Sashe 61
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sanda yaga dama a duk lokacin daya so koma wacce irin shiga ce a jikinta. Seta saki kukan data kasa riqewa daidai lokacin daya jata zuwa cikin jijinsa, kuka take yi sosai me nuna zallar takaici da baqin ciki. Be hanata ba sema matsawa baya da yayi yana kallon yanda ta durqushe tana ci gaba da kukan kamar ranta ze fita, se kuma tausayinta ya kamashi, ya sakata kuka da yawa Infact tunda suka fara haduwa take kuka amma ai ita dince ta fiya raguwar zuciya shi kuma yana son mace jaruma. A hankali ya qarasa ya dagota tareda hadeta da jikinsa yana bubbuga bayanta a hankali "Saboda nace kimin girki shine abin kuka, to shikenan barshi na kwana da yunwa kinga kafin dare se na mutu kawai tunda ni bani da kowa mata ta bata nan bare ta kula dani gashi kuma Amaryata ba abinda ta iya se kuka" Seta dago kanta da sauri ta kalleshi, shima ita yake kallo a qoqarin son goge maganar daya riga yayi seya miqe da ita a jikinsa ya shiga bedroom din, har kan gado ya ajiyeya yaja mata duvet tareda kashe mata bed side lamp din yai pecking nata a goshi da lips ya juya ya fita. Seta gagara baccin kwata kwata, wai Amaryarsa taji yace fa to kodai ya fara shaye shaye kuma? Haka ta ringa juyi tana tunani har bata san da bacci ya dauketa ba. Inda ta godewa Allah washe gari tana zuwa makaranta aka raba musu wani mini project kuma ba'a cikin London zasuyi ba. Wani qauye zasuje can kuma kwana goma zasuyi qarin jin dadinta group dinsu daya da Umm Ashrab. A hanya suna komawa gida suna tsara yanda tafiyar tasu zata kasance, suna tsaye kofar Apartment dinta suna magana ya shigo tayi masa kallo daya ta dauke kanta lokacin da suke gaisawa da Umm Asrab. Shima ita yake kallo ransa na quna, wato shigar daya hanata ita tayi ta saka riga da skirt na wani baqin leshi yamata kyau kamar Aljana ga daurin datayi ana hango gashinta haka bayanta duka a bude saboda mayafin ba wani na kirki bane. Tsaki yayi ya wuce su ya shige gidansa bam ya buga kofar kamar meyi da wani seta tabe baki yayinda Umm Ashrab ta kalli kofar ta kalleta "Anty Hamdah anya kuwa" ta fada in between dariya dan ta dade tana spying akan Hamdah da Abdul'ahad din tun farkon dawowarsa ta lura da irin mu'amalarsu. Har Zulaiha tayiwa magana da farko taji tsoron kar yaudararta yakeyi amma se Zulaiha ta nuna mata bata zaton Hamdah da wannan halin kuma shima Mr Abdul'ahad beyi kama da mutumin banza ba kilan dai akwai wani boyayyen al'amari a tsakaninsu su zuba musu ido kawai zasu gane koma menene. Murmushi ita ma tayi batareda tace mata komai ba daga nan sukayi sallama ta shiga gida. Sanda ya shigar mata kamar wani me gida ya shiga gidansa babu ko sallama se daddaga kai yakeyi, lokacin ta fito da kayayyakin da zata tafi dasu ta ajiye akan Couch tana amsa wata waya. Kallo daya ta masa ta ci gaba da wayar ta, shima se nemi guri ya zauna yana kallon kayan data zube. Da daddaya yaringa dagasu kome yake dubawa oho haka cosmetics din data ajiye qarshe ma seyai snapping nasu da wayarsa. Gefen data ajiye Underwears ya daga Kunya kamar ta nutse lokacin daya daga daya daga cikin Bra din kome yake nema kuma oho se tayi saurin katse wayar ta iso inda yake ta re da fizgeta daga hannunsa. "Wai meye haka malam zakazo kana min bincike a kamar ka bani ajiya". Be kulata ba shima ya fige yaci gaba da neman abinda yake nema din sannan ya danyi rubutu a waya da alama text ne kowa ya turawa oho. "Ina zaki kike hada kaya" ya tambayeta hankalinsa akan wayarsa. Sedata hararaeshi sannan tace "Inda ka aikeni". Seya dago ya kalleta kadan kafin yayi kwafa ya maida kansa kan wayar, badan wani abu ba daya koyawa yarinyar nan hankali yanzu base anjima ba yanda ko ce mata akayi ta qara gaya masa maganar banza bazata iya ba. Se ya mike da kwalbar turarenta daya a hannunsa yace "Get me some food I'm hungry please" "Baza'a dafa ba" ta fada a tsiwace "I said please" ya maimaita yana mata wani irin kallo. Se kuma ta danji kunya, ko ba komai yau rokonta yayi. Ita se alokacin ma ta lura kaman ya dan rame ga hancinsa nan ya qara tsaho, to ko bashida lafiya ta tambayi kanta. Kitchen din ta shiga, simple jellop rice ta masa da vegetables already tana da kaza a oven data gasa bata ma ci ba da safe seta qara te-heating masa ita ta hado da Coca-Cola me sanyi da ruwa da dora masa akan Dining har lokacin be dawo gidan ba dan haka tashiga shirya kayan. Seda ta gama tsaf ta zuge jakar sannan ya shigo ya chanza kayansa bana dazu bane da alama wanka yayi hannunsa riqe da ledoji guda biyu. A kujerar Dining din ya zauna ya jingina kansa dayake matuqar sara masa idonsa a rufe yace "Can you please serve me?" Seta kalleshi, salon nan nasa fa ya fara takurata. Baki a gaba ta isa gurin ta fara zuba masa abincin yana binta da kallo duk motsinta har ta gama ta tura masa gabansa bayan ta tsiyaya masa ruwa da lemo dukka. "Ke bazaki ci ba" ya tambayeta yana kai lomar farko bakinsa, seta daga masa kai Alamar Eh. Shiru sukayi duka yana cin abincinsa lokaci lokaci yana kallonta ita kuma tana yan danne danne a laptop dinta. "Take this" ya fada yana nuna mata daya daga cikin ledojin daya shigo dasu, seta taso kawai ita ma yanzu bata fiya son yawan maganar kuma ba takai hannu zata dauka wadda take kusa da ita yace "Not this one the other one" yana pointing dayar ledar. Sanyin data ji ya tabbatar mata da mene a ciki seta ja kujera ta zauna har dimples dinta na lotsawa saboda murmushi ta bude Ice cream din ne kuwa favourite flavor dinta. Seta kalleshi lokacin da take kai spoon bakinta tace "Thank you". He only smiled saboda yanda yake jin sa duk se a hankali. Ice cream din take sha har wani rufe ido take tsabar dadi shi dai kallonta kawia yakeyi dan ya gama cin abincinsa. Magunguna ya ballo a dayar ledar yace ta bashi ruwa mara sanyi abin kirki ba musu ta tashi ta dakko masa har tana tambayarsa meyake damunsa se ya nuna mata kansa kawai yana dan kwanciya akan kujerar idanunsa akanta. Seda ta shanye rubar gabanta tas sannan ta dauki dayar takai fridge ta ajiye, har lokacin yana zaune idanunsa a rufe se kuma ta danji dausayinsa. Tasan lafiya qalau baze zauna haka ba kila da yanzu tayi kuka. "Ko na kira maka Dr" ta fada tana tsaye akansa fuskarta da alamar damuwa. Haka take akwaita da tausayi sosai idan taga mutum bashida lafiya. "No i will be fine" ya fada yana qoqarin miqewa saboda mararsa dayaji ta wani murda masa kamar zeyi ihu, a daddafe ya nufi kofar seya tsaya saboda wani amai dayaji yana taso masa lokaci daya ba shiri ta isa inda yake jin yana kakarin aman tana zuwa kuwa ya wanke musu jiki tas daga ita har shi. Sannu ta ringa jera masa har ya gama dukka jikinsa yayi laushi. Zaman dirshan yayi a gurin jin wata juwa na neman kadashi ciwon da yakeji yana lafa masa. Duk seta tsure tana tunanin meya sameshi haka. "Help me remove my shirt please" seta tsaya tana kallinsa, ita ta ina zata iya tabashi harta cire masa riga. Wai kodai yana manta dokokin musulunchi ne? "Taimako ko a addini Halal ne _Ayush_" ta tsinkayi muryarsa. _Ayush_ din daya fada ne ya kashe mata jiki tareda sakata wani shauqi, seta tsugunna ta kama buttons din a hankali ta hau cirwa yana bin fararen yatsunta da kallo yanda suke trembling kaman me taba maciji. Seda ta ballesu dukka ya dan dago ta zare rigar gaba daya tsikar jikinta se tashi take da ganin kwantattun gashin dake hannayensa taqi ko yarda ta daga kai ta kalleshi. "Aush" ya fada yana dafe kijinsa da cikin rashin sani ta karceshi da farcenta setayi saurin daga ido ta kalle shi tareda kai hannunta gurin tana shafawa tace laushin jikinsa na ratsata. "Yi hakuri ba'a sanina bane". Kallon dayake mata ne cikin ido ya fargar da ita abinda take aikata wa, seta miqe cikeda kunya ta fara kame kame tana cewa "In zaka iya tashe kaje kayi wanka sena gyara gurin" cikin kwaikwayon muryarta shima yace "Bazan iya tashiba ki dagani". Setasa hannayenta ta rufe fuskarta dasu tana cewa "ka bari bana so". Nan ya samu abin tsokanarta, moment din seya tuna masa sanda take Hamdah yake Abdul'ahad a zamanin rayuwarsu a BUK. Kamar bashi ya gama Amai yanzu ba ya mike tsaye yana cewa "Let me go and fresh up ki bari na dawo sena gyara wurin" ya fice dagashi se dogon wando da singlet dukda karfin hali kawai yakeyi. Bayan ta fita tsaf ta gyara gurin hatta da rigarsa seda ta wanke sannan ta shiga wanka ita ma. Batasan ya ya qare ba dan har dare bata kuma jin duriyarsa ba kamar ta leqa apartment dinsa amma ta fasa haka tayi bacci dan da wuri zasu tafi washe garin. Jiki ba kwari ta ringa abu da safen dan har mafarkinsa tayi dan haka tana tashi saboda shi ta dora breakfast. Bayan ta gama tayi wanka ta shirya tsaf cikin baqar Abaya mara Adon komai haka fuskarta fayau turare kawai ta fesa. Seda ta fita da trolly dinta kafin ta dakko basket din data saka masa abinci ta nufi gidan kirjinta na bugawa ta danna door bell din jiran minti daya ya bude. A kallo daya ta hango ramar dayayi ga kuma Cannular data gani a hannun sa seta bude bakinta a hankali tace "Ya jiki?" Cike da mamakin ganinta ya amsa da "Alhamdulillah" dan ko kusa be kawo ita din ce ba, ya zata Benjamin yaronsa daya kirane ya iso, se ya matsa tareda bata hanya yace "Bismillah". Gaba tayi yana binta a baya karon Farko data fara shiga gidan.