← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 88

Sashe 44

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read

"Assalamu Alaikum" sansanyar muryar shi ta doki kunnena, duk wani karfin gwiwa dana tanada da kaudin da nake na cewa Abbu ya daina firgita ni ashe aikin banza nake yi, a take muryar shi tayi raga-raga da naman jikina, yayi gyaran murya tare da ambatar sunana, na amsa a nutse kuma a hankali cikin muryar rada, shiru ya biyo bayan hakan na lokaci mai tsayi, baka jin komi sai karan iska dake wucewa ta cikin wayar. Yace "Nafeesah! Ya muka kare da maganar mu ne?" nayi shiru ina zare idanu, da me na shirya zan ce ne? Gabadaya komi ya fita daga cikin kwakwalwata, yace "umh?! Ina sauraron ki" na bude baki zan yi magana sai dai sautin dake fita kawai shine "ermm.... ermmm" na kasa yin takamaimiyar magana. Abbu ya tausasa murya, "look Nafeesah. I don't have much time yanzu, mintuna kadan suka rage min in tashi zuwa Vancouver zan yi wani four months course acan so please do tell me, me kike tunani? Ina son ayi ayi auren mu dana dawo Nafeesah, da so samu ne a gare ni da tafiyar nan dake zan yi ta a matsayin mata ta Nafeesah don ba wani tsayawa zan yi bata lokaci wajen soyayya kamar yaro ba, kin san na tsufa da hakan koh?" wata hudu a Vancouver? A perfect timing!! Yace ina jin ki Nafeesah, an fara kiran fasinjoji, me kike tunani? Zaki iya aure na??" na lumshe ido a hankali zuciyata na suya a kirjina kamar an tsoma ta a ruwan zafi, "I Am Sorry Abbu...... I can't!" shiru ba magana daga bangaren shi yayin da kowace wucewar dakika zuciyata take nunka gudunta har na fara tunanin idan na kara minti daya a wannan lokacin zata iya bugawa gabadaya. Bayan kaman wucewar lokutan dana kasa lissafawa, yayi gyaran murya, muryar shi lullube da wani irin embarrassment da daci yace "zan kira ki idan muka sauka Nafeesah" a hankali hannuna da wayar suka sauka akan gadona kamar wadda aka zare mata numfashi. Nayi imanin da ace Duniya da lokaci suna tsayawa da sai ince nawa sun tsaya, komi nawa ya tsaya cak. Bana fahimtar komi sai daci da sanyin jiki dana ji suna fita daga bakin Abbu, ban yiwa kaina adalci ba, sai dai ina bukatar sanyin rai dana zuciya. Ina bukatar farin cikin iyayena, nasan cewa definitely Mommy zata yi farin ciki da hakan Daddy ne dai ban sani ba, ni kuma I only need those four months, In shaa Allah kafin lokacin ya cika, "I'll over come it!" na fada a fili cikin karfafawa kaina gwiwa. Karan bude kofa yasa nayi firgigit na kalli kofar, Mommy ta shigo tana kare min kallo, tace "kin yi bakuwa Ummiey" na kalleta da sauri, "bakuwa, wacece?" ta dan maida kanta wajen kofa tare da furta "shigo" Ikram ta shigo dakin bakinta dauke da sallama, da sauri na tashi tsaye ina amsawa, iso na mata zuwa gefen gadona ta zauna, Mommy ta juya ta fita ta barmu muna gaisawa, ruwa da lemu na dauko mata a fridge na dawo, muka zauna shiru a dakin saboda ba wani sabo muka yi da ita ba dama, can na katse awkward silence din nace "so???" ta sadda kanta kasa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa magana, na dan yi murmushi nace "Kina son tambayar Abinda ke tsakani na da Harith koh?" ta kalleni cikin mamaki kafin ta gyada kai, nace "magana ta gaskiya Ikram babu abinda yake tsakani na dashi, duk abinda kika ga mun yi was just a plan, yana so ne yayi provoking dinki" ta nuna kanta da yatsa, "ni kuma? Why??" na zayyane mata labarin duk abinda kenan, Ikram tayi shiru kanta a kasa har na gama. Tace "yaki ya fahimce ni ne kawai, shekaru biyu kadai suka rage min a karatuna, menene a ciki idan ya hakura zuwa shekarun biyu?" nace "Ikram kina son Harith shima yana son ki saboda haka ni ban ga abin tada jijiyar wuya a wannan maganar ba. Shawarar da zan baki shine to just go for it, karatu baya hana aure kamar yadda aure baya hana karatu idan har kika maida hankalinki akan hakan" tayi shiru kamar mai tunani kafin ta kamo hannuwana ta rike, "nagode sosai Nafeesah. In shaa Allahu zan zauna in duba hakan, nagode" na danyi rubbing hannunta dake kan nawa ina murmushi. Mun dan kara hira da ita kafin ta min sallama ta tashi, na raka ta har bakin titi ta samu abun hawa ta tafi ni kuma na koma gida. Da dare Daddy yake gaya min an sai min DE form a BUK, na turo baki nace "Daddy ni fa ABU nace maka ina so" yace "sun riga sun rufe saida basically ne shi yasa nasa aka nema miki BUK din" nayi shiru ina tunani, wannan shine kaka-kara-kaka din fa, ina gudun Abbu shi kuma yana kara bibiyata, nace "ni dai kawai na hakura sai next year" daga Mommy har Daddyn kallona suka yi, Mommy tace "sai mu saka ki a gaba muna kallo har shekara koh?" Daddy yace "Duk maganar zama bata ma taso ba, tunda an samu admission din ki daure ki tafi can din kawai" nace "amma a cikin hostel zan zauna koh?" Mommy tace "to in ba can ba ina? Dole can zaki zauna" Daddy ya daga baki kamar zai yi magana sai kuma yayi shiru kawai. Daga haka aka fara processing din nemar min admission a BUK. A gefe daya kuma naci gaba da karatu na.

Sati daya, biyu, uku suka shude babu alamun kiran Abbu a cikin wayata, ban kuma sake jin magana game dashi ba. Tunanika iri-iri game da hakan babu kalar Wanda ban yi ba da wasi-wasi, kila ya hakura ne, kila maganar da nayi ta bata mishi rai, kila dama ba sona yake yi ba.

*♡Jeedderh♡*

[12/23/2017, 13:52] Beluvd Zee: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*36*
Chapter 44 · 0% Book details