← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 88

Sashe 58

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bamu ankara da lokaci ya ja ba sai da muka ga Basheer ya fito zai tafi sannan Abbu ya duba agogo yaga karfe goma ta wuce, Abbu ya kama baki cike da tu'ajjibi yace “haka lokaci yake gudu dama?" na sadda kaina kasa ina magana a hankali yadda ba zai ji ba “kaine dai baka kula da lokaci yana tafiya ba saboda love ya rufe maka ido" ya mikawa Basheer hannu suka yi musabiha na mishi sai da safe nima ya karasa wajen abin hawan shi ya tafi, Abbu ya bude motar ya shiga ya zauna, ya kalleni yana kokarin yiwa motar key, “naji abinda kika fada sarai, zaki zo hannu ne ai zaki yi bayani by then" na ja da baya ina er dariya, na maida mishi murfin motar na rufe, yace “any thing for me?" na girgiza mishi kai, “babu, sai da safe Abbu na!" na juya da sauri na fara tafiya ba tare dana jira abinda zai ce ba, ina jin shi yana en maganganu har na mishi nisa kafin naji alamun yaja motar, na saki dariya a hankali. Ina shiga daki suka min caaa da magana, ni dai er dariya kawai na dinga yi da kyar na samu na kashe musu baki, Sadiya ta miko min leda mai dauke da gasasshen kaji da yoghurt, na zauna ina ci muna hira dasu har wajen karfe goma sha biyu Ni'imah tayi barci, sannan ne muma muka kwanta don dama duk saboda ita ne muke yin hirar don kar muyi barci mu barta ita kadai kadaici ya dameta, muka gyara daya gadon muka kwanta mu ma. Washegari wajen karfe goma Basheer ya kawo mana abin kari da kayan da Ni'ima zata canza, bayan su Anty Rahina sun zo mun gaida su nabi Sadiya gidanta muka je muka yi wanka muka canza kaya, sai kayan Sadiya na saka saboda ban tafi da wanda zan canza ba. Muna komawa muka tarar an sallame su, nan muka hada kaya muka wuce gidan Ni'imah. Muka gyara mata gida da komi muka mata girki, su Anty Ameenah ana kiran sallahr la'asar suka wuce, ni dai daga nan na musu sallama don a ranar zan koma makaranta. Sai bayan tafiyar su ne sannan na kira Mommy na fada mata abinda ya faru, sai da nasha fadan wai ban gaya mata da wuri ba sannan tace in hada ta a waya ita da Ni'imah, no dai na bata hakuri kafin in ba Ni'imah wayar Mommy ta mata jaje tare da kara mata da nasihu daga nan ta maido min wayar, na amsa, anan take fada min cewa wakilan Abbu zasu je gida Malumfashi tambayar aurena, nayi shiru ina gyada kai kawai, ta mim addu'ar Allah ya sanya alkhairi muka yi sallama da ita. Nima ba a jima ba na musu sallama na koma makaranta. Bayan kwana biyu aka sanya ranar auren mu ni da Abbu watanni biyu masu zuwa yayin da biki da tarewa kuma za a bari sai na gama exams dina. Wannan kenan!!
~Hii! This is just to tell u that u people r really amazing, I want u to know that I really love and appreciate ur love and affection towards me and my write up! Thank u very much and stay blessed!! 🧡🧡🧡
#TeamAbbu
#AnaTare🤝

*♡Jeedderh♡*
[1/1, 18:03] Hauwa-Jedderh💕: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*44*

Kwanci tashi asarar mai rai, biki yana ta kara matsowa yayin da muke ta shirye-shiryen rounding off din semester dinmu. Tuni Ni'imah ta warware har ta fara shigowa school abinta, cikin Sadiya yana ta kara fitowa ni kuwa gandoki har na fara tanadar kayan jarirai, lol.

☆☆☆☆☆

Cikin mamaki na daga wayata dake ringing bayan na duba sunan wanda yayi kiran, “Yau ko dai batan lamba waya kayi Harith?" tunda ya samu aiki a Ibadan ya tarkata ya tafi zumuncin dake tsakaninmu yayi kasa, shi aiki ni kuma karatu don haka we were not in contact recently, yace “haba Nafeesah, har ke kina da bakin magana? Sau tari zan tura miki sako ta whatsapp amma bana ganin reply dinki, anya idan da amana ruwa ya dafa kifi??" nayi dariya nace “kasan rayuwar dalibai sai a slow wallahi, shi yasa. Ka yini lafiya?" yace “yeah, Alhamdulillahi..." nan muka gaisa dashi da tambayar juna kwana biyu, yace “Sis take fada min ranar nan wai ai an saka miki ranar aure, shine nace bari in kira in tambaya inji laifin me nayi da ban samu labari ba?" nayi murmushi nace “to kuma kawai daga sa min aure sai in hau shela? Kaima ai naji ance ka kai kudin aure gidan su Ikram" yace “yeah... Amma ya aka yi kika sani? Ko abokaina basu san da labarin ba" nace “nima a gari naji, amma daga majiya mai tushe, Ikram din ce da kanta take fada min" yace “iye lallai naga nuna wariyar jinsi, so u guys have been in contact with each other amma shine kike fada min wai wani rayuwar dan makaranta and stuffs ko?" nayi dariya nace “ai kasan zumuncin mata ko ta yaya dai in a week ba su rasa yin waya shi yasa... So what's up?" yace “mun shigo workshop ne cikin Kano, shine nace bari in tambaye ki idan ziyara is allowed, zan leko mu gaisa" nace “why not? You are welcome!" yace “to ba laifi, goben idan zan shigo I'll inform you" daga nan muka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Firdausi ta dago kanta daga typing din da take yi a cikin laptop dinta ta kalleni, tace “ni yanzu meye makomar ki idan an miki aure? Zaki ci gaba da zama cikin hostel ne ko kuma zaki zauna tare da kishiyar ki ne tunda har yanxu ba a gama gyara inda zaki zauna ba?" na zauna a gefen gadona ina sighing, “ban sani ba nima wallahi, but kila, may be in ci gaba da zaman hostel" tace anya? I doubt idan mijin nan naki zai yarda, na harareta “me kuke nufi wai? Abinda Sadiya da Ramlah suka ce kenan dama" tayi dariya, “to ai yadda yake nunawa ne, he's barely holding it in, a dokance yake kuma a kagauce da auren nan, azo kuma ace an daura amma ya barki ki zauna a hostel? Ni dai a ganina da kyar ya bari" na dauki dan karamin filo na jefeta dashi, “ke fa m dinki karama ce wallahi, sam baki da kunya" ta fashe da dariya ni kuma na maida bayana kan gado na kwantar ina kara juya maganganunta a cikin raina, gaskiya a son samuna koda ace gyaran gidan da za a ajiye ni bai kammala ba to Abbu ya barni in ci gaba da zama a cikin hostel abina har sai an gama don ni fa har ga Allah ban shirya fuskantar Anty Mubeenah a matsayin kishiya ba balle har ta kaini ga zama a gida daya da ita a matsayin kishiyoyin juna, woah! Ko ya zaman zai kasance?? Na gyara juyawa a kan gadon tare da janyo face mask na rufe idanuna, a hankali barci ya dauke ni.

Washegari lecture din Abbu gare mu, da wuri na tashi na shirya cikin jallabiya brown mai kwalliyar light ash a jikinta, ban yi wata kwalliya ta sosai ba na yi rolling gyale ash mai dan fadi, na zura takalmin vincci flat na fita da dan saurina, takwas saura ina cikin hall din, nayi ajiyar numfashi lokacin da nake zama a kan seat, Abbu baya tolerating late coming ko da wasa, minti biyar ya kara akan karfe takwas to ka hakura da lecture dinshi na ranar kawai, na tuna lokacin dana taba yin nauyin barci ban tashi da wuri ba, na isa wajen six minutes past eight na tarar da kofa a rufe, kuma fa Abbun yana kallona a tsaye a kofar class din amma yayi biris dani tare da sauran dalibai abokan latti na, haka muka gaji da jira muka kama gaban mu.... Na ciza bakina cike da takaici, har yau idan na tuno abinda ya faru sai naji kamar inyi me, kuma fa sabida shi nayi makarar, shi ya kira ni a daren ranar ya tsare ni da hira har dare ya tsala., ai kuwa dai da kyar ya samu ya shawo kaina. Na saki dan murmushi a hankali dana tuno irin bidirin da muka sha a lokacin. Ajin yayi tsit lokacin da Abbu ya turo kanshi cikin ajin, yayi shigar wani danyen vowel ruwan hanta, bai saka hula ba sai dai ya taje sumar kanshi da yake shi ba ma'abocin saka hula bane. As always, yayi kyau kamar ka lashe shi. Ya fara searching din hall din da idanun shi a hankali har ya lalubo ni, ya sakar min murmushi very soft and lovely, ban bata lokaci ba wajen mayar mishi da martani, yayi gyaran murya amma fa jefi-jefi idanunshi kan kalloni kamar yadda koda wasa nawa basu bar shi ba.
Chapter 58 · 0% Book details