Sashe 34
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Abdulmalik kuwa yanzu se addu'a dan itace ma me tausarshi akan abun. Ya zama kamar wani zautacce, ya rantse ya kuma rantsewa akan bazeyi wannan aure ba ita kuma Hajja ta gindaya tata rantsuwar akan in be auri Haula ba to sedai ta tsine masa yabi duniyar kowa ya huta. Tun abun nawa Alhaji dadi har ya koma bashi tsoro, duk yanda ze bi yasa ta hakura takafe dan har Yayyenya ya je Har Maidugurin da yake ganin sun isa da ita amma ta shafewa idonta toka tace a rabu da ita ai Dan tane bana wani ba. To se muce Allah ya daidaita wannan al'amari haka. Some weeks later. Tsaye take cikin kitchen hannunta na hagu rike da ludayi tana juya miyar da ke soyuwa a kan Gas inda dayan hannun daman ke rike da waya magana takeyi cikin nishadin da ta dade rabonta da irinsa. "Kai leefa baza dai ka chanza hali Ba wai ma gaba dayanka nawa kake ne na rantse wannan matar seta goyamu ta zagaye Kano kaf bata gaji ba ta fada tana shekewa da dariya in ta tuna da pictur daya turo mata na wata gandamemiyar mata wai a matsayin budurwarsa. Sun dauki lokaci sosai suna magana da kanin nata kafin sukayi sallama.Tsaf ta gyara duk inda ta bata sannan ta kara goge kan dining din, har zata wuce ta hango farin katon envelop din da Ahmad ya kawo dazu da safe ya ajiye kan centre table seta dawo da baya ta dauka. Katinan daurin aurene masu kyau an rubuta _ABDULMALIK AND HAULAT_ akai ga ranar Daurin aurenan wannan Asabar din me zuwa. Tabe bakinta tayi sannan ta ajiye Dan ita yanzu shirgin daya kwaso suma ba kallonshi takeyiba sedai ko me ta tuna oho ta dawo da sauri, zazzage katinan tayi ta ware wadanda take da tabbacin na Amaryar ne dan kalar su daban tashiga kitchen dasu, ta kofar bata ta fita bayan ta yayyafa musu kalanzir yanda zasu fi ci dakyau sannan ta qyaata musu ashana take suka kama da wuta bata bar gurinba seda ta tabbatar sun cinye tsaf sannan ta kwararawa tokar ruwa karma a samu koda irin barbadinsu tayi gaba abinta. Sai bayan magriba suka shigo gidan shida Amininsa Ahmad, daurewa kawai yake wani irin azabar ciwo kansa yakeyi Kaman ze rabe gida biyu. Yanzun ma daga gurin Hajja yake duk akan dai maganar auran acan ya tarar da wannan gantalalliyar tsabar rashin kamun kai wai tazo gurinsa karbar invitation cards. Ahmad ne yace masa ya bugo su tunda safe ya kawo su gidan bayan ya dibi wadanda ze rabawa abokansu, badan yana tsoron bakin Hajja ba da ya gaya mata abinda zesa kota titin unguwar bazata qara sha'awar biyo wa ba. Haka suka bincike katinan tsaf amma babu alamar na Amarya se tulin na daurin aure kawai aka bari. Mamaki ne ya kama Ahamd da hannunsa ya ajiye katinnan fa ba wani ya aiko ba "Wallahi tare na karbo su gaba daya anan kagani na ajiye su dukka tare harda ma Gate pass na dinner data cemin a bugo". Be ko tankashiba ya nemi guri ya zauna yana jin yadda yake dada jaddada masa akan shifa ya kawo. Takun takalmin uwar gida ne ya maida Hankalinsu gareta Tayi kyau Harta gaji cikin Maroon din atamfar data saka tun kafin ta karaso kamshinta yai musu sallama. Cike da kissa ta qarasa jikinsa ta rungumeshi tana masa sannu dazuwa se ya saki baki dan rabonda tayi masa hakan tun suna zaman dadi. Harar Ahmad daya dauke kansa gefe tayi a ranta tace " Munafuki dukda hadin bakinka ai". Se seda ya Dan janyeta sannan yace "Babe kinga wasu cards a nan kuwa?" Wata hararar ta kuma ballawa Ahmad sannan tace "To Jaan ni ka bani ajiya ne ko da aka kawo ni aka bawa". shidai Ahmad Murmushi kawai yayi dan yanzu tsoron lamarinta sukeyi tunda tayi musu bore se kawai yace "Kaga Abdul bari naje kawai na bada a buga wasu tunkan Hajja ta kara hura mana wata wutar" yai waje abinsa. Abinci ta takura masa yaci Dan har ga Allah yanzu tana dan jin tausayinsa kadan gaba daya ya lalace ya fita hayyacinsa, gurin mayarda plates yaci karo da tokar cards din acikin sink murmushi yayi dan ko kadan abin be bata masa raiba saima dariya da salon kishin nata ya bashi. ********************************* A kwance suke sedai ba bacci suke ba kowanne da kalar tunanin da yakeyi a zuciyarsa kara. Juyi tayi ta qara shigewa jikinsa tana qara matseshi ajikinta ta rasa dalilin dayasa akwanakin nan take tsintar kanta cikin faduwar gaba sosai musamman yau daya rage yan awanni yazama nasu su biyu, zuciyarta takan raya mata kamar zata rasa shi, gani take kamar Haula zata kwace mata Abdul dinta gaba daya. Tayi nisa acikin tunaninta ya kira sunanta cikin wata irin murya "*AISHA*...." ya kira sunanta, Se ta dago da sauri ta kalleshi. Tunda take dashi be taba kiranta da Aisha ba wanda shine Ainihin sunanta da Dangin Maman Abba ne kawai suke kiranta dashi saboda sunan Kakarsu ne ta bangaren uba se wasu yan tsirarun mutane kamar Dr Guru sunan ya fado mata a zuciya, setayi surin kauda tunaninsa ta koma kan kiran da Abdul yai mata dab ita tsakani da Allah har mantawa take da sunanta kenan tunda ko a makaranta badashi take amfabi ba. Bugun zuciyarsa ne ya karu ga wani zafi da takeyi masa ya rasa abinda yasaka ya tsani wannan kallababben auran kwata kwata abin be kwanta masa a rai ba dai dai da minti daya Amma gashi Hajja taqi gane hakan, Karmar zata tsine masa yazamar mata jiki ayanzu. "Please Aisha karki gujeni komai wahala kinji koda kuwa ina cikin halin hauka ne nasan ke kadai zaki iya zama dani" se ya fashe da kuka. Tsoro ma ya bata ita dan haka kawai ta saka masa kukan suka shigayi tare babu me rarrashin wani har seda bacci ya daukesu sannan sukayi shiru. Shagalin biki ya kama gadan gadan tun daga ranar litinin har zuwa yau Alhamis ana kudi yaga tasku. Tun da suka fara wunin gidan ya gagareta saboda ba kaken maganganun da ake yaba mata har cikin dakinta suke biyota Mama Shuwa kadai ke kokarin kwantar mata da Hankali dan ma a wannan karon tadan samu goyon bayan Megidan dan dakansa ya shiga yake ce mata tayi hakuri. Shikansa uban gayyar yanzu seta wuni bata sakashi a idonta ba ita dai ta wa kanta alkawari bazata kara tayarwa da kowa hankali ba tasani hakuri baya taba faduwa banza Dan haka tacigaba da kaiwa Allah kukanta a koda yaushe. Ranar Juma'a sukayi wunin gidan Ango anan cikin gidanta, dafarko taso ta qi yarda amma Mumcy ta gargadeta akan tayi shiru anayi ne dan a tsokaneta ta tura musu aniyarasu ta barsu kawai, bangaren nata cike yake da faccalolin ta dakuma kannen Abdul din dasuke shiri haka yan uwanta da kawayenta da abokan aiki sun mata kara kwarai duk sunzo tayata wunin. Ba karamin kokari tayi ba gurin danne duk wani kishi da bacin ranta ta kure kwalliya cikin lace dan ubansu fuskar nan tasha make up tayi kyau qwarai dama me kyan ce abinda ya kara bakantawa yan korar Hajja su Kausar kenan Dan duk abinda akeyi anyine Dan a bata mata kuma gashi bata nuna hakan ba ko a kafarta ba. Suna zaune a Babban falon ana ta hira wasu na tsokanarta akan ta basu sirrin wannan jarumtar datayi sedai tayi yake kawai tace "Ku bari se layi yazo kanku tukunnan se in gaya muku". "Aa ba Amin ba kibar shi kawai" suka hada baki gurin fada. Zainab ce da Kausar se Anty Khadija babbar yar Hajja suka fado dakin Kaman an harbo su "Ke annamimiya mumafuka dangin mayu to wallahi tun wuri ki sakar mana kurwar dan uwa wato mun kwatoshi dakyar muna neman rabashi da wahala anje an qara yo binne binne ana neman kara mayar da shi ruwa ko to baki isaba ki tashi duk ma inda kika boyeshi ya fito Dan yau ba fashi se yaje dinner". Gaba daya matan dake dakin suka bisu da kallo batareda sun tanka suba. Khausar da ke tashen fitsara ta karasa kan Hamdah tareda ture mata dan kwalin daya kafu akan ta tace "Wato ga yan iska muna miki magana kin mana banza ko......" ai bata ida karasawa ba saboda marin data dauketa dashi, bata bari sun dawo daga mamaki ta shiga nunasu tareda yi masu kallon tsana tace "Tun daga kanki Khadija har zuwa ke karamar mara kunya (tana nufin khausar) ba wacce zan sake ragawa daidai nake da kowaccenku yar iska Dan shiru shiru ba wai tsoro bane Abdul kuma se kuje ku nemeshi Dan in naso hanashi auren nan da baku zo nan kuna babatun banza ba Dan haka kar wadda takuma gigin tako kafarta zuwa dakina in dai ba akhairi ya kawo ta ba in kuma ba haka ba wallahi sena aikata mata abinda batayi tsammaniba ko wace ce ita kuwa". Ai ba girma ba arziki suka bar gurin suna kumfar bakin bazasu yarda ba. Aysha ce matar Abubakar ta raka su da tsaki sannan tace "karyar banza daku tsaya mana in ba tsoroba wallahi kin birgeni da kinsan zaki iya hakan kika barsu suna taka ki son ransu". Ko da suka fadawa Hajja surutan banzan ta tayi ta gama sedai batayi gigin zuwa ba Dan yanzu itama ta fara shakkar surukar tata abu daya dai wannan aure ba fashi dukda ita kanta halin da Dan nata yake ciki yana damunta Amma ji takeyi Kaman zata mutu idan baayi wannan aure ba. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 2 Safiyar Asabar. Tunda garin Allah ya waye take fama dashi akan ya tashi ya shirya saboda zuwa daurin aure, tanayin hakan ne kawai saboda cika umarnin Abbah daya kirata jiya da daddare yake ya ba mata akan qoqarin da tayi akayi yinin bikin lafiya ba tareda wani rikici ba. Sannan ya qara da cewa tayi qoqari ta sakashi yaje gurin daurin auran in ba dan haka ba taso ta nunawa su Hajja iyakarsu, zata qunshe shi a daki su zauna ko iya wannan ta baqantawa Amarya rai ace ko daurin aure ango be halarta ba. Ko jiya da