← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 88

Sashe 86

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muna zaune akan dinning muna cin abinci, ranar Anty Mubeenah ce mai girki kuma ita ta dafa mana abincin da kanta don tuni muka sallami Harira bayan mun danka mata kudi masu tsoka da zata ja jari dasu, duk da cewa har yanzu dai sai a hankali amma she's improving sosai. Ta kalli plates dinmu, Jollop spaghetti da sauce din hanta, soyayyiyar agada, da coleslaw. Ita kuma nata taliyar ce kadai sai tulin vegetables akai, ta kai spoonful of cabbage bakinta ta taune ta hadiye da kyar, ruwa ta tsiyaya ta kai bakinta. “Nafeesah! This is a torture wallahi! Haba!! Wata na nawa bani da abincin daya wuce kabeji? Gaskiya na gaji haka nan wallahi, I want to eat chicken!!" ta fada da karfi tana watsa hannuwana sama kamar wata yarinya, aikuwa nan muka samu abin dariya, ni da yaran muka kwashe da dariya sosai, ta nuna mu da yatsa “dariya ma kuke yi koh? Just wait nauyina ya dawo 65, idan na fara cin nama a gidan nan..." Qaseem yace “Mommy, Anty Nafeesah tace ko kin kai 65 din sau daya zaki dinga cin nama a sati fa!" ta harare shi, “inji wa? Kai dai ku jira in rage nauyin, babu wanda zai hana ni cin nama" ni dariya ma ta hana ni magana. A haka dai muka gama cin abincin cikin raha, na taya Anty Mubeenah muka kwashe kayan muka kai kicin muka wanke, daga nan na koma daki na kwanta wai in dan runtsa kafin La'asar tayi.

Ihun yara na jiyo a falo suna ga Abbu, haba! Na dira daga kan gadon da sauri na fita. A karamin falo muka ci karo dashi, tsaye a tsakiyar su Hafsy cikin suits bakake da farar shirt, na danne dokin in rungume shi da naji naje gefen shi kawai na zauna ina murmushi. Sai da yaran suka gama murnar su ya basu chocolates da tarkace ya tura su dakinsu sannan ya juyo gare ni.

Nade ni yayi cikin jikin shi cikin tattausar rungumar nan tashi. Nima na mayar mishi da wadda tafi tashi taushi, mun jima a haka muna jin dumin jikin juna kafin na zare jikina daga nashi a hankali, na kalleshi ina dan murmushi, “ya hanya?" ya jingina kan shi da jikin kunya, “it was tiresome but Alhamdulillah tunda na iso lafiya" nayi murmushi “you must be kam... Yakamata ka watsa ruwa koh?" na mike da brief case dinshi a hannuna.

Ya mike shima yana sassauta neck tie din wuyan shi, daidai lokacin Anty Mubeenah ta fito daga dakinta. Sanye take da doguwar rigar Shadda wadda tabi jikinta sosai, now that I look at her very well, tana da diri da halittun jiki Masha Allah. Haka kawai naji wani abu ya makale min a wuya ganin yadda Abbu ya saki baki yana kallonta yayin da take kallon shi cike da so da kewa. Ganin kallon nasu ba mai karewa bane ba yasa na danyi gyaran murya sai lokacin suka dauke idanunshi a kan juna, na danne takaicin daya zo mun wuya nayi dan murmushi tare da cewa “dama wanka wai zai je yayi, amma tunda gaki bari in barku tare, inje in dan kwanta" na mikawa Anty brief case din, ban jira sun ce wani abu ba na shige dakina da sauri na maida kofar na rufe.

Numfashi na dinga ajiyewa da sauri kamar wadda tayi tsere, tabdijam! Idan har haka zan dinga ji idan naga Abbu tare da Anty Mubeenah to akwai matsala, lallai yakamata in san abin yi.

Da dare muka hadu a dinning wajen cin abinci, daga jin taste din abincin nasan cewa Anty really put her best effort don kuwa yayi dadi sosai, duk yadda taso taja Abbu da hira a wajen abun ya faskara har naji ta bani tausayi, sai dai wani sashe na zuciyata na raya min cewa kawai burga ce yake yi, amma a dokance yake da ita, hakan shi yake kara tunzura ni.

Bayan mun ci abincin muka hada kan komi muka kai kicin muka dawo falo, Abbu da yaran shi suna hirarrakin su, sai muka ja kujera ni da Anty Mubeenah muna tamu hirar har wajen karfe tara da rabi, na tashi na musu sai da safe na shige dakina.

Wanka nayi na dauro alwala, anan cikin bayin nayi shafa ina karfafawa kaina gwiwa daga munanan tunanika da zuciyata ke kitsa min, babu abinda ya canza, Abbu yana nan a yadda yake kamar yadda Anty Mubeenah take, nayi dashe a zuciyar Abbu wanda babu wata 'ya macen data isa ta dakusar min dashi, sai dai ta nemi wani gurbin tayi nata dashen, da wannan naji karfin gwiwa ya shige ni. Don haka koda na fito nayi tozali da Abbu akan gado, murmushi nayi naje gefen shi na zauna. Lafiya lau muka yi sallama dashi, na raka shi har bakin kofa ya tafi bayan ya manna min pecks a kumatu da goshina. Na maida kofar na rufe, kan gado naje na kwanta na janyo wayata nayi en dube-dube da chatting har dare yayi kafin na kashe wayar nayi addu'ar kwanciya barci na shafa. Filo na janyo na rungume a kirjina na rufe idanuna, can kasar zuciyata Istigfar na dinga janyowa da hailala saboda korar shaidanin dake saka min abubuwa a cikin raina...

~Lol! Su Malama Hajiya Mubeenah an dawo kan hanya fa! Wa yaji dadin canzawar ta kuwa? Ni dai naji
~N please ina baran addu'o'inku...
#TeamAbnaf
#OneLove

*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA...!*

*©Jeedderh Lawals*

*®Fikrah Writers Association* 🖊🖊

*60 FiNaLe*

Alhamdulillah! Rayuwa mai cike da inganci da zama lafiya muke shimfidawa mu da mijinmu. Mun hade kawunan mu waje guda domin samun kwanciyar hankalin mijinmu. Yes, akwai kishi, sai dai kishin zamani muke shimfidawa ba wai na dabbobi ba, kowa tana iyaka kokarinta wajen ganin ta faranta ran mijinta domin samun ragamar zuciyar shi don haka a takaice dai Abbu ya zama sha lelen mu.

Lokacin Hajji yazo, Abbu ya biya mana kujera mu duka banda Hafsy, muka je muka sauke farali. Bayan mun dawo naje Kaduna nayi kwana daya na dawo muka ci gaba da gudanar da rayuwar mu a nutse.

*****

Kallon shi nake yi idanuna na shekin bacin rai da tashin hankali, “ban gane ba? Kamar ya ba zan yi aiki ba, akan me??” tunda muka dawo daga aikin hajji na dame shi da maganar son fara aikina amma yayi biris dani, sai ranar ne ya bani amsa da cewa ai ba zai barni wae inyi aiki ba, duk wahalar dana sha!.

A nutse ya kalleni cikin sanyin murya mai cike da lallashi yace “to menene abin tada jijiyar wuya kuma? Kin dai san cewa ba tun yau ba nasha fada miki cewa bani son mata na su yi aiki, nafi so su zauna a gida su kula min da gidana da iyalina. Beside Nafeesah baki nemi komi kin rasa ba a gidannan, aikin me kuma zaki je kiyi saboda Allah?"

Na cure baki waje guda ina yamutsa fuska, “to ni nace ne dama saboda kudi zan yi aiki ne? Kawai sabida ina so inyi aikin ne, m bored to death! Baka barina ina fita ina ganin mutane sai abu mai muhimmancin gaske ya taso, baka barina inje gidanmu in musu kwanaki sai dai wuni.... Ni wallahi idan ba so ake yi mutum kadaici ya kashe shi ba a bar shi yayi aiki!"

Kallona yake yi baki a dage cike da mamaki, tun da muka yi aure iyakata da Abbu Nafeesah yi kaza, ince toh., ko kuma Nafeesah ba zaki yi kaza ba ince toh. Amma yau yaga gabadaya na wani canza ne, abinda bai taka kara ya karya ba, maganar aiki ba tun yau ba yayi making it very clear ba zai bar matar shi tayi aiki ba amma gashi ina tonon fada da maganar.

Na kawar da kaina daga kallon da yake min na mamaki, “a’ah! Yo mutum sai yaki fadin gaskiya haka kawai! Idab ma bazan yi aikin ba a dinga barina ina fita mana, amma kullum ni a garkame a gida kamar wata furzuna? Da yake ita er gaban goshi ce naga babu ranar banza da ba zata fita ba amma ko a jikin ka sai ni, me nayi maka ne saboda Allah??" kwalla ta ciko idanuna, da sauri na juya na shige dakina. Kan gado na kwanta ina ajiyar numfashi idanuna a lumshe. Kwana biyun nan zuciyata a wuyana take, kome aka yi da wanda ya kai da wanda bai kai bama jin haushin shi nake yi. Na dan ja siririn tsaki, meye ma na wani sako zancen Anty Mubeenah? Duk da cewa dai abin yana ci mun tuwo ne a kwarya, kun ganta nan kullum tana waje yawo, yawace-yawacen nan nata har lokacin bai ragu ba, karewa ma watarana sai ta fita sannan take fada mishi duk da cewa dai an samu saukin kin fada mishi da bata yi. To ni kuma Fisabilillah kullum ina garkame a gida, idan yara suka tafi school Anty ma ta fita ni kadai ake bari inyi ta gantali a cikin gida, abin ya dame ni sosai.

Ina jin lokacin da aka taba kofa alamun an shigo cikin dakin, bayan juya baya da nayi sai na lumshe idanu na. Ya zauna a gefen gadon da nake kwance, yace “wai Nafeesah me ke faruwa ne? U never go against my words n you never raise ur voice on me, naga maganar aikin nan fa tun ba yau ba na fada miki cewa ba zan iya barin mata ta tayi aiki ba. Mubeenah tana da degree akan computer science ni na hana ta aiki but in return sai na bude mata saloon din can, ba gashi yanzu komi ya zama even ba? I'll do the same to u, Dan Allah kar ki maida maganar nan ta zama babba ranmu ya baci Nafeesah!"
Chapter 86 · 0% Book details