Sashe 5
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sonsa kenan. Be dauki kansa da nisa, yanada matukar mu'amala me kyau ko acikin Yan uwansa maza. A Kasan rumfar Bunu dake gefen Cikin Babbar farfajiyar gidan Yazauna, kafarsa daya kan daya kafatanin hankalinsa nakan Main Entrance na Palour daga inda yasan Mutuniyar tasa zata fito. Cikin takunta me daukar hankali seka rantse tana sane take rausaya in tana tafiyar amma ko daya kawai halitta ce da Allah yayi mata. Riga da Skirt ne a jikinta na Lace Kalar sararin samaniya ta yafa siririn farin Veil a kafadarta Babu ko digon kwalliya a fuskarta inka cire chappet data shafawa lips dinta wanda ko kusa baa ganin kyallinsa. seta zama kamar wata Flower, kallonta yake a zuciyarsa yana qara godewa Allah akan irin zaben da yayi, yasani cikin mata dari babu kamar Hamdah she is just Unique. Salon gayunta daban ne Shi da kansa yasan yana da kwashe kwashen Yammata amma betaba haduwa da Mace me kwarjini da zati kamar taba. She is just different in her own ways haka ya dulmiya cikin duniyar wasikar Jaki, already yana hango ta a matsayin matarsa wai har ga Yarinya ta haifa masa me kama da ita..... Clapping Hannunta tayi akan fuskarsa abinda ya dawo dashi daga tunanin kenan. "Hamdah Dan Allah Karki rabu dani wallahi mutuwa zanyi inna rasaki". Yanda yai maganar seya bata tausayi kamar wani maraya daya ke shirin rasa ragowar gatansa dan haka seta ja kujera ta zauna a gefensa. Jug din dake dauke da Favourite Lemon Juice dinsa ta jawo ta tsiyaya takai masa baki. Kamar dolo yaringa kurbar lemon yana kallon kyakykyawar fuskarta Har ya shanye. "Babe Marry me" ya fada kalmomin a rarrabe "Wallahi i love you with all my heart Kullum se nayi mafarkin munyi aure I'm afraid kar wani yazo ya dauke min ke......" hannu ta dora akan light pink lips dinsa tana kallonsa a cikin ido tace "God forbid bad thing hakan ma baze taba faruwa ba Insha Allah ni takace we are made to be pairs so kabarma wani tunani". "But when?" ya tambayeta. "trust me JAAN" tabashi amsa. "As you said my lady Allah ya mallakamin ke bansan irin murnar dazanyiba "yakarasa yana shafa fuskarta. Fari tayi masa daya kusan juya kwakwalwarsa sannan tace "I shall be yours Insha Allah dear karka damu zaka sameni yanda kake so". Hirar su suka cigaba dayi harzuwa wani lokaci kafin yamata sallama yatafi Saboda Magriba tayi. Acikin satin tafara IT dinta nan cikin asibitin Malam Aminu kano (AKTH), Abdulmalik ke kaita kullum sannan in ta tashi ya dakkota. A cikin dan lokacin suka qara shaquwa da fahimtar juna, sun ruga da sun yardarwa kansu bazasu iya rayuwa babu junansu ba. Kawae cikar lokaci suke jira na tabbatuwar burukansu na mallakar Juna. Sauda yawa in bashi da abinyi a gida ze tafi asibitin ya zauna ya jirata in kuma tana da less aiki haka zasuyita zagaye asibitin suna hirar su tunda be riga yayi resuming aiki ba. ****************************** A bangaren Abdul'ahad kuwa tunda ga ranar dasuka gama exam be sake sakata a idonsa ba. Ya damu kwarai har wani Lokacin yana Ji kaman yaje gidansu ya ganta amma se zuciyarsa ta kwabeshi da ba yanzu ba. Kasancewar hutun da aka bada na makaranta ba meyawa bane two weeks ne kadae yai matukar daurewa acewarsa nan da sati biyu zata dawo ya cigaba da troubling nata Se daga baya ne ma yakejin labarin ai suna SIWES, Ai kuwa sosai yaji haushin hakan dan ko bakomai ganinta na rage masa abubuwan daya keji Akanta amma dukda haka be shirya bayyana mata kansa ba yanzu "Lokacin zezo amma bayanzu ba" zuciyarsa take gaya masa. Haka rayuwa taci gaba musu da tafiya. 5 months leave A cikin wata Biyar da fara IT dinsu abubuwa dayawa sun faru ta kowanne bangare, soyayyar Hamdah da Abdulmalik, son masi wani da Abdul'ahad yakeyi ga kuma IT dinta daya fara nisa dan har an fara zuwar musu supervision. Suna tafe ita da Maryam dawowarsu daga kasuwa kasancewar bikin Maryam din saura sati daya Ya rage, seka rantse Hamdah ce Amaryar yanda ta kacame cikin hidimar biki. Maryam Kawarta ce tun ta Yarinta Iyayensu Abokai ne sannan tare suke makaranta tun daga Junior secondary har yanzu da suke University. Akwai shaquwa sosai a tsakaninsu sannan tasu tazo daya dadin da dawa unguwarsu daya dan haka kusan koda yaushe daya tana gidansu daya. hira sukeyi harta kai su inda Maryam din ke cemata "kinji wai Guru ne zezo mana supervision ko". Da karfi zuciyarta ta buga Wanda batasan dalilin hakan, tsakani da Allah tamanta da wani mutum me suna Guru ita. Ta rasa dalilin da ya saka aduk lokacin da aka ambaci sunansa se zuciyarta ta buga da karfi, se tayi shiru bata bawa Maryam amsa ba. Maryam data lura da sauyin yanayin lokaci daya ta kalleta cike da kulawa tace "yadai Hamdah why the sudden change?" "Nothing kawai kaina ne naji ya fara ciwo". "Ayyah najawo miki koh muje gida seki sha magani kuma ga wannan azazzala'un sekira takeyi" (tana nufin Afeeya). Ita dai da uhm ta bita dan gaba daya jitayi komai ya kwance mata. Ko gidansu Maryam din kin yarda tayi ta qarasa, a bakin titi ta ajiyeta da niyyar anjima in taji sauki zata je su qarasa abinda basu gama ba. Lokacin data shiga gida wanka kawai ta fada ko zata ji sanyi sanyi. Ta rasa meya cunkushe mata zuciya lokaci daya haka. Kwanciya tayi lamo kamar me bacci duk da yunwar data shigo da ita amma ta kasa fita taci abinci. Khaleefa dayaga shigowarta amma shiru bata fito ba ya tashi ya bita dakin, da ido ta bishi har ya kulle kofar fuskarsa dauke da murmushin tsokana yace "trouble seekern Mumcy yadai yau ko an musulunta ne an chanza hali". Kallo daya ta masa ta dauke kai tunda yaga haka yasan yau tsohon hali ne ya motsa. Dukda kasancewarta me Surutu amma tana da halin miskilanci wanda yawanci se wani abu na damunta, a qa'idarta bataso a dameta when she is alone. Tafiyarda da ta same ka on her own ta gaya maka damuwarta than kai ka tambayeta. Haka ta ringa juyi akan gadon dan ko Abdulmalik daya kirata ce masa tayi they should talk later yanzu Bata cikin good mood sanin halin mutuniyar tasa ya saka shi ya kashe ya barta ta huta. Messaga ne yashigo wayarta Daidai lokacin datake kokarin ajiyewa kaman karta duba amma ganin number ba suna ya sakata budewa. "Warm greetings. I'm Dr AA Galadima I shall be in your training centre tomorrow for supervision.Thank you" Shine abinda sakon ya kunsa. Kara gyara kwanciyarta tayi kawai aranta tana mitar waya turo mata wani Dr AA fisabilillahi haka ze zo ya tasa mutum a gaba da shegun tambayar ya aka haifeka, dole ta fito da duk wani jotting dinda takeyi ta fara karantawa inda bata gane ba tayi googling ko ba kumai bata so ya raina mata hankali. *********************** Karfe tara a cikin Training lab Tayi mata, Casual Attaire dinta ta saka Arabian Chiffon gown maroon da kananan stones peach colour agabanta da tsakiyar bayan. Maroon veil din rigar ta rolling kanta dashi bayan ta kama tulin Baqin shinta da ribbon tayi parking a tsakiya irin Acucin nan. As usual babu ko powder a fuskarta, yanda ta dora well Ironed Lab coat dinta Se ka rantse wata Consultant ce. Shoe da bag dinta duka peach Sosai kwalliyarta tayi kyau. Gaba daya bata da nutsuwa yau din, wani irin yanayi takeji ajikinta dan haka tayi shiru bata saka baki acikin hirar da sauran students din sukeyi. Kamar ance tadago karaf idonta ya sauka akan Dr GURU. A iya ganin datake yi masa a school bata taba ganinsa da wani kaya Wanda ba suit ba Gaba daya se ya sauya mata yau. Wata dakakkiyar shadda Hilton cream colour ce a jikinsa. Yanda ya kafa hula akansa tamkar wani sabon Ango. Sabanin da dayake barin Suma akansa yau taga yayi askin saisaye har fuskarsa ya qara gyara quarter million Sajensa. Tasan Guru yana da kyau he got the perfect skin tone kamar me wanka da Madara. A hankali take jan numfashi tana ajiyewa wanda ke cike da daddadan kamshin turarenshi lokaci daya taji tamkar an sauke mata wani dutse daga kan zuciyarta. Kallon mutanen cikin Lab din takeyi majority dinsu Matane hankalinsu gaba daya yana gurin Harda mazan dan babu Hassada Yau kam Gayun Guru ya kai a kalleshi. A karo na uku Malam Garba ya maimaita HAMDAH AHMAD AMMANI wanda se alokacin tajishi shima saboda wata Halima data taba ta seta mike ta dauki jakarya da Log book dinta ta nufi inda taga sauran course mates dinta sun tsaya kaman an zare mata laka. kallonta yakeyi Amma seka rantse bemasan dazamanta a gurinba wata irin nutsuwa na saukar masa. Yau kadai ya yarda SO bala'ine dan acikin watanni uku haukacewa ne kawai beyi ba, Dole ta saka shi karbar supervision din kawai dan ya ganta suyi magana ba wai dan shi ya kamata yazo musu ba. Kamshin turarenta daya shaqa kadai ya masa maganin qishin ganinta daya addabeshi, he missed everything about this Damsel just 5month Amma jiyakeyi kaman ya shekara 10 beganta ba. Had it been he has the chance he would have hug her and feel her close to his heart ko ya rage zafin sonta dake neman zautashi. Bakinta ya kalla That looks dry, nan take ya tuna da wancen incident din ya hadiye wani mugun yawu daya kusan sakashi ya kware dole Ya bude littafin gabansa koda kawar da tunin daga zuciyarsa ya fara abinda ya kawo shi. Daga yanda yake tambayarta tasan da gayya yake hakan Sosai yai bombarding dinta da questions dan kusan duk abinda ya tambayi wani seya nemi data yi masa karin bayani akai ita kuwa ta cuna baki Wanda hakan ba karamin kara rudashi takeyiba. Suna gamawa ya mika mata jakarsa akan ta kai masa mota to his surprise bata musaba ta karba tareda yin gaba kafin ya fito. Seda ya gama sallama da kowa sannan yafita tana tsaye kofar SS Wali tana jiransa Dan haka yayi gaba ta bishi a baya. Daidai jikin motarsa suka tsaya irin kallon dayake jifanta dashi ne yasaka ta sauke kanta kasa ta shiga