← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 88

Sashe 65

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai bayan da nayi sallar asubahi sannan na samu na kara bitar karatu. Karfe tara muka fara exam dinmu muka fito kafin sha biyu, daga nan barci nayi don jiya kam ban samu nayi barcin kirki ba. Sai da su Ni'ima suka zo sannan na tashi daga barci lokacin wajen karfe biyu ne, sai da nayi sallah sannan muka shiga shirye-shiryen zuwa wajen Reception din. Suka wanke min kai suka kafar dashi kafin suka gyara min shi sai sheki yake yi da tashin kamshi, nayi wanka na fito nan ma aka shiga yin kwalliya kuma. Da aka kira la'asar muka yi saurara muka yi sallah sannan muka ci gaba, na zura doguwar rigar shaddar da Abbu ya kawo min, Ramlah ta daura min dankwalin rigar yayi kamar gwaggwaro, na saka dankunne, sarka da awarwaro masu ratsin brown a ciki, muna cikin yin shirin wanda aka turo ya dauke mu ya yi waya yace ya iso, da yake suma a shirye suke sai duk muka rankaya muka tafi. Wata er ubansun Range Rover ce baka tana ta sheki tazo daukar mu, aka bude mana muka shiga maza biyu ne a gaban motar don haka muka shiga baya muka tafi, daya daga cikinsu ya juyo muka gaisa har da yin shakiyancin su na abokanan ango, su Firdausi ne masu tare min ni kam kaina yana kasa, duk inda muka wuce sai an bimu da kallo wanda probably nasan cewa motar suke kallo don kuwa haduwarta ya wuce misali.
Tafiya muke yi a hankali har Hotoro, aka yi horn a kofar wani gida aka bude muka tura hancin motar muka shiga, anyi decorating din wajen da kayan ado da ake yi wajen bukukuwa ga kujeru an shirya, wajen cike yake da mutane ana ta hada-hada, aka yi parking sannan muka fita. Wasu mata gungu guda suka zo suka ja mu har wajen da na tabbatar saboda ango da Amarya aka yi shi saboda wajen ya fita daban, wasu royal kujeru guda biyu a kasan canopy an sa tuntu akai a kasa kuma an shimfida wani babban carpet me fadi da laushi. Mai gayya mai aiki Abbu yana zaune a kujera daya, munyi anko da kayan jikinshi shadda light brown mai surfanin zare dark brown, leather brown cover shoes da hular zanna bukar itama brown, kaina a kasa yake ban yi gigin daga ido na dubi Abbu ko tarin mutanen da hankulan su ya dawo gare mu har suka taimaka min na zauna a kujerar kusa da Abbu, in a wink sun bace daga wajen, photographer yazo ya fara haskemu da flashes ya dauki kamar guda goma kafin ya tafi. Abbu ya dan matso saitin kunnena ya rada min “kin yi kyau sosai amaryata" na danyi murmushi ina wasa da yatsun hannuna. Mutanen wajen basu da yawa duk da haka na hango wasu daga cikin dangina na Malumfashi mazan, Aminu, Haruna da Samir duk diyan kanne da Yayin Daddy ne, a matan wajen kuma na hangi Anty Amina da Anty Rahina, Sadiya, Saratu, Da Halima su kuma cousin din su Sadiya dinne, sauran matan kuwa da zasu kai guda goma ban san su ba na dai yi zaton kila matan abokan Abbu dinne. Ba wani bata lokaci aka fara gabatar da walimar, wani daga cikinsu ya bude taro da addu'ah, ya mana fatan alkhairi ana yi ana raha ana ta shan dariya saboda jokes din da mutumin ya dinga cracking, daga nan kuma aka yi en ciye-ciyen snacks da aka raba da kuma drinks, daya bayan daya suka dinga zuwa kowa da matar shi, mu gaisa dasu su mana fatan alkhairi su bamu kyauta, wani a cikin wrapping sheet wani kuma a envelope har su Anty Aminah dasu Ni'imah, daga nan kuma aka shiga daukar hotuna kamar me?! A haka har duhu ya fara shigowa, sannan ne fa aka kara rufe taro da addu'ah muka fara sallama dasu suna shiga motocin su suna tafiya, kafin dai a kira magriba an barmu daga mu sai mu, su Anty Ameenah ma suka mana sallama suka tafi, su Ni'imah sun bi mazajen su sun tafi sai Ramlah tabi bayan su Sadiya. Muka shiga falon matar gidan mai suna Farha ta mana jagora ni da Firdausi har cikin bedroom dinta muka yi sallah, matar tana da fara'ah ga kirki, muna gama sallah muka fara hira wadda yawancin ta akan rayuwar aure ne, challenges din dake cikin shi da shawarce-shawarce akan zamantakewa da kuma wasu shawarwarin da suka sa ni sunke kaina cikin gyale na, tace “kunya kike ji? Wallahi idan kika ce zaki saka kunya cikin rayuwar aurenki to zaki samu cikas kuwa more especially ke mai kishiya, ai wallahi dagewa zaki yi ki cire kunyar nan ki kama mijinki tsam kafin kishiya ko wata a waje ta miki kwacen shi" na gyada kaina cikin yarda da maganganunta. Su Abbu basu shigo gidan ba sai bayan sallar Isha, Farha tayi-tayi damu akan mu tsaya mu ci abinci muka ce a'ah, ta bude wani karamin Kit, tana bude shi wani kamshi mai dadi ya hade dakin, ta dauko kwalaben humra guda biyu ta bani ita kuma Firdausi ta bata turare, tace min “sai dai humra din nan ki bari sai kin tare kafin ki fara amfani da ita Zai fi" muka mata sallama muka fita waje inda Abbu yake jiranmu, muka sake sallama da Farha da maigidanta muka shiga mota muka tafi. Babu wanda yayi magana a cikin motar har muka isa makaranta, Abbu yana yin parking Firdausi ta bude motar ta fita bayan ta wa Abbu sai da safe shi kuma ya mata Allah huta gajiya. Tana fita kamar wanda yake jira ya kamo hannuna, bai damu da yadda nayi gaggawar kwace hannuna ba ya sake janyo hannun nawa yana caressing da thumb dinshi, “kunshin nan yayi kyawu sosai, idan ya goge ki sake yin wani kinji? Shima idan ya goge ki sake wani, I'd like to be seeing it kinji??" na gyada mishi kai a hankali, yayi murmushi “good girl, amma ni sai wani noke-noke kike yi da wani kauda fuska, kin daina min magana, laifin me na miki iye?" ban yi magana ba sai kaina dana girgiza yace “ikon Allah! Aikuwa ba zamu yi haka dake ba, za kina bude baki ne kina min magana idan ba haka ba kuma raina zai baci fa, and u wouldn't like me idan hakan ya faru, ok?" na sake gyada kai, sai kuma nayi sauri nace “toh" yace “na fara nema mana visa fa, wani gari kike so kije for our honeymoon?" na dan zare ido, “honeymoon?" yace “ehh mana, da kin gama exams kin koma za a dawo min dake daga nan kuma zamu tafi honeymoon dinmu" nace “amma da aka ce sai session dinnan ya kare?" ya wani zaro ido kamar wadda ta fadi wani sabo, “ses... me? Ni dai nasan da bakina baki ji na fadi haka ba koh?" nace “ai nayi zaton haka ne" tun kafin in gama yake girgiza kai, “no! Ba haka bane. Gidan da zamu zauna is ready, komi ya riga ya kammala, kun gama jarabawar ku to me zan jira kuma? kin dai san ba zan barki kici gaba da zaman hostel ba kuma yanzun ma don we've already agreed on it ne shi yasa kika ga nayi shiru amma maganar gaskiya ban jin dadin zaman ki anan" na wani yi rau-rau da idanu, ya dage gira, “Allah baby kina jin dadin ki, kuka zaki yi kuma, me na miki?" ya kai hannunshi na dama ya tallabo kuncina dashi yana caressing din kuncina, hannunshi was very warm, na lumshe idanu na a hankali, na jiyo yatsar shi a saman idanu na yana shafawa, “zan ga yadda zamu kare da rigimar ki baby, dama ana haka ne? Daga magana sai ki kama kuka irin daddyn ki ya shagwaba ki koh?" na turo baki tare da janye fuskata daga hannunshi wadanda suka fara sanya min sayingsanyin jiki, murmushi kawai yayi. “Wadannan kyautukan da kika samu ban san ya zanyi dasu ba, do u have any idea ko wajen da zaki ajiye su?" nace “ka ajiye min su a wajenka" yace “to shikenan, zan kaisu gidanmu in ajiye, idan kin zo sai mu bude tare koh?" na rufe fuskata shi kuma yayi dariya, “nasan akwai kudi a ciki su kuma zan saka su cikin account ko ya kika ce?" nace hakan ma yayi, nan ma yace ok. Muka dan yi shiru na dan lokaci kafin ya duba hadaddiyar agogon fata dake daure a lallausan hannunshi, “to nine, yakamata kije ki kwanta yanzu koh?" nace “to, sai da safe" dama duk a wani takure nake ji na, na kama murfin motar zan fita ya sake janyo hannuna da bai jima da saki ba ya juyo dani, “not so soon baby, babu ko sallama?" na danyi frowning in confusion, wace sallama yake so muyi bayan wadda na mishi yanzu? Ban kai ga furta abinda nayi niyya ba naji ya hade goshina da nashi waje guda, irin sallamar jiya ya min sai dai ta yau tafi zurfi da demanding, ya sake ni a hankali idanunshi a lumshe, har lokacin goshin mu a hade yake, numfashi yake ajiyewa a hankali can kuma sai ya sake ni gabadaya, “Goodnight Amour" ya fada cikin whisper, cikin salubewar jiki na fita daga cikin motar. Ina shiga daki text dinshi ya shigo wayata, “make sure to eat something kafin ki kwanta, sweet dreams" na girgiza kai kawai na ajiye wayar akan gado na fara zare kayan jikina, ruwa na watsa na dawo nayi shirin kwanciya barci. Ba wata yunwa nake ji ba don haka na kwanta kawai, Abbu da Al'amuran shi masu ban mamaki suke min yawo a kwalwa, abubuwan da yake min were very new to my innocent life, ban san ya zan kamanta abinda nake ji a cikin raina ba amma ina jin kamar abin is wrong, anya ban yi kuskure ba kuwa?? Nayi juyi akan gado tare da tura kaina cikin pillow.
~Hii there dearies, so me zaku ce game da chapter din yau?
#TeamAbNaf! Hahh! Wata Fan ta kirkiro da sunan nan, ya burge ni kam sosai, what did you think?
#AnaTare

*♡Jeedderh♡.

*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋

*48*
Chapter 65 · 0% Book details