← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 62

Sashe 59

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ke iya qarfinta ganin suna yawi akan titi Allah ma yaso su kadai ne babu kowa saboda dare ya farayi dan har sha biyu ta gota. "Mara kunyar qarya ashe kina tsoron mutuwa nazata kin qagu ae kibi tsohon mijinki tunda gashi kinje can kin kasa zama ko tunaninsa kike" ya fada yana matsa cikinta da dan qarfi. "Wash Allah na" ta fada saboda azaba dan gurin aikinta ya matsa, dukda baya mata ciwo kwata kwata bata san wace irin ooeration bane wata hudu amma kamar ba'ayi shi ba dama ba dinki bane ko fatar gurin ka kalla layine guda daya inda aka yanka amma yanzun daya danna taji zafi kam. Seyai saurin kunna fitilar motar yana kokarin daga rigar dan shaf ya manta da aiki a jikinta. Wani irin yar yaji tundaga kansa har kafarsa lokacin dayai arba da farar fatar jikinta da yake a shafe kaika rantse bata cin abinci ma bare aje batun yaya biyu sun zauna aciki. Saurin sakin rigar yayi at the same time ya dagata cak ya maida ita sit dinta. Tafiya suka cigaba babu me cewa wani qala har suka qaraso gida, seda yai parking motar sannan ya bude ya fita, kofa ya bude mata itama ta fito tana cika tana batsewa kamar zata fashe shidai se munafukin murmushi yake binta dashi. Ransa fes ko haka aka tsaya ubangiji ya wanke masa damuwarsa. "Hajia kinmanta jakarki" ya fada ganin tayi gaba ba tareda ta dauka ba. Badan keys dinta na ciki ba da bar masa zatayi , se taja ta tsaya ta zumbura baki, girgiza kansa yayi irin zanyi maganinki kafin ya dauki jakar ya biyo bayanta tana tsaye har ya wuceta. Seda ya bude mata kofar da kansa kafin yace " Oya shiga Good night" ya janyota jijinsa tareda sakar mata light kiss a goshinta da kan lips dinta. "Ji mana" ya fada harta turo kofar dan gani take in taci gaba da tsayawa to kuwa bazasu kwashe kalau ba ai ita ba yar tsanar roba bace da ze ringa daquma yanda yaga dama. "Next time in zaki fita kiringa shiga ta mutunchi please kar na qara ganinki da wannan rakani gantalin" ya fada yana juyawa abinsa, seta tsaya kamar wadda aka kafe. Inba rainin hankali ba ita ze kalla yace wai ta ringa shiga ta mutunchi look at who is talking about decency. Tsaki taja tayi shigewarta cikin gidan ranta a matuqar bace ga Ice cream din da bata shaba ga bata mata lokacin da yayi haka ta kwana tana qunquni. Knocking din da ake yi ne ya tada ita da Asuba, idonta cike da bacci ta sakko daga kan gadon tana mamakin waye wannan haka kuma seta kejin kaman kofar Bedroom din ake bugawa kodai bacci ne. Rigar jikinta me santsi ce da bata kai mata ko guiwa ba haka ta sake dogon gashinta daya ke har tsakiyar bayanta. Dan mayafin data gani ta dora akan nata dukda be rufe komai ba ta bude kofar Bedroom din ta fito. Seta tsaya turus tana qara ware idanuwanta ta tabbatar daidai take gani ko kuwa dai magagin bacci take, Guru ne zaune akan couch ya harde qafa daya kan daya yana juya wayarsa idonsa fes akan kofar se tayi saurin komawa da baya saboda yanayin kayan jikinta. Tafi minti biyar a tsaye cikin dakin ta ma rasa me zatayi, abun ya kai mata har wuya wannan wane irin iskanci ne da rainin hankali waima ta ina ya samu hanyar shigo mata gida? Kamshin turarensa da kuma takun sahun takalman dataji suka tabbatar mata ya shigo dakin, seta daure fuskarta ta mau ta juyo tana kallonsa "Wannan wane irin is..... " "Ya isa malama ni ba surutu ya kawoni ba ki wuce ki samamin abinda zanci yanzu ina da meeting karfe 8am". Saboda tsabar mamaki seta nemi guri kawai ta zauna tana binsa da kallo, ta ma rasa abinda zata ce masa. Dakyar ta samu courage din cewa "Zaman dadiro mukeyi ko yaya" "A'uzu billahi" ya fada tareda saurin kallonta dan da hankalinsa yana kan wayarsa. Seyaci gaba da cewa "Karki qara dangantani da wannan baqar kalmar ko nayi miki kama da dan iska ne?" Seda ta watsa masa wani kallon banza sannan tace "Meye marabarka da shi? Taba jikin matar da bataka ba ko kuma shiga gidan mace ba tare da izini ba ai kafi qarfin a kiraka da Dan iska ma sedai kwart....." Bata samu damar qarasa ba saboda cafkar da yayiwa bakinta. Cikin tsantsar muguntar da take nuna fushi yake kissing dinta tsabar Azaba seta saka kuka dukda baya fita saboda bakinta da yake a rufe. Seda ya tabbatar da ta horu sannan ya saketa yana maida numfashi yace "Gobe ma ki qara jifana da wannan kalmar na rantse da Allah sena nuna miki qarshen Kwartanci ki kuma tashi kiyi abinda nace in ba haka ba kinsan in fada sena cika" yai ficewarsa daga dakin. Kuka ta shigayi wiwi, wannan wane irin wulaqancine? Zawarci hauka ko kuwa saboda ta baro qasarta zuwa wata duniya shine ze biyota ya tozartata? Meyasa be taba mata hakan ba lokacin da suke a Nigeria se yanzu da ya ganta ita kadai inda bata da me kareta. Bata san lokacin data kwashe tana kukan ba saboda baqin ciki ta kasa denawa. Kamshinsa data qara jiyowa kusa da ita shiya sanar mata da dawowarsa, bata dago ba haka bata dena kukan ba yana tsaye yana kallonta hannayensa zube cikin aljihunsa, kasa jure kukan yayi a hankali ya qarasa inda take ya dagota gaba daya zuwa jikinsa ya mata kyakykyawan masauki a cikin broad chest dinsa. Luf ta kwanta lokaci daya tana shaqar daddan turarensa dake kwantar mata da hankali. Bata san meya sa take samun nutsuwa a jikinsa ba kwatankwacin lokacin da take tare da Abdulmalik dinta kuma abun ya zarta nada. Lokacin baya a duk lokacin daya hada ta da jikinsa tana so amma tanajin tsoron kasantuwar haramacin haka amma ta rasa a wannan haduwar meyasa batajin haka, da so samune su dawwama a haka kar ta taba rabuwa da jikinsa. Seta fara qoqarin janyewa tunawa da haramcin abun da kuma sabon rainin hankalinsa gareta. "Ka sakeni malam" ta fada a tsiwace tana janye jikinta, seya rufe mata baki da hannusa sannan ya dago fuskarta da daya hannun bayan ya saketa yana kallon idanunta zuwa qaramin bakinta da take budewa da niyyar sake masa wata masifar, he just can't resist her lips, seda yai brushing lips dinsa akan nata cike da mugunta ya cijeta kadan akan lips sannan yace "Karki qara furta cewa na sake ki baby girl" seya jata kaman yarinya dukda yanda take turjewa amma seda ya danganata da kitchen. Gefe ya tsaya yana cewa "10 mins ki samanin abinda zanci Malama I'm running out of time" ya shiga danna wayar daya zamar masa dabi'a. Kayan jikinta take kallo tana so taje ta dauko koda Hijab ne ta saka dan Jarabar tasa kuma ta zarce hankali gara ta dafa koya barta ta huta amma ya kasa ya tsare hanyar, ganin da tayi hankalinsa baya kanta yasa ta shiga aikin a ranta ko ta zageshi yafi cikin kwando harta tafasa masa ruwan Tea da toast bread ta dungurar masa da plate din a gabansa fuuu ta wuce. Da murmushi ya rakata kafin ya kalli abincin, mug din ya daga ya fara kurban tea din a hankali wani irin dadi da gardi ya masa kamar be taba shan Tea a rayuwarsa ba lokaci daya ya bude ciki ya kwankwade. Beci bread din ba saboda he isn't fan of bread at all se ya juya kaman ze koma dakin kome ya tuna kuma se kawai ya fita. A daidai kofarta suka ci karo da Zulaiha da take qoqarin shiga. Kallon mamaki ta ringa binsa dashi a ranta tace "ikon Allah Mr Abdul'ahad a apartment din Miss Hamdah so surprise" ita dai suka gaisa ya matsa mata ta shiga tana cigaba da juya abin a ranta. Kuka kashirban ta tarar da Hamdah tanayi kai kace Mumcy ce ta mutu ko wani tana ganin Zulaihan ta qara volume shikenan abinda take gudu ya afku wane kallo mutane zasu fara mata dan ta tabbatar Zulaiha ta ganshi dan da fitarsa da shigowarta bekai minti daya ba. Seta shiga kallonta kaman me son gano wani abu tattare da Hamdah. Shidai taganshi well dressed da alama ma office ze tafi kuma dai babu alamaun a gidan ya kwana ita kuma gata da kayan bacci tana kuka, se kuma wata zuciyar tace mata "they are all from Nigeria probably he is her relative, dukka su biyu babu me yawan magana bare su nuna haka" wannan tunanin yasa ta zauna a kusa da ita. Haquri ta shiga bata Allah sarki se kukan da take yi ma ya kore zargin komai daga zuciyarta haka tayita fama har Hamdah tayi shiru sannan ta shiga tayo wanka suka fita saboda dama wani guri suke son zuwa da sassafen. Allah ya taimaketa tun daga wannan ranar bata qara kodajin horn din motarsa a gidan ba. Batasan inda ya tafi ba koma ina ne shi ya sani ita dama ya tafi kenan kaman yanda dama aka ce baya wuce sati daya sati biyu in kuma ya tafi se an ganshi. Ranar wata Monday kusan two weeks da tafiyar Guru da wuri ta shiga school kuma ko motarsa bata gani a parking lot dinba. Wuraren karfe biyu ta shiga cafeteria dan taci abinci bata samu ta karya a gida ba sannan tunda ta shiga makarantar take busy. Nurain wani course mate dinta, dan Nigeria ne shima dan asalin Kebbi State. Tun ranar daya fara ganinta a Airport yake bibiyarta har ya zama na ashe ma ajinsu daya. Yarone qarami dan befi da shekara daya da dan wani abu ya girme mata ba amma ya nace tunda ya ganta wai shi sonta yakeyi duk kuwa data gaya masa itafa ba budurwa bace amma yace yaji ya gani a cikin school kamar Jela kullum haka yake binta yauma haka tana shiga Cafeteria ta hangoshi da wani Austin da Juliet suma abokanan karatunsu ne suna cin abinci. Table din da suke ta qara suka gaisa kafin ta koma separate table tayi order abinda zataci tana ta baza hanci jin kaman kamshin turaren
Chapter 59 · 0% Book details