Sashe 43
Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kai bakace ma da ita yake magana ba. Harararsa tayi qasa qasa sannan tayi qaramin tsakin ai kuwa ya dalle mata baki da hannunsa yana cewa "Naga alama ke auran ma rashin kunya ya qara koya miki harda yimin tsaki senayi maganin wannan bakin naki naga alama tunda bashi da control". Bata kulasa ba se shafa inda ya bigeta da take tana masa Allah ya isa a zuciyarta har ya wuce Gadar Kabuga taga yana shirin daukar wata hanyar daban. " Malam ina zaka kaini nifa gida zanje" ta fada cikin zafin rai, seya kalleta yayi murmushinsa da iyakacinsa gefen baki ba tareda ya bata amsa ba yaci gaba da tuqi abinsa zuciyarsa fes kamar an wanketa da Hypo, ganinta zaune a kusa da shi yafi komai dan haka yaringa yawo dasu a gari kamar sun rasa abinyi, shiru tayi masa dan tayi alqawarin bazatayi masa magana ba in yaga dama su kwana suna garari a titi be dameta ba. Wayarsa ce ta shiga ringing, 'Wife' ta gani akan screen din seta dauke kai lokacin da shima ya juyo ya kalli wayar, murmushi yayi dan yaganta sarai yanda ta wani harari wayar kamar matar tasa ce a gabanta se ya daga tareda saka wayar a speaker "Hello Yaya Abdul ina ka tafi ne muna ta jiranka gashi har Hamdah ta fara rigimar namanka and wai Aunt Berbie din ta tafi" Ni'ima ta fada cikin murya me nuna tsananin rauninta ko kuma wani yanayi na rashin lafiya. "Bana hanaki doguwar magana ba" ya fada batare da ya amsa mata tambayarta ta farko ba. "I'm sorry Sir" ta fada tana murmushi, se yace "Bawa Angel wayar". Miqawa Hamdah wayar tayi ta kuwa karba da saurinta " Daddy where are you come back please lets go and find Aunt Berbie she left Uncle Yusuf's place" cikin siririyar muryarta me dadi take magana cike da shagwaba. Kwaikwayon muryarta yayi shima yace "Don't worry Angel Daddy will bring Aunt Berbie home soon and she will forever stay with us you hear?" Tsalle ta farayi tana murna ta shiga gayawa Mamanta Daddy yace ze kawo musu Aunt Berbie da ita zasu koma UK, murmushin karfin hali kawai Ni'ima keyi sukayi sallama ta kashe wayar. Duk yanda taso taja Maryam da hira ta tambayeta wani abu akan Hamdan qi tayi daga qarshema excusing dinta tayi ta tafi dakinta ta kwanta tunda basu saba bama, yau ita ma ta fara ganinta. A bangaren su Hamdah kuwa seda aka kira sallar magrib suka dauki hanyar gida lokacin kamar zata fashe zabar fushi. Wani rainin hankali ya kwace mata wayoyi ya kashe ya zuba su a aljihunsa. Duk yanda yaso ya jata da magana banza ta masa har abin ya bashi haushi shima ya shareta, seda suka zo kofar gidansu ta kalleshi ganin ya samu gefe yayi parking yana jira ta fita seya tuna mata da haduwarsu ta qarshe ranar daya dawo da ita daga school da magriba kamar irin lokacin, "Ka fita ka hau Napep zan shiga da motan ciki". Seya kalleta yana jin sonta yana fizgarsa adukkan daqiqa, ji yakeyi kamar ya janyota jikinsa ko hakan ze rage masa radadin missing dinta dayakeyi, kujerar ya gyarawa zama sosai ya kwanta yana cigaba da mata irin kallon dayake ladabtar da ita a shekarun baya, akwai abubuwa dayawa daya kamata su tattauna akai amma bayanzu ba har se yayi nasarar dakatar da wannan auran da take shirin daurawa amma ta yaya? Dole ya nemi lokaci su zauna da ita to amma besan kwanaki nawa ya rage auran nata ba dan haka se yace mata " Saura kwana nawa ne ki qara daura auran Bazawara". Tunda ake gaya mata kalmar bata taba mata muni irin na yau ba, ita Abdul'ahad ze kalla ya kira da bazawara lallai wato ya goge shafinta kenan tunda har tayi aure, se kawai ta saka masa kukan da take ta dannewa. "Ya haka kuma daga magana se kuka kamar Matar Mamaci, ops namanta ashe ita ce to kiyi shiru dan Allah inkin shiga ciki se ki ci gaba karki saka min ciwon kai". Ai seta qarawa kukanta volume dama neman yinsa take yanzu kuwa ta samu dalili, " Bazata girma ba halinta yana nan" ya fada cikin zuciyarsa yana dan murmushi, hannunta ya kamo yana murzawa a hankali wani irin electrification na shigarsu dukka biyu "Nifa wasa nake miki magana shine zaki fara kuka ni mantawa nayi da halinki naje na sakawa yarinyata sunanki gashinan itama ta zama fitinanniya irinki bata da aiki se gagara". Harararsa tayi tana murguda masa baki batayi dai magana ba, peck yai mata akan lips dinta dasuke matuqar birgeshi sannan yaja da baya yana cewa "Tashi ki fita please nasan Matata tana can tana jirana nasan ta fara missing dina" ji tayi kamar ya caka mata mashi akan zuciyarta, wato matar sa tana jiransa dan haka cikin zafin rai tace "Ai ba daure ka nayi ba bakuma nace ka biyo ni ba, se ka tashi ka fita ka bani motata". " Yi hakuri Hajjaju ba guduwa zanyi ba ina zuwa gida zan bayar a dawo miki da ita kin san ni ba dan fashin mota bane da in na dauka bana dawowa da ita" ya qarasa yana kashe mata ido daya. Wata bala'in kunyarsa ce ta kamata, ashe be manta da motar sa ba, cikin son nade tabarmar kunya tace "Nima ai ba Sata nayi ba kuma all this while motan ka tana nan a ajiye yanzu ma jira a dakko maka ka tafi da ita" se ya katseta yana cewa "Aa ai ni kuma bana maimaita aji, innayi gaba na tafi kenan ki riqe ki qarawa wannan baqin mijin da zaki aura tunda naga ke baya kika ci gara ma wancan ya kai ki nunashi a matsayin miji wannan kuwa sedai ki ringa boye shima har na tausayawa yaran da zaki haifa I'm sure se sun ringa questioning naki akan meyasa kika aure shi wai ma saura kwana nawane" yanda yake maganar ze nuna maka zallar kishin da yake cinsa. Rainin hankalin nasa ya fara yawa, mijin nata zece wa baqi se kace shidin farine ne dan haka taja jakarta da wayoyinta daya dora mata akan cinya ta bude motar sannan tace "Seka aika a tambayo maka ai kuma koyafi Coal baqi a haka nake sonshi yafi min kai sau dubu" ta fice daga motar. Lokaci daya idonsa yayi Ja, jijiyoyin kansa suka tashi rudu rudu. Wace irin kiyayya yarinyar nan take masa ne haka, wacan lokacin ma fa haka tace masa, meya ragu dashi, menene bashi da shi da bazata soshi ba fisabilillahi. Harya koma gidan Yusuf yana wannan tunanin a zuciyarsa, mamaki fal ya cika Ni'ima da Yusuf daya fito rakasu dayaga motar da Hamdah tazo da ita dazu, kallonsa kawai ta ringayi lokacin dayake bawa Yusuf saqon ya kaiwa Hamdah motar gobe sannan ya karbi little da tayi bacci daga hannunsa ya sakata a mota. Ko a hanya babu wanda yai magana a cikinsu, dukda tarin tambayoyin da take dasu amma babu fuska, tasan dole za'ayi haka dama yanzu kam dolenta ta nema masa mafita kilan hakan ya tabbatar masa da irin qaunar da takeyi masa, zatayi koma menene dan taga mijinta yasamu cikon farin cikinsa koda kuwa hakan yana nufin rasa nata. Number Hamdah data dauka a wayar Maryam batare da sani ba ta qara dubawa ta tabbatar tana nan yanda take sannan ta kalleshi tausayinsa na ratsata. Tasan so, dan haka bata ganin laifinsa akan duk abinda yakeyi ita ma irin yanayin da take ciki akansa kenan, ita take sonsa, ta sani ya aureta ne kawai badan yana sonta ba sedan tausayi dan haka tayi alkawarin sadaukar masa da nata farin cikin ta nemo masa nasa ko ta halin yaya kuwa. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 3 Tafi awa biyu da kwanciya amma ta kasa bacci, Wani irin ciwo takeji har cikin zuciyarta kamar ana hura mata wuta. kallon Abdul'ahad dayake ta faman aiki a cikin system dinsa tayi tausayin kanta na dada kamata, se kawai ta saka kuka abinda kadai tasan yana janyo mata gaba dayan hankalinsa kanta kenan, tariga ta gane lagonsa ta wannan bangaren aikuwa babu shiri ya ture system din ya isa inda take a kwance ya dagota "Menene Ni'imatullah, wani gurin yana miki ciwo ne" ya fada yana duddubata dan ya tabbatar da lafiyarta. Seta tsagaita da kukan har lokacin be bar tambayarta ba dan haka tace "Ba kaine ba tun dazu ka shareni bakayi min magana ba na tambayeka meyake damunka kace babu komai" seya ja da baya yana dungure mata kai. "Amma yarinyar nan kin rainani shine zaki fara kuka salon ki daga min hankali ko to ki tabbata sena hukuntaki kuwa" ya fada yana tashi daga kan gadon. Hannunsa ta riqe tashiga bashi hakuri amma ya shareta sema system din sa daya janyo ya ci gaba da abinda yakeyi. "Yaya Abdul" ta kira sunansa idanunta akansa, ita dai Allah yasani tana son Abdul'ahad tun bata san menene so ba, tayi rainon soyayyarsa a zuciyarsa tun tana yar mitsitsiyarta. Seda ya gama abinda yake tsaf sannan ya juyo gaba daya yana kallonta "Yadai Yammata kike kallona haka" ya fada yana dage mata gira daya, setayi murmushi tareda janye tagumin da tayi sannan tace "Yah Abdul yau naga Hamdah, tana da kyau kuma tana da kirki Yah Abdul naji dadi sosai da Allah ya dawo mana da ita cikin rayuwarmu Hamah nata damuna Gobe ka kaimu gidansu mu qara ganinta kaji Yah Abdul dan....." Hannunsa ya dora akan lips dinta alamar tayi shiru sannan ya muke ya isa jikin wata yar Cupboard inda yake ajiye First Aid box dinsa, wasu magunguna ya dakko tareda ruwa mara sanyi sannan ya dawo kan gadon. Da kansa ya balla mata sannan ya saka mata abaki ta kora da ruwa ita dai se binsa kawai da kallo takeyi, irin wannan kulawar tasa ce take da da hura wutar qaunarsa a zuciyarta "Oya kwanta" ya fada yana bubbuga pillow daya gyara mata, kwanciya tayi tana ci gaba da kallonsa tasan tunda yayi shiru baze bata amsa ba bata hakura ba ta sake cewa "Yah Abdul magana fa nake maka kayimin shiru". "Wai Ni'ima ban isa na hanaki abu ki hanu sau nawa zance