Sashe 56
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kawai ta zauna a gefen gadon Mumcy inda ya tarar da ita ta saka kuka. "Kiyi haquri Maman muma ba'a son ranmu ba amma wannan ita kadai ce hanyar da zamu inganta rayuwarki, Abdurrahman ba miji bane kura ce da fatar Akuya ya yaudare mu ne kawai dukda bawa baya taba kaucewa Qaddaar sa ki godewa Allah daya kawo sanadiyyar rabuwar ku dan na tabbata idan kika san ainihin shidin waye se kinyi dana sanin Faruwar ranar da kika hadu dashi ma a rayuwarki gaba daya dan haka kiyi saurin share hawayenki kuma ki godewa Allah kiyi fatan hakan yazama alkhairi a gareki insha Allahu qarshen wahalarki kenan kinji" kalaman Abba da suka sanyaya mata zuciya kenan da daddare bayan data same shi da takaddar da Yah Farouk ya bata. Haka ta koma dakinta jiki a sanyaye sedai koda sau dayane tana so ta qara ganin Abdurrahman din, tana so ta tambayeshi wane laifi ta aikata masa haka da har ya mata irin wannan danyan hukuncin, so take ta tuna masa da romon bakin soyayyar dayai mata alqawari da tarin kulawa kafin ta yadda ta aureshi ya manta lokacin daya ce ze wa marigayin mijinta takwara in har ta haifi Da namiji lokacin da yake cewa he can't wait to have cute kids with her amma ya qare da yi wa yayansa kisan wulaqanci amma babu komai akwai Allah ze kuma yi musu hisabi dan dai bazata iya yafe wannan cutar da yayi mata ba. Cuku cukun neman Admission ta shigayi dan tana so ta fadada iliminta. A kaf yaran gidansu Goma ita kadaice ta dauke bangaren Abbah wato lecturing, ita ma tana so ta taka matsayi irin nasa wata rana a kirata da Professor Hamdah Ahmad Ammani dan haka ta shiga neman makaranta inda zata dora Phd dinta akan Genetics Engineering, cikin ikon Allah ta samu admission a Wata makaranta dake birnin London ta kuwa fara shirye shiryen tafiya cikin sati biyu komai ya kammalar mata hatta da gidan da zata zauna ta kama an kuma gama shirya mata komai seda ya rage saura kwana uku ta fara lectures jirginta ya daga zuwa qasar ta London ta bar gida da tarin kewar mutanen cikinsa. Bata wani sha wahalar gane kan garin da kuma makarantar ba saboda Islaha Yayar Afeeya dake aure take kuma zaune a kasar ta London kuma makaranta daya suke karatu, ita ta nuna mata komai da ko ina kasancewarta me saurin fahimta in few days ta zama yar gari. Unguwar da take zaune duk yawanci gidajen dalibai ne dukda akwai ma'aikata wasu single wasu kuma masu aure da suke zaune a gurin. Tayi Sa'ar samun makotanta biyu da suke jere da juna dukka musulmai ne dayar Bahaushiyace ma amma yar Ghana me suna Zuhaihat se kuma Darussalam Balarabiyar qasar Saudiyya da Allah ya hada jininsu haduwar farko kuma sukayi sa'a ashe course daya suke karanta. Darussalam ma Bazawara ce kamar Hamdah tana da Da guda daya Ashrab ta rabu da mijinta saboda yayi Ridda sakamakon wata baturiya daya fada soyayya da ita lokacin suna zaune ne a kasar Canada dalilin dayasa suka rabu kenan ta dakko danta ta dawo nan London take karatu tana kuma some part time Job. Kofar dake jingine da tata ta gefen hagu ce suka ce mata wani dan Nigeria ne a ciki amma ya dade baya garin kuma dai Landlord din ya ce musu be saki gidan ba har yanzu tsahon shekara biyu yana ci gaba da biyan kudi shi dinne dai Allah be sa ya dawo qasarba. Karatunta takeyi bilhaqqi dan dama shi ya kaita, ta dade da siyan katon kwado ta garqame kofar zuciyarta dashi ta kumayi cilli dashi a tsakiyar Teku ta yanda babu wanda ze bincikoshi ballantana ya har ya qara yi mata kutse zuwa cikinta. Kasar ta London ta karbeta matuqa, tayi kyau na birgewa fatarta tamkar ta wani jariri sabuwar haihuwa tsabar laushi haka jikinta ya murje ta zama wata babbar mace ta kwatance. Hamdah Ahmad Ammani Mace yar kimanin shekara 27 a yanzu ta amsa sunanta na qasaitacciyar Mace da take juya duniya a hannunta. Nata sirrin kyan shekaru ne suke qara fiddo dashi domin yanda jikinta ya qarasa cikewa a yanzu da kuma chanje chanjen da ta samu na halitta seya qara fito da ainihin kyawun sura da Fuskar da Allah yayi mata. Diri da kirar jikinta tamkar irin matan Ethopia da suka amsa sunansu Mata haka fuskart kamar Balarabiyar qasar sudan Amma ita fara ce tas koma ince Yellow. Kwayar idanunta su suke qara mata kyau se kuma hakoranta da suke a jere kamar wadda aka sakawa a kanti, Tabbas Hamdah Me kyau ce tabarakalla masha Allah cikinta da wajenta kamar yadda Zuciyarta take me kyau, taskun rayuwa data shiga wani al'amari ne daga rabbil izzati da babu bawan daya zarce a jarrabashi. Kowanne dan adam da tasa kalar _Rubutacciyar Qaddarar_ sedai kawai ta wani tafi ta wani zafi kamar yadda Examination take a makarantu anan duniya sedai muyi fatan Allah ya hadamu da abinda zamu iya. Watanninta biyu a London tuni ta zama yar gari, ranar Friday da wuri take fitowa daga school saboda presentation ne kawai sukeyi. Bayan ta fito ne ta biya ta super market tunowa da yau birthday din Ashrab yaron Darussalam dan haka ta shiga nemo masa abinda zata bashi as gift. Hannunta riqe da manyan ledojin data ciko da tarkacen kayan wasan yara su motoci jirage da sauransu saboda tasab abinda Ashrab din yafi so kenan, dole seta tsallaka titi kafin ta koma daya hannun ta hau mota sanin qasa ce me doka da tsari ba kamar inda ta baro ba yasa cikin kwanciyar hankali ta fara taka titin bayan da danger ta tsayar da dukka masu ababen hawa ta kuma bawa masu tafiyar qafa damar tsallakawa sedai yanda ya shararo mota kamar ze bi takanta ne ya matukar bata tsoro har bata san sanda ta watsar da kayan hannunta gaba daya ba tsabar diricewa seta tsugunna akan titin. Wani abin haushi abin takaici kwata kwata ashema ba akan hannun sa take bane a daya tsallaken motar take, seta bi bayan motar data wuce kamar walqiya da kallo kunya da takaici suka cikata ganin yanda aka baibayeta ana mata sannu da tambayar bata dai ji ciwo ba ko, ita dai tunda ta samu aka hade mata kayanta suka tare mata Taxi ta shige tayi gaba tana kara Allah wadai da Halin koma waye daya tsorata ta da gani wannan duk inda ya fito Dan Nigeria ne dan su kadai suka saba da irin wannan bala'in gudu babu gurin zuwa din haka tayi ta mita har me Taxi ya sauketa a kofar Estate dinsu ta bashi kudinsa sannan ta kwashi kayan ta shiga ciki. Tana qoqarin bude kofar plat dinta idanunta suka sauka akan motar dazu cikin parking lot dinsu kamar yanda komai na Estate din yake a tsare gidaje hudu ne a kowanne rukuni haka kowanne mutum an tanadar masa gurin ajiye mota guda daya yanda kowanne gida yake da Number Haka parking lot din ma yake kowa da nasa. A 'No 506' a kayi parking motar ma'ana ta maocinta ce da akace yafi shekara biyu be zoba seta tabe baki kawai aranta tace "Kowa da halinsa ze zauna" ta kwashe kayanta tsaf ta shiga dasu. Wanka ta farayi dan ta gaji sosai sannan tayi Sallar Azahar ganin lokaci yayi, tana dab da dora girki ne Zulaihat ta shigo hannunta dauke da Coler abinci se kuma Leda qarama da batasan ko menene a ciki ba. Da murmushi ta tareta ta hutar da ita girki, haka suke duk wadda tayi abinci tana bawa kowa a cikin su ukun tun tana baya baya dasu harta haqura ta saki jiki dan Su biyu kusan shekararsu Hudu a tare ita ce zuwan kwanan nan, zama zulaiha tayi tana mata sannu bayan ta mika mata abincin tayi mata godiya ta fara ci tana wa Zulaiha tsiyar girkinta Yaji gashinan har ta koyawa Umm Ashrab kaman yanda suke kiran Darussalam ita ma tana cika yaji a abinci. Ledar data shigo da ita ta mika mata tana cewa "Gashi Neighbor dinki ne ya dawo dazu ya kawo mana tsaraba nasan besan akwai new tenant ba shi yasa na raba nawa biyu na kawo miki kene me son Perfumes sosai" . da murnarta ta karbi ledar me tambarin Alharamain ta shiga fito da turarukan ciki, guda ukune kwalabe yan mitsi mitsi amma duk wanda yasan darajar turare yagansu yasan masu daraja ne. Dagowa tayi ta kalli Zulaiha kafin tace "Amma dai wannan neighbor da kirki yake na kuma gode sosai kuma wallahi kaman kinsan na dade ina neman wannan turaren" tayi maganar tana shanshana kwalbar hannunta, sedai ta kasa tantance turaren ciki ne yake qanshin ko kuma ledar da aka sako su ce. Ita dai ko a lahira tana tunanin zata shaida wannan Kamshin dan a gurin mutum daya take jinsa amma yau gashi a wani guri daban, seta mayar dasu ciki ta qarasa cin abincinta sannan ta zura dogon Hijabi akan Armless gown din jikinta suka fita tareda Zulaiha dan su je plat din Mum Ashrab su qarasa shirin birthday celebration din da za'ayi da daddare. **************************** Kamar kidan ganga haka zuciyarta ta shiga bugawa ga hannunta daya gagara tsayawa guri daya tsabar rawar da yake har seda Zulaiha ta lura ta karbi key din data kasa rufe kofar dashi ta rufe. Duk kalma daya dayake fada a zuciyarta da kwakwalwarta take sauka tana qoqarin qaryata kanta akan cewa bashi bane ba dan haka ta dauke kanta dan ma karta kalli me maganar ko ba komai bata so tsohon mikin data kwantar ya qara taso mata. Ta gefensa suka wuce, dogon mutum me cikakkiyar sura ta mazantaka ya juya baya dan haka bata ga fuskarsa ba tayi saurin fadawa gidan Umm Ashrab kamar wadda aka biyo tana mayar da Numfashi. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Kallonta Zulaiha da Umm Ashrab suka shigayi tareda tambayarta abinda ya faru, bata amsa musu ba se ma gefen kujera data samu ta ta zauna tareda Lumshe idanunta tana kokarin saita bugun zuciyarta. Ta kusan minti biyar a haka mamaki da tsoro duk ya cika su to meya sameta haka? Bude idanunta tayi ta kalli yanda