← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 88

Sashe 3

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

           Tun da muka gama hada breakfast na koma na kwanta barci, ban tashi ba sai wajen karfe goma na safe. Brush nayi na fita falo na karya, daddy ya fita wajen aiki. Dama dai Mommy full house wife ce, babu aikin da take yi. Shi yasa nace muku rayuwar auren iyayena tana matukar burge ni, Mommy tayi karatu har matakin masters akan Pharmacy amma daddy ya hanata aiki, duk wasu bukatu nata kuma ya dauke su ba kamar sauran mazajen yanzu ba da idan matarsu tayi karatu taki yin aiki sai labari yazo ya sha banban saboda ba zasu raba hidimomin gida tare ba. Wanka na shiga nayi, na fito na shirya cikin doguwar riga ta wani material grey mai dan nauyi, dinkin ya kamani tsam ya bi jikina, sai daga kasa ne ya baje sosai. Saboda yanayin kirar jikina dama ba wai kiba gare ni ba, er siririya ce ni amma fa Akwai kira, daga sama har kasa kam sai dai in gode Allah. Kalar fatar jikina baki ne, duk da ba wai can ba, zaku iya cewa chocolate color dai. Gyale na dauka na dora shi akan kafada ta na fita. Dakin mommy nayi knocking na shiga, tana zaune a gefen gado da dan littafin hisnul Muslim a hannunta. Kallona tayi na zauna a gefenta, a dan shagwabe nace "mommy dan Allah inje gidan Anty Uwani?" anty Uwani kanwar mommy ce, yaranta hudu duka maza, mun saba dasu sosai saboda zumuncin iyayenmu. Lokaci zuwa Lokaci na kan je can har in musu weekend. Mommy tace "kinga baki tambayi daddy dinki ba Ummie, babu ruwana pa!" kara shagwabe fuska nayi nayi nace "mommy da wuri pa zan dawo Allah" Kallona tayi na lokaci kafin ta gyada kai, "shikenan,  but kar ki kai yamma fa!" cikin murna na gyada mata kai. Cike da doki na tashi, har na fita na sake komawa, purse dinta na bude na zari dubu biyar na fita da sauri ina dariya, kallo kawai ta bini dashi. A Unguwar Rimi suke zaune, sai dana tsaya na sai dangin fruits a bakin hanya sannan na karasa gidan. A can na wuni sur, sai gab da magrib sannan ta sa direba da danta na biyu AbdulJalal wanda yake kusan sa'ana ne suka rako ni gida. Daddy har ya dawo, Allah ya taimake ni ban sha fada ba saboda Daddy baya son yawo ko kadan. Bayan sallar isha'i ina zaune ina kallon film din Kaabil daga cikin laptop dina Ramla ta kira ni, murmushi nayi da naga sunanta a jikin wayata, wato har ta gama fushin kenan?? Da er dariya ta na daga kiran, "Lauratu ya ne?" haka nake kiranta idan naso tsokana. Ina jin dan siririn tsakin data saki, "ke pa u r a prof a ruining mood din mutum wallahi, meye wani Laure kamar wata Goggo a kauyen kayau?" dariya na sheke da ita cikin tura haushi, hakan ya kara tunzura ta kuwa. Sai da na gama tsokanarta sannan na tsaya ina sauraronta, hakuri ta bani game da abinda ya faru ranar, nima hakurin na bata tunda dukanmu we are at fault. Daga nan hira muka hau yi da ita, mun share fiye da awa daya muna hira har sai dana gaji don ni dama can ba gwanar hira bace musamman ma hirar waya, sallama muka yi kowa ya ajiye wayarsa.

      Da dare muna falon daddy mu duka muna en hirarraki, aka kira daddy a waya. En maganganu suka yi kafin ya ajiye wayar yana kallona, "Uwata kinji an karbi letter dinki pa!" ban san dalili ba, gabana ya fadi ras! Rasa abin cewa nayi kawai na tsaya ina kallonshi, yaci gaba, "ranar Sunday zaki tafi mun gama magana da Ibrahim din. Sai ki fara shiri koh?" jikina naji yayi sanyi sosai, kafin kace me! Hawaye sun fara min yawo a kumatuna, cike da damuwa daddy yake kallona, "Uwata lafiya?" kai na gyada mishi a hankali, "I just started missing u ne daddy!" Dariya ya saki yayin da mommy tayi murmushi, hannu na ya rike a tausashe, "ohh my loving princess.... We gonna miss u!" group hug muka hada kamar zamu yi kuka.

Shirye-shiryen zuwa Kano na fara yi, hada tarkace, sallama da dangi da en abubuwa. Komi cikin sanyin jiki nake yin sa, wannan shine karo na farko da zanyi tafiya ta fiye da watanni uku. Daddy dinmu dan asalin garin Malumfashi ne ta Katsina, danginshi duk a Katsina suke zaune don haka mu kan je can idan mun samu hutu in musu kwanaki zuwa sati. Amma Ina jin wannan tafiyar ta banbanta, zuwa zanyi fa in zauna da mutanen da ban sani ba na tsayin watanni hudu zuwa biyar, a garin da ban sani ba duk da cewa mun yi zaman Kano na shekaru biyu, amma that was then, I think tun ina primary 5 ne??? Haka dai naci gaba da Shirye-shiryena har zuwa ranar Sunday. Sai wajen karfe biyar na yamma muka bar Kaduna, daddy ne ke jan motar, mommy na gefen shi ni kuma ina gidan baya. Tafiyar tayi min wani irin sauri, sai naga kamar muna tafiya ne akan iska ba kan kwalta ba. Cikin dan lokaci kankani mun isa Kano, unguwar Tal'udu muka wuce tunda anan gidan yake. Naji daddy yana ba Mommy labari game da abokin nashi, yace lecturing yake yi amma ba a staff quarters yake zaune ba, yace dan asalin garin Kano ne kuma yanzu haka yana neman kujerar dan Majalisa ne. Yaran shi uku da matar shi daya..., ni dai tunda naji yace yana harkokin siyasa na maida hankalina kan wayata, dan siyasa? Allah ya gani basu cika burge ni ba, ban son siyasa.
Kugi na karshe da motar tayi a cikin garejin gidan ne, tun daga cikin mota nake karewa gidan kallo. Ba wai yanke hukunci kai tsaye ba, yanayin gidan tafiy kafin ace mallakin just a lecturer (sorry lecturers, m not underestimating ur payment or something). Gida ne hawa daya, parking lots din gidan cike yake da manyan motoci ba na wasa ba, ga bikes da kekuna ina ji na yaran shine. Daga nan kana iya hango wani dan karamin garden a can gefen gidan, har wani dan karamin wajen wasanni na gani.
A hankali muka fito daga cikin motar, already wani da nafi kyautata zaton mai gadi ne ya fara kwasar kayana yana shiga cikin gidan dasu. Shi yayi mana jagora zuwa wani babban falo daya min kama da fadar uwargidan sarkin Kano, ya sha jere na wasu narka narkan leather seats kala biyu, farare da browns, ko wane jeren kaya yana da nashi dinning table, Plasma TV wadda zaka yi zaton zata cinye bangon falon saboda girmanta. Kafafunmu suka nutse cikin wani tattausan rug carpet kamar auduga, nayi iya bakin kokari na wajen ganin cewa ban hangame baki nayi kauyanci ba, maganar gaskiya ban taba shiga tsarraren falo irin wannan ba duk da cewa ba laifi nayi shige-shige a parlours da gidaje na manyan mutane, wannan kam looks extraordinary sosai. Kujera muka samu muka zaun 3 seats, ina tsakiyar su daddy, er aikin gidan ta fito daga kitchen ta gaida su daddy kafin ta shige wata kofa a cewarta zata kira madam. Ina jin lokacin da daddy yake gayawa Mommy ai Ibrahim din baya nan, yaje wani seminar. Ni dai ba baki, I was very nervous a lokacin. Mintuna kamar goma sai gata ta fito, Ya Allahu!! Meye wannan a gabana? Naji zuciyata tana tambaya lokacin da nayi tozali da matar. Don fari fa Akwai fari kamar Baturiya, kyawu ma Akwai shi Masha Allah, wata irin kiba marar fasali ne da ita. Lokacin data zauna akan kujera suna gaisawa dasu daddy sai naga ta shirge a waje guda kamar kayan wanki. Da kyar na iya saisaita kaina na dan zame daga kan kujerar na gaisheta, da er fara'ar ta ta amsa har da ambatar sunana, "Safeenah ko?" na gyada mata kai a hankali. Ta maida kanta gasu daddy suna er hira, idanuna suka ci gaba da wandering a cikin falon bana ma jin me suke fada. Aka kira magrib daddy ya fita sallah, ni da Mommy kuma muka yi a cikin falo don bamu samu albarkacin samun gayyata zuwa dakin matar gidan ba, kuma ba a nuna min inda zan zauna ba, karewa kayana ma suna nan baje a tsakiyar falon. 'yar aikin gidan muka tambaya ta nuna mana bayi dake nan cikin falon muka shiga muka dauro alwala, motar daddy naje na dauko prayer mat muka shimfida anan muka yi sallah abinmu.

Daddy yana dawowa daga sallah yace mommy ta tashi su tafi, nan fa idanuna ya raina fata da naga Mommy ta yiwa er aikin gidan magana akan taje ta gayawa matar gidan zasu tafi, idanuna suka yi raurau kafin kace me na fara hawaye shabe-shabe. Ba a dauki mintuna biyar ba sai gata ta fito tana taku da kyar, ban sani ba na takama ne ko kuwa dalilin kibar ta ne? Sallama suka yi dasu ta koma daki abunta. Hannuna mommy ta kama na musu rakiya har bakin motar su, zuwa lokacin kam kuka nake har da shessheka, suka saka ni a tsakiya suna lallashina har na samu kukan ya lafa. Ina nan tsaye suka shige mota suka ja suka tafi bayan na sha nasihohi daga gare su. Na bi bayan motar nasu da kallo har suka bar gidan aka maida gate aka rufe, na maida kallona ga dankareren gidan da zan rayu a ciki zuciyata cike da tarin damuwa iri-iri, daga can kasan zuciyata ina jin wata irin nadama na dabaibaye ni, Me ya kaini???? A hankali wasu siraran hawaye suka biyo kan Kumatu na.....!

Just want to say thank u for those following me, commenting and voting on this story. Please keep it up, keep voting, comment, and share it with your friends......

                          T
[11/6, 17:17] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!!*

                      ©JeedderhLawalS

                            *04*
Chapter 3 · 0% Book details