← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 62

Sashe 27

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

tayi ko me? Idan ita mata r taka taji haushi gobe muganta tana Amai". Da mugun mamaki ya kalli Hajja, sosai halinta akan lamarin daya shafi yayanta yake bashi mamaki. Shikenan ita nata baya badaidai a masa Fada ba? Ko kusa beyi tsammanin haka ba a irin yanda ta daukaki Hamdan wato shiyasa akace wanda yace baya sonka baya taba chanzawa dai. Bashida ta cewa kuma dan haka ya ja kafafunsa dasukayi sanyi yai waje yanajin yanda Hajjan ke surfa masa masifa kaman zata ari baki wai an shanyeshi. Yanda yake tafiya kadai nuna maka tsantsar bacin da ransa yayi. dukk wanda yasan Abdulmalik yasan mutum ne me Sanyin hali da wasa da dariya. bashida hayaniya ko kadan dan Za'a iya cewa duk cikin yayan gidansu babu mai saukin hali irinsa Amma akace wai mai hakuri bai iya fushiba to hakance take faruwa aduk lokacin da ransa ya baci. Bashida dadi kwata kwata musamman akan abinda yake so. Irin so da kuma muhimmanci dayake bawa Hamdah akan komai nasa ya saka musu kishinta kodan kasancewarsa Namiji acikin yaya 8 da Allah ya bawa Hajja Fattu dan Haka suke ji dashi. Yana tafe yana Tunani yanda al'amuran gidan su suka fara wanda a labari ance duk laifin Hajja Fattu, ita ta fara watsa gidan ta saka musu muguwar Dabi'ar yan ubanci a tsakaninsu musamman yayanta akayi sa'a me gidan shima kan keke ne. Kwata kwata be damu da sanin wani abu da suke ciki ba idan ya fella ya tafi neman kudinsa se yayi wata uku yana yawon qasashe be waiwayi gida ba tun ma a wancan lokacin. A rayuwarsa Kudi kawai yasani kuma neman su ya saka a gaba. Hajja Fattu itace macen auransa ta farko, Yayansu takwas da ita mata Bakwai namiji daya. Khadija ita ce babbar Yarta kuma Babba a mata a gaba daya gidan dan ya auri wata mata Hajia Laure wadda Allah be tsawaita zamansu ba ta rasu gurin haihuwa tabar Yara biyu dukka Maza. Bayan Khadija Hajja nada Ummu-Salma, Munubiya, Abdulmalik, Zainab, Hasina sai kuma autarta Khausar. Bayan rasuwar Hajia Laure ya auro Hajia Amina wadda akafi sani da Hajia Shuwa ko Mama inda itama ta Haifa masa Yaya Biyar Salim, Kabir, Abdallah, Husna da Hindu. Hajia Sa'adatu ita ce ta uku wadda suke kira da Mami ita kuma Yayanta Shida. Abubakar, Umar, Usman Da Aliyu sai Sumayya da Surayya. Sai kuma Anty Halima da keda Yaya shida itama wato Sharifa, Abdussamad, Muhsin, Zuhra da Fauziyya. Babu wata jituwa tsakanin matan gidan sosai hakan ce ta shafi har yayansu musamman yan Dakin su Abdul din. Dukda a bangaren mazan da sauki basu fiya shiga alamuran Dake faruwa a gidanba haka wasu daga cikin matan...tunaninsa ne ya katse ganin kiran Hamdah a waya Dan Haka yayi saurin shiga gidan wai ta gaji da zaman shiru ita kadai. haka dai sukai wunin ranar ba dadi Sun kwanta da alkawarin gobe zasuje asibiti. Asuba ta gari Mr nd Mr s Malik. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 1 Zaune suke gaban Dr Nasir hannun Hamdah cikin na Abdulmalik din. Kusan minti biyar kenan da kiran da Dr yayi musu bayan check up din da aka musu yanzun ma result suka je karba. seda ya gama yan rubuce rubucensa sannan ya dago yana kallon su dauke da murmushi a fuskarsa, "Mr and Mrs Abdulmalik right?" Ya yi maganar yana kallon su duka. "Nasir go to the point please" ya fada dan yasan Halin Kanin nasa da was. Ya yarda da suzo gurin Nasir ne dan yasan koma wacce matsala ce ze rufe musu ita batare dackowa yaji a gidansu ba dan Hajja tace ya kawo mata result din in suka dawo yasan shi kadai ze iya masa alfarma ya chanza koda an samu matsala tunda Dan uwansa ne. Seda Nasir yayi yat dariya dan shima yana da yawan fara'a kamar Abdulmalik din sannan yace "Sakamakon bincikenmu ya nuna cewa you are all fine". Ajiyar zuciya suka sauke a lokaci daya kowanne yana godewa Allah a zuciyarsa, maganar Dr ce ta katse su inda yake cewa "Sedai ita madam dince take da yar matsala kadan from our investigation we found that she normally encounters serious pain when she is on her period and dama normally the drugs din da suke sha for relief sunada some side effect shine ya danyi affecting mahaifarta ta kasa saurin conceiving and wani abu ma is like ta samu cikin kusan two times so in yazo mata da ciwon mara se tasha wadannan same drugs din suyi flushing babyn out. Amma fa wannan ba wani serious issue bane magani kawa za'a bata insha Allah komai ze daidaita". Tun da Nasir ya fara magana ta tabbatar da ita keda matsalar ta fara kuka, shikenan ashe itace bazata haihu ba tasan yanzu yan uwan Abdulmalik sun samu makamin yakarta dole ma su sakashi yayi aure kila yanzu seya auro wannan Me kama da Mayun, wannan tunanin da tsabar kishi suka qara tunzura mata zuciya. Lallashinta yakeyi har suka iso gida bayan Dr ya hadosu da magunguna da zata sha har na tsahon wata shida. Ranar yaga ta kansa, duk wata kalma ta rarrashi da dadin bakin dayasan yana tasiri akan ta yayi Amma abin kamar yana dada angizata. "Shikenan sekiyi tayi tunda bakisan kiyi abu kadanba ki hakura ba in kuma kukan ne zeyi mana maganin matsalar se naji hun?" Cikin fushi yayi maganar dan harga Allah ta fara bashi haushi. Ya rasa da wanne take so yaji, da rashin lafiyar tata ko da kukan data tasa shi a gaba tanayi da yakeji kamar saukar ruwan zafi a jikinsa. Fada ya shiga yi mata ba kadan ba kamar ze doketa sedai ita kam ko a jikinta guri ta samu tayi zaman dirshan tana shaqar kuka shi kuma yana tsaye akanta yana surfa bala', Ganin da yayi babu sarki se Allah dan har cewa yayi in batayi shiru ba seya falla mata mari budar bakinta tace "Ai dama dole yace ze mareta yanzu tunda bata da wani sauran amfani a gurinsa". Ba shiri ya durqusa tareda janyota jikinsa gaba daya yayi hugging dinta yayi so tight at once yana shafa Gashin kanta da bayanta tare da hura mata iska a kunne. Kukan ta fara ragewa se ajiyar zuciya data ke saukewa wata na bin wata kamar Yarinyar goye. "Ya isa mana princess haba jiyanda duk kika hada gumi ga kanki har yayi zafi so kike se kin sa yayi ciwo ko" ya fada cikin wata kasalalliyar murya a ransa yana jin zafin furucinta. Yanzu har tana tunanin ciwo zesa ya qita ne? Yau ko HIV akace tana da ita a zatonta ze gujeta saboda hakan se akan abinda ma shine sula. Bayan shi ya ringa siya mata maganin da kudinsa tun ma a lokacin tana budurwa dukda hanata shansu da Mumcy takeyi se yace baze iya jure ganinta tana shan wahala ba alhalin akawai magani. Jin tayi shiru ya sa ya ci gaba da cewa "Shifa Nasir ba fa cewa yayi bazaki haihu ba hasalima har magani kina gani gasu ya hadomu dasu just 2month treatment everything will be alright hakuri kawai zamuyi". cikin sanyi gaba da yi mata bayani bayanda ya fuskanci fadan baze sakata ta nutsuba. Gyara kwanciyarta tayi sosai a jikinsa ta qara lafewa sannan tace "Toh Jaan su Hajja fa nasan bazasu yarda da hakan ba ayanzu ma suna matsamin lamba inaga sunsan ga matsalata nasanma Aure kawai zasu yi maka kilan ma wannan me kama da aljanun (tana nufin Haula) ko wannan bulalar(Hafsa) zata aura maka" ta karasa maganar tana shirin fashewa da sabon kuka. Duk da damuwar dayake tareda ita maganarta bata hanashi yin dariya ba, se yanzu ya ganota ashe kishi ne ya sakata kukan, se ya shiga tsokanarta yana cewa "Yauwa Babe gara dai ki fadi gaskiya ashe kishine kawai yake damunki kinbi kin hargitsani to kwantar da hankalinki kima saka ranki a inuwa dan aure kam inda niyyar karawa baki sani ba jira kawai nake ki haihu kina tafiya wannan wankan gidan da kika ce sedai ki dawo ki tarar da Amarya a gidannan Allah ne yasoki baki da rabon yin kuka da wuri" ya karasa yana kashe Mata ido. Pillow ta dauka ta fara jifansa tana "wallahi Aa ai kace baza kamin kishi ba". In banda dariya ba abinda yakeyi yana cewa "Aa fa Babe banda sharri a yaushe kika ji na fadi hakan" nan suka shiga zagaya falon tana kai masa duka yana kaucewa. Seda ta gaji Dan kanta sannan ta kwanta tana mayarda numfashi. Akan cikinta ya dora kansa shima yana kallon fuskarta, yanda zuciyarta ke bugawa da sauri har a kunnensa, seya dora hannunsa saitin zuciyarta ya dan danna kadan yace "kwanta kwanta kishi ba yanzu zaka tashiba". Mirginawa tayi ta ture kansa yai saurin rikota gaba daya yana dariya, locking lips dinsu yai for some minutes what he never get tired of sannan ya saketa yana kallon fuskarta. Magana yake so suyi amma ya rasa ta ina ze fara mata yasan yanzu sabon balli ze tashi amma baze jurumi ganin kukanta kullum ba, ya sani tana da zafin kishi amma dole yasan yanda Ze koya mata ta ringa daurewa, babu wanda akayiwa alkawarin gobe. Ko a mafarki be taba tunanin ze hada ta da wata mace ba amma hakan bayana nufin ya bata guarantee din daga ita ya rufe ba, ranar kuma da Allah ya jarabceshi se ya ce mata me?. Hannuwanta dukka biyu ya kama yana kallonta with serioua face yace " Hamdah". Seta tattara nutsuwarta imduka ta maida kansa dan tasan ba kasafai ya fiya kiranta da Asalin sunanta ba dole abu me muhimmanci ze gaya mata. "Hamdah kisakawa zuciyarki hakuri komai dakika gani a rayuwar Dan Adam RUBUTACCE ne. kidauka cewa hakan _*RUBUTACCIYAR KADDARAH*_ cikin kundin rayuwar mu kinji, and abu daya karki taba yarda cewa ni Abdulmalik zan qi ki saboda lalura, lalurar ma wacce bake kika dorawa kanki ba. Hamdah ke nake so, komai naki yayi min daidai da tsarina. Zan zabe ki akan mata Dubu. ke nake so bawai wani abu nakiba haihuwa ko rashinta bazesa na rabu dake ba ko na wulakantaki ba. Kin manta ranar dana karbi auranki? Nayiwa Abbah alkawarin kulawa dake iya kar numfashina.
Chapter 27 · 0% Book details