Sashe 51
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kana da lura zaka gane. A kofar kitchen din suka ci karo da Mumcy kafadata sakale da farar rigar likitoci (lab coat) da alama shigowarta kenan ita ma seta bude ido tana kallonta kafin tace "Oh ni Maryamu ashe dagaske musbahu yake yace min kinzo Allah dau yasa lafiya irin wannan zuwan bazata babu notice haka". murmushi qarfin hali tayi ba tare da ta tanka ba ta raba gefen Mumcyn ta wuce cikin kitchen din dan a yanda takejin yunwa batada karfin yi mata wani bayani a sannan. Tayi sa'a kuwa Mama tabawa na kwashe tuwon alkama da miyar kubewa da tayi ita ma da mamaki take kallonta " Uwar masu gida saukar yaushe jiya fa muke zance zuwa duboki Hajia tana cewa Kaduna tayi dadi an jiki dif". "Yanzu Mama saka min tuwon dan Allah wallahi yunwa nake ji kamar nayi me" ta fada tana zama akan kujerun qaramin Dining din dayake cikin kitchen din saboda yanda taji kafarta ta fara rawa. Tuwon ta zuba mata takuwa hauci hannu baka hannu kwarya kamar wadda ta shekara bata ci komai ba "Masha Allahu Ubangiji ya sauke ki lafiya Anty na nidai dama in ce wannan dau dakikayi ashe da Magana" Mama Tabawa ta fada cikin farin ciki kamar ita ce me cikin, haka taci gana da janta da hira ita kuma tana kwasar abincinta tana gyada kai dan ya mata dadi, seda taci kusan mara uku sannan taji ta dam bata haqura ba seda ta kora da Fresh Milk medium bottle sannan ta fita daga kitchen din tana tayi mata tsiyar wai ko Nomau zata haifo musu ne. Da kallo Mumcy ta ringa binta lokacin data shiga dakinta tana karantar sauyin data gani a tattare da ita nan take ta gano cikin dake jikinta, saidai wannan uwar ramar datayi tazarta ace ta laulayi koda yake ya danganta da irin tsirfar cikin. Gefen gadon ta samu ta kwanta dan gaba daya jikinta ya mutu tace "Wash kai Nayi missing Gadon nan wallahi" Se Mumcy ta kalleta tana murmushi "To ai gaki akansa yanzu maganar missing ta qare, wai meya faru da yamma haka kuma ke kadai ce ko tare kuka zu?" Seta dan yi jim dan bilhaqqi har ta manta da matsalar data korota. Ganinta cikin gidansu yasa komai ya bace mata seta qirqiro murmushin da iyakar sa lebenta kafin tace "Ni kadai fa Mumcy wallahi na kasa jurewa se samin lokaci yake yana fasawa saboda shi kullum yana ganin Hajiyarsa shine kawai daya barni wai gobe a kawo ni ni kuma yana fita nayi tahowata" ta shiryawa Mumcy qarya dan tana ganin hakan ce kawai zata ceceta. Bata damu da fadan data ringayi mata ba dan wannan me sauqi ne hartayi ta gama akan me zata hawo titi ita kadai bayan ga yanayin da take ciki ita bata son sakarci da wauta. Kulawa cikakkiya da tasan tana buqata ta shiga bata se gata a cikin kwana biyu da tayi a gidan ta dawo hayyacinta saboda kula da kuma kwanciyar hankalin data samu. Tayi fresh tayi mulmul bata da aiki seci da bacci dab seda Abbah ya dawo ne ma yake tambayarta gida da Mijinta wanda ta ma manta dashi dan tunda ta baro gidan ta kashe wayarta shima se tace masa ganin gida tazo Mumcy na kallonta amma har zuwa lokacin bawai ta gama yarda bane dan tana lura da ita tunda tazo ko sau daya bataga sunyi waya da mijin nata ba hakan yasaka ta fara zargin Akwai wani abu a kasa da bata so ta fada. Se ranar data cika sati da barin gidan hajiyarsa ta samu labari ta bakin Munaya kanwarsa data je Hajara take gaya mata cewa Hamdah fa ta tafi gida kuma wayarta a kashe take sannan shi gogan kamar ma be damu ba sabgar gabansa kawai yake karma wani abu ya kuma faruwa ace ita ce, bata saurari komai ba ta rangada masa kira akan duk inda yake yazo tana nemansa, yasan Hajia sarai bata da sauqi dole ya baro meeting din daya tafi Abuja ya dawo Kadunan washe gari kuwa da sassafe ta tasoshi a gaba suka nufi Kanon Dabo. kasancewar week end ne Dan haka yawanci suna gida harda kuwa su yaya Abubakar da Baffa tareda matansu duk sunzo. Lokacin da suka zo ma ita tana can baccin farillanta na safe bata ma san wainar da ake toyawa ba. Mumcy ce ta shiga dakin, ganin yanda tayi dai dai akan gado tana bacci yasaka ta tada ita "Mumcy kin katsemin bacci na nasan yau haka zan wuni ba dadi" ta fada tana mikewa daga kwancan Dan cikinta ya fara girma har ya fito ana iya ganinsa."To tashi kya karasa a gidanki ga mijinki da surukarki nan sunzo daukarki". Setayi dif nan take hawaye ya fara ambaliya a fuskarta "Yanzu Mumcy kun yarda na koma gidansa ko bakisan me yake shirin aikata min ba". "Nasani Hamdah Amma kiyi hakuri ya gane kuskurensa yakuma biyoki ya bada hakuri ko ba danshiba Dan mahaifiyarsa gatacan ta ajiye girmanta tana rokarmu Dan haka ki dauka hakan ma yana cikin *RUBUTACCIYAR KADDARAR KI* ki kuma yi kokarin da hakuri gurin tsallaketa. Har akullum Ina miki nasiha da hakuri dominshi ne jagoran rayuwar dukkan Dan Adam, tashi kiyi wanka kinji suna jiranki" ta karasa tana kautar da fuskarta Dan dauriyarta ta kusa karewa. Kwata kwata hukuncin da mijin nata ya yanke beyi mata ba Amma yaya zatayi, yaqi barin sa yayi bayanin tahowar tata kawai yace wai sabani suka samu kuma ya gane kuskurensa ayi haquri ta koma amma bai fadi ainihin dalilin sabanin ba. Wani ban garen itama tana tunanin dawowarta gida ta zauna din da dadi ba dadi dai gara tana gidan auranta. Zama tayi a gefen gadon tana jiran Hamdaj data shiga wanka. Lokaci lokaci tana share hawayen tausayin Yar tata, Allah kenan meshiryawa bawa rayuwarsa in ba haka ba Hamdah bata cancanci fadawa irin wadannan matsalolin auratayyar ba wancan Matsalar Dangin Miji wannan kuma Mijin dungurungun. Harta fito daga wankan ta shirya bata saniba seda ta girgizata tace "Indai akai na kike tunani Mumcy ki kwantar da hankalinki nasan Allah be manta daniba kuma fa ni gidan ne kawai ma bana so matarsa setayi ta sa wasu turaren wuta mara dadi nayi ta amai shine fa nace ya raba mana gida yaqi amma bafa wani abu ne serious ba" dole ta kakalo murmushi ta rungumeta tana cewa "Ai kedai you are capabale of giving some one heart attack, dama dalilin kenan kice Allah ya taimakeni banyi abin kunya a gaban suruki ba. Allah dai yayi miki Albarka ya saukeki lafiya Insha Allahu inaji A jikina wata rana komai zai zamo miki labari zaki ji dadin zaman aure yanda baki tsammani ba A lokacin zaki kwashi sa kamakon hakurin da kikayi" Farouk ne ya shigo kiranta, seyati jim ganin Mamansu tana kuka. Guri ya samu ya zauna kusada Hamdah ya janyeta daga jikin Mumcy kanta a kafadarsa yace "Ki gayamin in har bakya son sa zan tsaya miki da Ilimina seya sake ki" se Mumcy tayi saurin dakatar dashi da cewa "A kul ya saketa fa farouk wata hudu me kake zaton mutane zasu ce" cikeda takaici yake kallon Mumcy wai Mutane take tunani bata san hadarin da Yarta take ciki ba, se kawai ya mike hannun Hamdah a nasa suka fara tafiya. A zahiri ana ganin basa shiri amma yafi kowa lura da lamuranta. Yana sane yana kuma bin duk zaman da take da wannan mutumin da tun farko dama beso auranta dashi ba. Da ace shine Abubakar ko Baffa yasan ya isa yayi magana a saurareshi da bata auri wannan green snake din ba. "Hamdah nasan zaman da kike, ki gayamin zaki koma ko bakyaso" ya qara tambayarta a hanya. Seta kalleshi kafin tace "Yah Farouk Momy da Abbah nakeji, bana so hankalinsu ya tashi. Zan koma amma in naji ba daidai ba zan kiraka na shaida maka komai nidai kuyita bina da addu'a kawai" da haka suka qarasa palour. Har qasa ta durqusa ta gaida Hajiyar Abdurrahman se kallonta take baki yaqi rufuwa saboda Riga da skirt tasa yadan kamata haka yasa cikin jikinta fitowa. Suna hada ido dashi ta dauke kanta dan bata qaunat ganinsa ko kadan, shima a nasa bangaren ganin cikin yake kamar wani baqin kumurci dukda kyan da yayi mata shifa be hango ma kansa ya karbi cikinnan ba. Haka suka musu sallama shikansa Abban daurewa kawae yayi Amma har zuciyarsa gani yake kaman baiyi mata adalciba na rashin sauraron nata bangaren, haka suka kama hanyar kaduna bakin hajia bai rabu da saka mata albarka tareda yaba karamci irin na iayayenta ba har suka shiga garin kaduna. ************* Abdul'ahad Abdullahi Galadima ne ya fito daga Conference Hall, hannunsa na dama dauke da laptop kirar kamfanin Apple a dayan hannun kuma wayace yake daddan nawa alamar kira zeyi. "Barka da rana Ammi" yafada har yana Dan sunkuyawa alamar girmamawa Kaman yana gabanta "Rana ko dare Babana ai mu yanzu karfe goma harta gota lafiya dai koh" ta amsa shi "Oh namanta ne wallahi Dan mu nan shabiyun rana naga missed call dinki lokacin ina wanka tun bayanda na fito kuma inata ayyuka Se yanzu na samu saukinsu". "Allah sarki to Allah ya taimaka dama najika shiru kwana biyu ne shi yasa na kira naji ko lafiya to Alhamdulillah tunda komai kalau" haka suka ci gaba da magana a zuciyar sa Addua yakeyi Allah yasa kartayi masa tambayar da baya so bai karasa tunanin ba yajiyo muryarta tana cewa "Babana wai yaushe zaka dawo ne na gaji da wannan saka ranar da kakeyi daga tafiya sati biyu ka share wata kusan hudu" kansa ya dafe a ransa yace daya kenan a fili kuwa cewa yayi "Insha Allah Ammi very soon zan dawo Akwai shirye shiryen dana keyine inaso Dana dawo in cika miki burinki in qara aure" Tuni ta washe baki ta hau murna Wanda har ya gane hakan daga muryarta "Allah ya nuna mana dakuwa ka gama min komai ita kanta matarka hankalinta ze kwanta dan kullum zancenta kenan ni har tausayi take bani wallahi badan ciwo ba da Kagama Sa'ar mata kaidai a rayuwa Dan Ayanzu banida wani buri daya wuce inga tarin jikoki na ta bangatenka ABDUL'AHAD