← Book details Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 62

Sashe 62

Rubutacciyar Qaddarah Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tsarin iri daya ne da nata se banbamcin furnitures nasa komai fari ne qala palour daga painting har kayan ciki. Sosai gurin ya mata kyau yanda yake a tsaftace kaman ba gidan namiji ba seta dire basket din tana kallon Agogo tace "I will be gone for some assignments, ten days zamuyi" setayi shiru tana kallon yanda ya zuba mata ido da wani expression da ta kasa ganewa. "Allah ya dawo daku lafiya take care, and Thanks for the Food". Mikewa tayi yana take mata baya har suka fito waje, dan kallon surrounding din yagi yaga babu kowa se kawai ya janyota ya mata wani irin tight Hug har seda ta dan tsorata, a cikin kunnenta ya rada mata "Thanks for the Food Baby Girl" ya saketa a loaci daya, seta juya ta fara tafiya har tana hardewa tsabar yanda jikinta ya amshi saqonsa. Motar da zata kaisu school tuni ta iso dan haka ta shiga ta zauna tana mayar da numfashi. Tanajin yanda idanunsa suke yawo akanta ta tababate be tafi ba yana tsaye har sanda Umm Ashrab ta fito suka gaisa sannan ta shiga motar suka tafi se a sannan ta daga ido ta kalleshi, murmushi ya mata bata san ya akai ba itama se kawai ta mayar masa wai seda suka fita sannan ta fara jin haushin kanta. Yanzu seya zata ma tana son abinda yake mata ne, ita kadai ta ringa cika tana batsewa da bata san dalilinta ba. Koda suka hadu da Nurain baya baya yayi da ita dan ko a tafiyar be yarda ya hada Bus daya da ita ba dan shi kadai yasan me yaji ba iya wadda ya masa a school bane takanas ya bishi har gida ya kafa masa strong warning akan ko kallonta ya qarayi se yayi maganinsa dole ya shafawa kansa lafiya. Cikin kwana tara suka gama abinda ya kaisu a na goma ta dawo cike da kewar data rasa kota waye sedai Motarsa kawai data gani ta yaye kashi 60 cikin abinda yake damunta. Tunda suka tafi bata da wata nutsuwa sosai ance sabo turken wawa tariga ta saba da scent da kuma warmness na jikinsa harzuwa taste of his lips tayi missing. Da Azahar suka iso, shara ta hauyi dan gidan ya danyi qura dan an fara sanyi dukda beyi nisa ba har bayan la'asar sannan ta gama. Seda tayi magriba sannan ta salla wanka tayi sallar isha sannan taci abincin da Zulaiha ta girka musu kafin tabi lafiyar Gado ta kwanta baccin gajia. Cikin dare qarar wayarta ta tada ita, cikeda magagi ta daga wayar ta kara a kunnenta ba tareda tayi magana ba "Ki tashi kiyi sallah" kadai taji kamar an fada kafin a kashe wayar qit. Seta miqe idanunta har rufewa suke yi tsabar bacci tana mamakin saurin da Asuba tayi. Wanka tayo ko baccin ze saketa amma a banza haka ta tada sallah. Har ta idar da sallah tana qunquni tana zaune akan sallayar tana lazumi tajiyo motsin mutum a palour se kawai ta saka kuka dama abu a kusa. Wannan wace irin jaraba ce daga dawowarya, ita yau ko gidan Karuwai take zaune ai tana da Yanci tunda zaman kanta take baza'a ringa fado mata gida Any how ba sannan ita dai ta duba keys dinta dukka sunanan babu wanda ya bata to ta ina ya samu mabudin gidan? Tana cikin share hawaye ya shigo dakin jikinsa sanye da Farar jallabiyya kal kansa ya gyara gashin kansa daya tara kadan kaman wani under 30. Kamshin mayen turarensa ta faraji kafin tajiyo sallamarsa ciki ciki. Gefen gadon ya samu ya zauna yana kallonta a ransa yana mamakin hali irin na Hamdah se kace matar Mamaci kullum kuka "Ka manta ita dince ai" zuciyarsa ta tuna masa. Se yayi tsaki me sauti cikin qufula yace "Malam tashi ki bani abinci ni yunwa nake ji kuma da wuri nake so na fita" seta tsaida kukan tsaf ta miqe tareda riqe qugu tana so yau kam suyita ta qare ne ta gaji, seta fara magana kamar haka "Daka biya nawa kudin sadakina ehe nace a nawa ko kuma Baiwa nidin aka ce an kawo maka da zakazo da gadara asubar Allah karinga bani command kaman wani ubana wai na baka abinci to wallahi ka dade baka ci ba ka kuma tashi kafitar min daga gida kafin na tara maka Jama'a". Kallon yanda take maganar cikin tsallar fitsara da rashin kunya yake har wani girgiza jiki takeyi ita ga mara kunya, seya gyara kwanciyarsa sosai akan gadon yace "Banason yawan magana ki wuce kiyi abinda kawai na sakaki kinji ko" ai kafin ya rufe baki tayi kansa, kafafuwansa ta fara ja tana masifa "Wallahi tashi ka fita na gaji da irin wannan tozarcin da wulaqanci ai ni ba Karuwa bace da zaka ringa shigarmin daki da mutunchina da darajata har kasa Mutane sun fara zargina da aikata sabon Allah kuma wallahi bazan dafa ba tunfa ba ajiyeni kayi ba kuna ban yafe batamin sunan da kayi ba se Allah ya saka......" Be bata dama ba saboda wata irin damqa dayai mata ya birkitota kan gadon gaba daya ya zamana tana qasa yana samanta. Gaba daya ya birkice mata kaman wani tsohon zaki duk yanda taso ta daure amma seta kasa ba shiri ta saka kuka ganin abin nasa na neman wuce gona da iri. Cikin kuka ta fara magana "Kayi hakuri Abdul'ahad karka keta min haddi na roqeka ka tausayamin dan girman Allah ban taba zina ba kuma kaima nasan ba mazinaci bane na tuba ka yi hakuri ka kyaleni". Kaman an dauke ruwa haka ya tsaya, kalmar Mazinaci data ambata ce ta katse masa duk wani hanzari. Seya mirgina gefenta ya dafe kansa da dukka hannayensa biyu saboda yanda yake sara masa yana ambaton suna Allah a ransa. Bargon dake kan gadon taja ta rufe jikinta saboda tuni yayi fatali da Hijab da kuna rigar baccin dake jikinta. Kuka take bana wasa ba tana jin wata irin quna har cikin ranta. Ita kuma tata qaddarar kenan daga aure se kuma fadawa tarkon Namiji wannan shine ta fito daga rana ta fada wuta. Kukan da takeyi da ciwon da kansa da Mararsa suke masa lokaci daya suka hadu suka qara dagula masa lissafi seya kai hannu da niyyar rarrashinta. Baya taja da sauri tana qara wa kukanta qaimi tana cewa "Nidai ka tashi ka fita dan Allah" ta rufe idanunta se hawaye dayake zubowa kawai. Dakyar ya miqe yana layi ya zura jallabiyyarsa, bazata ce ga abinda yayi ba ita dai tajito qarar rufe kofofi dukda idonta a rufe yake bata kasa gane qaruwar duhu a dakin ba da alama an kashe fitila an kuma rufe labulaye saboda garin har lokacin beyi haske ba. The next thing sejin numfashin mutum tayi a kusada kunnenta yana qoqarin hade fuskarta da tashi lokaci daya ta dena kukan jikinta ya dauki rawa jin wani baqon Al'amari da bata tsammata ba. Wani irin kiss me tafiya da sauran hankali yakeyi mata dayai nasarar sakata yin shiru, sauran abubuwan da suka biyo baya bazata iya fasaltasu ba. Abu daya data sani sun shiga wata duniya ita da _ABDUL'AHAD GALADIMA_ me ban al'ajabi. Abubuwan sun ringa faruwa ne kamar a mafarki wai ita da Abdul'ahad? "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un" ta furta da qarfi tareda fashewa da kuka daidai lokacin data qarasa dawowa cikin hayyacinta. "Abdul'ahad mun sabi Allah mun aikata babban laifi Abdul'ahad Zina da Aure mun shiga uku" ta fada tana sake rushe da kuka da qoqarin janye jikinta daga mugun riqon dayayi mata kusan minti goma da suka wuce. Tanajin yanda wani zafi ke fita daga jikinsa yana ratsata amma bata damu ba burinta a yanzu be wuce ya saketa ba, ta ina zata fara roqon yafiyar ubangiji? Wannan yafi kama da ganganci ba kuskure ba me ma ya kaita bada kai har bori ya hau? Seta qara kecewa da Kuka tana jifansa da duk kalmar data zo bakinta. *RUBUTACCIYAR QADDARAH* *By Maryamah* 2020 *PAGE* 4 "Ka cuceni ka yaudareni ka kuma ci Amanar yarda wallahi se Allah ya sakamin wannan itace soyayyar da kake iqirarin kana min dama abinda kake muradi kenan meyasa tun farko baka bayya na manufarka akaina ba". bazan y 4 < > B D J L Z \ h j r t ~ Times New Roman Times New Roman Symb Symbol Arial Arial Calibri Calibri SimSun Cambria Math Cambria Math !%),.:;>?]} $([{ SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO_W4 TECNO LD7 WPS Office 009d6275d04d476f8218a8ea1cbf56da
Chapter 62 · 0% Book details