaga Abdulmalik din ya bashi tsoro yana kwance bambancinsa da gawa numfashi gaba daya ya zama wani qashi da rai. Amma ya dake har yana cewa inma mutuwa zeyi sedai ya mutu Amma aure ba fashi. "Eh ai dole kace haka tunda baka da asara kana da wasu Yaya mazan to wlh kaji da kunnanka bazan zuba ido Ina kallo inrasa Dana ba Dan haka yau base gobeba zakaga abinda zanyi". "Ai sekiyi muzuba mugani nida ke wazeyi nasara "fuuu ya ja rigarsa ya fice daga asibitin. Dama a hanya yake akwai Important meeting da ze tafi Abuja washe gari amma saboda bata masa ran datayi a ranar ya tafi. Kaman yanda hajiyan tayi alkawari kuwa kwana biyu ta hada Kanin Alhaji Kamalu guda daya Baba Salisu da Amininsa tun na yarinta Alhaji sabo se babban Dansa Namiji da me bi Masa Alhaji Nura da Dr Ibrahim ta kirga kudi 200k ta basu suka kai kudin gaisuwa dan tun a ranar da aka kwantar dashi da kanta ta kira Mumcy akan ta shaidawa Abbah zasu turo. Da farko yaso yayi gardama Amma da Mumcy ta nuna masa akan yayi hakuri basu san sirrin da Allah ya boye a auran ba tunda masu adawarma sun hakura to su bari kawai. Haka suka karbi kudin ba tareda tunanin komai ba suka kai tunda sunsan Tsakanin Alhajin da Hajian ba'a shiga. Sun samu kyakykyawar tarba, harkar girma aka musu suka baro gidan suna yabon dattako irin na Prof da yan uwansa. Labari me dadi suka dawowa Abdulmalik dashi an saka ranar auransa Sati biyar masu zuwa. Tuni ya warke tunda ya samu maganin ciwonsa. Masifa bala'i har ma da tsinuwa sun shata alokacin da Alhajin yasamu labarin abinda tayi masa Amma bashida yanda zeyi Dan ita ma ta nuna masa jan wuya dole ya hakura amma tabbas Fattu ta ja masa asara, kwangilar daya karba ma ta hannun Matawalle yake ji sedai cikin ikon Allah koda ya gaya masa rashin lafiyar Abdulmalik din da kuma hukuncin da da Hajja ta yake Matawallen yace ba komai ai aure rabone hakan kuma baze shafi zumunchinsu ba. Sosai ake shiri ta kowane bangare Hajja dakanta ta tafi Dubai ta hadowa Dan nata kayan lefe Dan yanzu ba laifi tanayi da Amaryar tun bayan daya kawo mata ita suka gaisa, yanayinta da nutsuwarta ya birgeta sannan ta tabbata kaf surukan gidan babu kyakykyawa kamarta dama ita damuwarta kar ace an fi danta Dan haka da gaske take shirin koba komai babu me kushe zabin Dan nata dan duk cikin kawaye da kishiyoyi babu wacce takeda zukekiyar suruka irinta. Aminiyar Haj Hauwa ta kira ta akan rade radin da takeji na wai an saka wa Abdulmalik rana to ina Zancen nasu Hadin ya tsaya kai tsaye ta gaya mata cewa "yaro baya so Dan haka baza tayi masa dole ba" bakinta taja kawai tayi shiru dukda yanda yar tata take damunta akan abin Amma tasan muddin tafadi wani abu yanzu suna iyayin baran baran sedai tayi alkarin bazasu barshi haka ba dole ta dau mataki akan al'amarin. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 Biki nata matsowa shiri akeyi ta kowanne bangare, tuni ango ya murmure haka ma Amarya kashi 70 na ramar da tayi ya tafi sedai fa har a sannan bata da nutsuwa. A koda yauahe yaushe tunaninta ya na wani guri daban Wanda su suke gani Kaman Jimamin barin gida ne sedai agurinta ba haka bane. Bakuwa wani abu take
Chapter 15 · 0% Book details