Sashe 6
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasa da zoben hannunta dan bazata iya jure Eye contact dashiba. Wasu irin abu take ji suna fitowa daga idonsa suna shiga nata. Bata san meyasa she is restless around Dr Guru ba ta rasa wane irin Chemistry ne a tsakaninsu datakejin wani abu game dashi da ko Abdul dinta bata jinsa haka. Dukda bata kallonsa amma tanajin yanda Idonsa keda effect akan duk wata gaba ta jikinta. Tamkar scanner haka yake binta da kallo yanajin baze taba gajiya da kallon wannan halittar ba. Gudun zuciyarta ne ya qaru yayinda qafafuwanta suka fara rawa tamkar bazasu iya daukarta ba, ta gaji da tsayuwa dashi kamar wanda yake shirin tsafanceta gashi yaqi karbar jakarsa daga hannunta. Dakyar ya iya katse shirun dan be ki su kwana a haka ba cikin wata irin murya mekama data Wanda ya suma cikin mayen SO Kamar me koyon magana Haruffa a rarrabe Ya kira sunanta HA...M...DA...H!!!! Lokaci daya tsigar jikinta suka tashi danjin sautin sunanta a bakinsa, be barta ta dawo daga shock din ba ya qara mata da "I missed you HAMDAH......." *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 0 Dariya sosai ta bashi ganin yanda take zare ido tana kalle kallen gefe Kaman Me tsoron kar wani yaji abinda ya fada. He is totally lost Dan haka inma yace ze chanza zancensa kara fallasa asirin zuciyarsa zeyi. Hannayenta yariko yana kallonta straight in to her eyes sannan yace "yes I Miss you Miss Ammani, i missed your troubles, your voice, ur scent, infact I missed everything about you Hamdah". Ita dae inbanda kallonsa babu abinda takeyi, she couldn't believe it wai daga bakin Guru takejin wadannan maganganun, kalaman da a wurin Abdulmalik kadai take samun irinsu. Hure mata ido yayi tareda dage mata gira daya yace "yadai yammata kina admiring kyau nane ko, to kallon ya isa haka karki ragewa budurwata farashin saurayi". Haka kawai seta Tsinci kanta tayi da jin haushin kalmarsa ta karshe "wai budurwarsa" se kawai ta dauke kanta gefe tareda turo baki sannan tace "Toh naga ai dai nawa saurayin ma yafika kyau Kuma shi Fari ne kawai irin wannan ne bashida shi" tayi pointing quarter million sajen sa. Seda yayi karamar dariya yarintarta nadaga abinda yake Kara birgeshi da ita. ya lura duk maganarta is straight from her heart Dan haka yayi niyyar tsokanarta yace "Iye kice kina da saurayi oya gist me about him". Aikuwa Kamar me jira ya tambayeta nan tafara bashi labarin Abdulmalik da irin son da takeyi mishi. At this point Bakaramin dauriya yayi ba gurin saita nutsuwarshi. wani masifaffen kishi ke cinsa, kallon ta yake yanda ta dage tana bashi labarin Abdulmalik din "bari ma nanuna maka picture dinsa" ta fada tana kokarin ciro wayarta daga jaka seyai saurin tareta "Aa you don't have to keda zaki kawomin shi har office ya gaidani" murmushi me kyau tayi "kuma fa haka ne sir zan kawo maka shi kaganshi sosai you will believe what I'm telling you". Gaba daya jiyai wata zufa na keto masa, in har tana son saurayinta haka toh shi a wanne matsayi? yake anya ma zata bashi damar gwada tashi sa'ar a matsayin masoyi kuwa? Gaba daya seyaji komai ya qulle masa, yanzunma shawarar Fahad ce akan yafara janta ajiki amatsayin Abota. Gashi daga farawa tana neman tarwatsa masa zuciya da kalaman daya kira da muggan kalami. Hannunta dake cikin nashi ya matsa kadan tareda cewa "hey is ok lallai wannan guy din yayi sa'a daya samu irin wannan zukekiyar yarinyar". kunya taji Dan haka tayi saurin rufe fuskarta da hannunta da har lokacin yake cikin nashi tana murmushi. Wani irin shock yaji lokacin da hannunsa ya sauka akan fatar fuskarta, laushi da santsin dayaji baze misaltu ba se yai saurin zame hannunsa dan yaga alama tana so ta chanza masa layi. Kallon agogonsa yayi sannan yace "I get to go se mun kara haduwa Amma fa you didn't replay me" Bude idonta tayi tana kallonsa sannan ta watsa hannu tace "What?" Yana kallon Impression din kan fuskarta yace "I said I missed you bakice komai ba" yakarasa da muryar shagwaba Kaman me shirin yin kuka. Ba shiri ta fara Dariyar yanda yayi kalan tausayi, "Oh dariya ma na baki ko?" ya fada yana rungume hannunsa a kirji har lokacin kallonta yakeyi. Seta tsayarda dariyar tata sannan tace "Ok what do you want me to say?" "Tell me you missed me too mana" ya kara marairaicewa kaman me shirin kukan gaske. Wata Dariyar takeyi sosai Dan yanda yadage akan inbata fada ba zeyi kuka, dakyar ta daure tace "Ok ok I missed you too shikenan". "Are you sure" ya tambayeta "Yes I'm very sure" ita dai she just say it dan dai kawai Bawai har zuciyarta hakan bane. Gaba daya bata da nutsuwa duk lokacin data ke a kusa dashi, "Thank you dear take good care of your self you hear" Ya fada yana kissing fararen tiny fingers dinta daya rike a hannunsa. Setayi saurin zamewa dan abun nasa kuma ya fara bata haushi Da "Ok sir" tabashi answer. Allah Allah take ya tafi. Motarsa yashiga Tareda yi mata key yana daga mata hannu. Samun kanta tayi da daga masa hannu Itama harya wuce. "Thank God" ta fada. Juyo wannan dazatayi sukayi 4 eyes da Abdilmalik daya kumbura kiris yake jira ya fashe, idanunsa sunyi ja tsabar kishi. Ba karamin tsorata Tayi da ganin yanayin saba dan tasan be iya fushi ba, yau Allah ne kadai ze kashe wannan rigimar gashi bata san iya abinda ya gani ba. Kila tun dazu yana tsaye Sir Guru ya riqe hannunta. Harta qarasa kusa dashi tana sake sake a zuciyarta da yake ita ma gwanace se kawai "Jaan yaushe kazo Ina nan narako sir guru shiya zo mana supervision bari na dauko bag dina mutafi" tayi gaba Kawai dan bata sa ran ze amsa ba kuma ko me ze fada baze mata dadi ba. Da kallo yabita kawai Har ta shige cikin building din yayi kwafa ya shiga cikin motar yana jiranta. Wato ita bata ma lura da bacin ransa ba ko kuma shareshi kawai tayi, zata dawo ta same shi seta gaya masa wane dan iska ne wannan data zo tana wangalewa baki suna dariya harda kama hannunta. Yana wannan tunani tadawo se jin rufe kofan mota yayi. A masifance yajuyo yana kallonta, yama rasa ta ina ze fara. dakyar ya iya nemo kalmar "uban waye wannan na ganku tare kina washe masa bbaki har yana rike hannunki?" Murmushi tayi kawai tana kallonsa. "Oh dariya ma kikeyi wato ga dan iska yana magana ba" se kawai ta kwashe da dariya dan gaba daya fadan beyi masa kyau ba. Aikuwa Kamar ta tunzurashi nan ya dage ta inda yake shiga batanan yake fita ba. gajiya dajin fadan nasa tayi Dan haka tayi saurin saka hannunta ta sakalo wuyansa sannan tarufe masa baki da dayan hannun tayi pecking hannunta dake kan lips dinsa. Ta sani dole yayi shiru, kokarin cire hannunta dayai wa lips dinsu katanga yakeyi amma ta hanashi sema baya da tayi tana wani killer smile tace "not now dude". Seya koma jikin kujera ya kwanta kawai yana kallonta dan daga Dan Rainin hankali se Hamdah yarinyar dagama gane lagonsa. "Easy mana haba se fada kake tayi haka kawai kasamin kanka yayi ciwo wai ma bana gaya maka lecturer dinmu ne fa. Sir Guru ne fa danake Baka labarinsa. Binta kawai yake da kallo yana jin yanda take tsarashi. Shi dai tasa jarabawar kenan Allah ya dora masa Son wannan yarinyar, tana da matukar tasiri akansa duk da yanda zuciyarsa ke masa kuna amma bayanda ya iya. Abu daya yasan yana maidata cikin hankalinta wato ya shareta dan haka ya janye hannunta Dagajikinsa ya tada motar suka bar asibitin hankalinsa kacokam ya maida kan tukinsa. Yana jinta tana cewa Zata ci shawarma, seta suka zo kofar Down town ya ciro ATM car dinsa ya mika mata tunda tasan pin din. Seta tsaya tana kallonsa tabbas tasan ransa ya baci tunda har ze ce taje ta siyo abu da kanta. Abdulmalik din da saboda ita ya mayarda dukka motocinsa super tint karma a ringa ganinta. "Na koshi" ta fada a sanyaye . Ga mamakinta setaga ya maida ATM din inda ya dakko shi. Har sukaje kofar gidansu be qara ce mata komai ba. Yanayin parkingya cire lock din motar alamar ta fita kenan lalai abin nasa da gaske ne. Dole ta tattara duka nutsuwarta ta fuskance shi. "Believe me I'm all yours Jaan, you have me. Wannan daka gani he is only my lecturer wallahi babu komai a tsakaninmu". Ya yarda amma yana so ya shigar da ita saiti sosai dan haka seya daga kafada tareda cewa "what ever". Se kawai ta saka kuka, mataki na qarshe kenan datasan dole baze shareta ba. Aikuwa tuni ya rikice yana bata hakuri. Yana son yarinyar to the extent baya iya daukan fushi me nisa da ita addu'ar sa kawai Allah ya mallaka masa ita Kuma yaga alama lokaci yayi da ya kama ta ta kasance agidansa tun kafin wasu su masa kwace. Kafin wani lokaci ya ware Dama kukan bana Allah bane suka shiga hirarsu Kaman basu taba samun wata matsala ba,juyawa sukayi siyo shawarma da Ice cream din bayan sun dawo ya ajiyeta ya wuce gida. Kusan sati uku kenan da faruwar wancan incidence din, lokaci lokaci Dr Guru kan kirata wai su gaisa sannan har a whatapp sukan danyi magana lokaci lokaci Musamman in yayibposting wani abu that is related to Genetics field din dayake wanda itama anan take so tayi specializing to anan ne yake samun dama suyi magana sosai dukka inform of lecture. A hankali sabo ya shiga tsakaninsu, they are getting to know each other dan zuwa yanzu tasan abubuwa da yawa akansa. Gidansu, Kannenshi da Yayyenshi dukka tunda yana saka pictures dinsu. Ta fuskanci kaman shi Kadae Ne namiji a gidansu. Koda wasa bata bari Abdulmalik yasan alaqarta da Guru ba dan ma yanzu haduwarsu ba sosaiba . Ya fara aiki a wani Oil Refinery a Lagos, Duk da kaurin Albashin amma kwata kwata beyi murna da samun aikin ba, yaso ace wadanda yayi applying a NNPC na Kano ne suka fara fitowa amma yasan ko giyar wake yasha be isa