Sashe 48
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ban san me ya kamata inyi ba a daidai lokacin nan ba, juyawa zan yi in koma ta hanyar dana fito, tunkarar shi zan yi ko kuwa zan zagaye shi ne in wuce abina?? A hankali na daga kafafuna na fara tafiya har naje gabanshi na tsaya, kamshin turaren Hugo boss dana Secret Men suka ziyarci hancina har sai data kaini ga lumshe idanuna. Kaina sadde yake a kasa amma nasan cewa kyawawan idanunsa suna kaina saboda ina jin su all over my body. Na daga baki a hankali nace "Abbu ina yini, an dawo lafiya?" ya kura min idanu ba tare dana yi magana ba, a hankali na dan saci kallonshi, Kyawawan idanunsa suna kaina yana kallona intensely, muna hada ido ya wani daga gira sama, "is that all?" na bude idanu na kalleshi sosai cikin alamun tambaya, "na'am?" ya kai yatsa ya dan dangwali hancin sa tare da dan sosawa, "well, you didn't seem that happy to see me girl...." ya saddo kanshi daidai fuskata very close wanda na tabbata idan ya kara taku biyu sai hancinsa ya gogi nawa, na dan ja taku biyu baya ina jin bugun Zuciyata yana karuwa saboda kusancin da Abbu ya kirkira a tsakaninmu. Ya kalli kafafuna da suka matsa, ya dauko kallona tun daga kafafuna har zuwa kan fuskata bakinshi yayi coiling forming wani irin mischievous smile sending shivers down my spine. Ya rike idanuna da nashi yayin dana kasa janye nawa idanun daga gare shi, wasu irin abubuwa ne suke fita daga nashi idanun suna shiga nawa idanun suna haddasa min wani irin rawar jiki da bugun zuciya yayin dana fara jin zufa tana tsattsafo min a tafin hannu dana kafata, murmushi ya saki mai sauti tare da janye jikinshi ya jingina da mota, na saki ajiyar zuciya a hankali. Mota kawai ya bude ya shiga tare da bude daya bangaren ya kalleni, "get in" na kalleshi na dan lokaci kafin na zagaya ta daya gefen na shiga, kamshin freshener na water lily ya gauraye cikin motar, motar was unbelievably nice da alamun sabuwa ce, ya tashi motar muka fara tafiya yayin dana lumtsume a cikin seats din motar masu tsananin laushi, gajiyar dana yi ta fara sirarewa daga jikina, na kara relaxing gami da lumshe idanuna, ban san ina muke nufa ba, Ya Allah! Ban ko yi tunanin ina zai kaini ba na fada cikin motar shi, way to go Nafeesah!! Naji zuciyata tana tuhumata akan rashin tunanina. Na bude idanuna a hankali da niyar tambayar shi inda muka nufa, daidai lokacin yayi parking a bakin wani restaurant. Ya bude murfin motar ya fita nima na take mishi baya. Cikin restaurant din babu mutane sosai, muka samu table muka zauna. Da sauri waiter yazo da list din dishes dinsu, Abbu ya karba yayi order muka zauna jiran a kawo abincin. Abbu jingina yayi da kujera kawai ya kura min idanu yana kallo kamar wanda ya samu TV, yayin dana sadda kaina kasa ina wasa da hannun jakata. Kunya gabadaya ta rufe ni, baisan yadda kallon da yake jifana dashi yake affecting dina bane, bai san yadda nake ji kamar in nutse a cikin kasa bane saboda yadda yake kallona kamar wani wanda ya shekara dari bai ga wani abu so dear to him ba, na rasa da wanne zan ji, da kunyar shi ta tun asali dana ke ji ko ta maganar 'aure' daya kirkiro mana ko kuwa ta rejecting dinshi da nayi? Ya danyi leaning hannuwanshi akan table din yana kallona, nima kallonshi nake yi amma fa kamar wadda take tsoron shi ko tsoron jin wani abu daga gare shi, kodayake a zahirin gaskiya ina jin tsoron abinda yazo dashi ne, yaje in jira yi dawowar shi, gashi ya dawo din, me zai faru kenan? Ya bude baki yayi magana a karo na farko tun da muka shiga restaurant din, "to ya kike Nafeesah? Hope you are good?" na gyada mishi kaina, ya koma ya jingina da kujerar da yake kai a zaune tare da rabbe hannuwanshi a kirji, "well actually you kinda amazes me" na saci kallonshi ina so in san dalilin shi na cewa haka, yace "I mean ban yi zaton zan samu tarba irin haka daga gare ki ba, ace common sannu da zuwa wannan daga gare ki ta zama golden word, why Nafeesah?" nayi shiru ina sauraren shi, why? Nasan na tsinci kaina a cikin mixed emotions, na farin cikin ganin shi da kuma confusion na ganin shi da wata fargaba wadda ban san dalilin jin ta ba. Aka kawo mana abincin da yayi oda fried rice with liver sauce da plaintains sai lemun 5 alive, ya turo min nawa plate din gabana, "ci koh?" na ja plate din gabana na fara cin abincin a hankali, duk na takura saboda presence din shi a gabana. Gabadaya jina nake yi so strange, tunda maganar auren nan ta shiga tsakaninmu nake jin kaina a gaban Abbu kamar wata bakuwa na rasa ko me yasa haka?? Ya dago daga kai abinci bakinshi ya kalleni, "me yasa kika zabi zaman hostel ne?" na daga kafada, "kawai. Na ga kamar hakan zai fi sauki ne" yace "are you sure ba guduna kike yi ba?" na girgiza kai da sauri, "haba dai, gudu kuma? Beside why would I?" ya tabe baki, "wai ma idan abinda kike tunani kenan in fada miki it's of no use Nafeesah, because you will never, ever escape from me!" na hangame baki cike da mamakin wannan Al'amari na Abbu, wasu abubuwa da yake yi kwanan nan suna daure min kai, sometimes zai yi magana ne kan shi tsaye ina tunanin baya tuna cewa Nafeesah yake yiwa magana ba matar auren shi ba, yana nuna yana da control over me kamar an riga an daura mana aure. Na rufe bakina tare da kai spoon din abinci bakina, shima murmushi yayi kawai ya cigaba da cin abincin shi. Babu wanda ya sake yin magana a cikinmu har muka gama cin abincin, Abbu ya biya kudin muka fito. Sai da muka fara tafiya na kula ashe a cikin makaranta wajen yake, ko a cikin mota bamu yi magana ba sai kallona ta madubi da Abbu yake, shi kanshi yasan cewa ya takura min da kallo, ya danyi murmushi yace "na takura ki koh? Sorry, bani da zabi ne Nafeesah when you look this attractive..... Me kike shafawa fatar kine kullum wani fresh kike kara yi" naji alamun blushing a kan fuskata, Anya Abbun dana sani ne kuwa? Yau gabadaya ya zame min wani sabon mutum, maganganu yake jefa min carelessly ba tare daya kula da yadda suke affecting din zuciyana da gangar jikina ba. Yayi parking a cikin parking lot muka bude motar muka fita, na zagaya ta gefenshi nace "Abbu nagode, Allah ya saka da alkhairi sai da safe" kallona yayi ba tare da yayi magana ba, sai na rasa abinda zan yi, in jira umarnin shi ne ko kuma in tafi abina? "me yasa kika ce ba zaki aure ni ba?"