← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 88

Sashe 75

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mubeenah tayi shiru kanta a kasa, tunda take dashi bai taba mata ihu irin na ranar ba, bai taba daga murya kamar haka ba, duk abubuwan daya fada ta aikata har da ma wadanda bai fada ba duk tayi kuma sun faru, kalma daya data doke ta... “Kana Son ta?? Ni fa?! That means baka so na kenan?" without second thought ya gyada mata kai, “kwarai Mubeenah! Ni dake duk mun san cewa zaman hakuri da zaman ‘ya‘yanmu muke yi, amma zancen ‘so' kin san cewa babu shi a tsakaninmu" ta fara girgiza kai, bai jira mai zata sake ce mishi ba ya warci brief case dinshi a fusace ya ratsa ta gefenta zai fita, kofar dakin ma ko albarkacin ta rufe ta bata samu ba, tsoron shi daya Allah yasa cikin yaran babu wanda yayi over hearing din conversation dinsu yasan may be ya saka confusion a cikin kansu. Ranshi ya kara baci da wannan tunanin, daga bayan shi ya juyo muryarta a kausashe “Nafeesah!...." tun ma kafin ta gama fadin abinda tayi niyya ya juyo a fusace, “don't you ever dare drag her into this, ba irinki bace ita saboda haka ke kici gaba da laluben duniya ki barta taci gaba da laluben lahirar ta!" ya juya a fusace ya bar gidan zuciyar shi na azalzalarshi cike da bacin rai ko sallama bai wa yaran nashi ba da suke dakinsu suna kallo.
Mubeenah ta bishi da kallo cikin bacin rai na maganganun daya yaba mata yanxu, fargaba da tsoron anya bata bari kwabarta tayi ruwa ba kuwa? Dana sanin ina ma tayi amfani da magungunan da Saddiqa ta kawo mata???

******
Muna gama waya dashi falo na koma ina jiran karasowar shi. Ina cikin zaman jiran ne Zaynab ta fito daga dakin dana ware mata a sukwane tana ihu, “Anti Nafeesah.... Anty Sadiya ta haihu yanzu!!" nayi ihun nima tare da direwa cikin murna, sai da muka gama iface-ifacen na tambayeta abinda ta haifa tace Mace. Ba bata lokaci ta shirya ta tafi ganin baby. Na zauna ina jiran dawowar Abbu impatiently ina jin kamar inyi fuffuke inje inda suke. Ina dakina ina canza kaya daga shigar da nayi ta wani mini daya tsaya min a gwiwa da half vest mai hannu daya ta taryar Abbu zuwa riga da zani na atamfa, ban san ya dawo gidan ba sai dana leka waje naga motar shi a fake sannan. Abin ya bani mamaki, nayi tunanin zai shigo dakina direct idan bana falon kamar yadda yake yi, ban kawo komi a raina ba na nufin dakin da saurina cike da doki. Na tura kofar ko sallama doki bai bani damar yi ba na fara zuba mishi bayanai, “Abbu yanxu Sadiya ta haihu, kazo ka kaini in ga baby ka ji??" kwance yake yayi rub da ciki ya tura kan shi cikin filo, na zauna a gefen gadon ina dan jijjiga shi alamun ya tashi, “Abbu.... Abbu kaji?" nan ma shiru babu magana, ban sani ba common sense ne ya dauke min ko kuwa? Ban yi tunanin ina takura mishi ba ko barci yake yi naci gaba da jijjiga shi, “Abbu kazo ka kaini in ga baby kaji? Abbu??"
Juyowa yayi a fusace, cikin muryar dake hauhawa da bacin rai yace “Oh God Nafeesah!! Will you please just shut up and leave me alone??" jikina yayi sanyi ganin yadda fuskar shi take cike da bacin rai, “amma Abbu.." na fara magana in protest, “leave me alone!!" ya fada cikin karaji, sai kuma naga ya dafe kanshi da sauri, ya lumshe idanunshi na en sakanni kafin ya bude su, “please!!" ya fadi cikin sanyin murya wannan karon. Jiki na rawa na tashi na fita daga dakin ina tambayar kaina me ya hau kan shi??
Kujera na laluba na zauna cikin tsananin sanyin jiki, ban iya daurewa kwallar data taran min ba sai data gangaro kan kumatuna, gabadaya sai na dora laifin fushin Abbu a kaina. Watakila ni na dame shi da hayaniya har ranshi ya baci, kila barci yake yi na tashe shi da hayaniya kun san yadda mutane kan zama moody idan sun tashi daga barci balle shi da naje ina jijjigawa abinda Anty Shafa tace mata basa tashin mazajen su daga barci ta wannan hanyar. Ko kuma yana bukatar kadaici ne ni kuma ban kula da hakan ba? Idan haka ne kuwa ai laifi na ne. Tashi na sake yi na koma dakin, lekawa nayi kamar munafuka wannan karon yayi rigingine, na shiga dakin a hankali tare da maida kofar na rufe, barci yake yi. A hankali na dauki bargo na rufa mishi, na juya kenan naji an riko hannuna na juya da sauri. Ya bude idanunshi da suka shige ciki har sun canza kala ya kalleni dasu, take naji wani irin bacin rai na shige ni. Na samu kaina da tuhumar kaina da responsibility na bacin rai da yake ciki, a hankali nace mishi “kayi hakuri Abbu!" janyo ni yayi na fada kan gadon tare da jana jikinshi ya rungume ni, ina jin yadda zuciyar shi take bugawa da sauri, yace “noo, am sorry! I shouted at you bayan baki yi mun laifin komi ba" na kwantar da kaina akan kirjinshi ina shafa saitin zuciyar shi da hannuna, “Allah ya huci zuciyar ka Abbu na. Wanda ya bata maka rai bai kyauta min ba ni kam tunda nima yasa nawa ran ya baci" kuma gaskiya na fada, raina ya baci kwarai daga ganin bacin ran dake dankare akan fuskar shi. Yayi dan murmushi tare da jan bargo ya rufe mu dashi muka shiga barci.

Koda muka tashi ran shi wasai babu bacin rai a tattare dashi. Da yamma na lallaso shi da kyar muka je gidan Sadiya muka ga baby don da cewa Yayi wai ya za ayi in fara fita ina amaryar sati daya? Da kyar da jibin goshi ya bar ni bayan na dauki alkawarurruka da dama wadanda sirrin mu ne, daga can muka wuce ya fara koya min mota sai gab da magrib muka koma gida. Kwana biyu da yin haka visar mu ta fita kasashen ketare yawon bude ido (honey moon) ta fita. Da kaina na zauna na fitar da kasashe biyar wadanda nake matukar so da burin ziyarta a rayuwata. Muka fara shirye-shiryen tafiya amma fa bayan anyi sunan Sadiya.

~Daga yanzu ba zaku dinga ganin posting dina akai-akai ba gaskiya, mun koma school kuma things are somehow... Kun dai san lamurran en makaranta ina fata za ayi mun uziri?
#TeamAbnaf
#AnaTare

*♡Jeedderh♡*
*NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*®°•Fikrah Writers Association°•*🖋

*53*

A rana ta uku da haihuwar na kara komawa gidan Sadiya daga can bayan Abbu yaje ya dauke ni da dare muka biya ta can babban gida gidan su Abbun muka gaida iyayen shi, Hajiya Siyama mutuniyar kirki ta amshe mu da hannu bibbiyu har da dan guntun fadanta wai me yasa ya barni na fara fita yanzu? Har tana karawa da cewa wai ai su a zamanin su amarya sai tayi rabin shekara kafarta bata taka kofar gidanta ba., na kama baki a raina na kara da lallai kuwa! Bayan mun gaisa ta saka mana albarka muka wuce sashen Hajja Fati itama muka gaida ta. Nan ta hada ni dasu tarkacen daddawa da sauran su. Mahaifinsu kuwa kwaryar zuma farar saka mai kyau ya bani, daga nan muka juya gida hannu riki-riki da tsaraba.
Ranar sunan kuwa da safe na tafi. Muna ta ayyuka da tsare-tsaren wajen da baki zasu zauna bayan falo. Sai bayan la'asar su Anty Mubeenah suka iso gidan ita da yaranta lokacin muna can bayan gidan muna suyar samosa wadda ake ba baki.
Ni'imah data kai wa su Anty Ameenah wadda muka soya ta dawo, ta daddabo ni tare da rada min “ga fa uwargidan ki can tazo!" naji kamar zuciyata zata faso kirjina saboda bugawar da tayi, ganin yadda nayi kuru-kuru da ido yasa tayi dariya, “haba babe cool mana, sai kace wadda zata cinye naman jikin ki?" nayi murmushin yake kawai.
Ni'imah ba zata gane halin da nake ciki ba, ba wai tsoron Anty Mubeenah nake ji ba, kawai ina fargabar yadda karon mu da ita zai kasance a matsayina na matar Abbu-Mijinta a halin yanzu, nasan ko kallon banza ba zan samu ba wannan karon, fatana daya mu rabu da ita lafiya ba tare da rayuka sun baci ba. Don haka nayi gefe daya da tunanin naci gaba da rolling din da nake yi.
Har inda muke Hafsy ta lalubo ni, nan ta zauna tana ta zuba min labarai har muka gama, aka shiga da wadanda muka yi ciki mu kuma muka shiga BQ muka yi wanka muka gyara jikinmu.
Wata uwar sun shadda muka saka a matsayin ankon suna, dark purple ta sha aikin pink din zare, Ya Allah! Zo kuga yadda na fita a cikin kayan nan. Kyawuna ya fita sosai kamar ka sace ni ka gudu, muka tsaya muka dan karkashe flashes kafin muka koma cikin gida. Bayan dogon hesitating da tunanin zanyi ko ba zan yi ba, daga karshe dai nayi sallama dakin maijego na shiga cikin dakiya duk da cewa zuciya na wani mayen tsere take yi a cikin kirjina.
Chapter 75 · 0% Book details