← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 88

Sashe 29

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read

Minti biyar tsakani naji Wayata tana vibrating, da sauri na janyo ta, as expected; Abbu ne. Sashe daya na zuciyata cike yake da murnar jin muryar Abbu yayin da a gefe daya nake jin wata er fargaba da tsoro dana rasa ko na menene a cikin raina. Na daga wayar da sallama cikin wata siririyar murya wadda ban san ina da Ita ba. A nashi bangaren sai da yaji wani yarr! Hakan ne ya haddasa mishi sanyin jiki da sanyin murya a lokaci guda, shima cikin sanyin muryar ya amsa min, yace "Why didn't you call early?" ban fahimci abinda yace ba nace "naga dare yayi ne shi yasa na maka text" wanda a hakikanin gaskiya ba haka bane ba, ina jin tsoron abinda jin muryar Abbu zai haddasa min a cikin jikina ne, yace "it's just nine fa, ya kike anyway?" nace "lafiya lau...... Naga sarkar daka bani, nagode sosai" ya dan yi er dariya, "shine Daddyn ki ya kira ni yau tun da safe yana interrogating dina kamar wani wanda yayi kyauta da abinda bai dace ba, sha ya bani dariya sosai ya kuma burge ni" naji na dan saki murmushi, ina so inji ana yabon iyayena, nace "sarkar ce Abbu naji Mommy tace babba ce, why would you give me such a precious thing?" na tambaye shi abinda nake ta tunani tun dazu, me yasa zai bani sarka babba haka ni ba diyar shi ba ni ba matar shi ba, in fact bamu hada ko wace irin alaka dashi ba sai ta Diyar Aboki da Abokin Uba? Ya katse ni ta hanyar cewa "Because I can ofcoure! So ya kika ga sarkar? Ina fata ta burge ki?" na kalli zoben hannuna naga yadda ta kayata hannun nawa sosai, nace "Sosai ma Abbu, zoben ya zauna a hannuna perfectly kamar don ni aka yi shi" yace "ai dama saboda Ke aka yi shi din" na danyi jim ina so kada in yiwa amsar tashi fahimtar da ba kenan ba, na maida akalar hirar tamu zuwa wata daban ta hanyar tambayar shi ina su Hafsy! Yace "pretty ta sha kuka tun jiya har dan zazzabi tayi saboda tafiyar ki" nace "Allah sarki Hafsy! I really miss her so much!" ba zato naji yace "ni fa?!" tsit nayi ina kifta idanu, maganar tazo min a bazata, ya sake cewa "ni fa? Didn't you miss me?" cikin wata irin seductive murya, Ya Allah! Me Abbu yake nufi da innocent rayuwata ne yake min magana cikin irin wannan muryar? Na tabbata da a kusa dashi nake babu abinda zai hana ni jefa jikina kan shi, cikin rawar murya numfashi na har daukewa yake nace "Abbu... Sai.... Da safe. I gotta go" daga can bangaren shi ya dan hade ran shi, a hankali yace "you are not enjoying having my company?" nayi saurin girgiza kaina, idan da mutumin da nafi jin dadin hira dashi duk duniyar nan wanda nake ganin ko kwana zamu yi akan waya muna hira ba zan gaji dashi ba to Abbu ne sai dai ina tsoron abinda zai je ya dawo, bana fata in sake dandana abinda naji daga Muneer a wajen ko wani namiji kenan ya zama dole in janye jikina daga Abbu tun kafin inyi ending up hurting my self. Nace "m just a bit sleepy ne Abbu" yace "ok, yakamata kiyi barci kam. Sweet dreams to you" "Thanks.... And same to you!" na karasa fada more like a whisper to myself, ban sani ba ko yaji ko bai ji ba? Bana ma so yaji din ni, nayi sauri na kashe wayar. Makale ta nayi a kirjina daidai saitin zuciyata ina ajiyar zuciya idanuna a lumshe, na kwashe Lokaci mai tsawo a haka kafin in silale kan gado in kwanta. Babu abinda ya dinga dawo min a cikin kaina irin fuskar Abbu, yanayin yadda yake gudanar da rayuwar shi very cool and impressive, murmushin shi, yanayin kallon shi, zubin halittar shi.... A takaice dai da tunanin Abbu nayi barci a ranar. Wasu irin mafarkai na dinga yi barkatai kala-kala kuma cikin su babu wanda ban ga Abbu a ciki ba. Muna zaune akan wani lilo ni dashi a wani hadadden lambu mai cike da ni'imah, hira muke yi dashi duk da bana sanin abinda yake fada amma murmushi nake tayi a mafarkin har ina hadawa da dariya, ya dauko strawberry da fork ya miko min, na daga bakina kenan zan karba naji an daka min duka a kafada ba shiri na tashi daga mafarkin da nake, hannuna dafe da kafadata inda yake min xugi na tashi zaune ina kallon wanda ya aikata wannan danyen aiki. Mommy ce tsaye a kaina tana hararata, tunda naga haka nasan abinda nayi. Da sauri na kai duba na zuwa jikina, as I expected; babu riga. Da sauri naja bargo na rufe zuwa wuyana tare da sadda kaina kasa, nasan cewa yau mai kwatana a hannun Mom sai Allah. Cikin hararar da take jifa na dashi tace "Yanzu saboda Allah Ummiey har yanzu baki daina wannan rashin hankalin da kike yi ba? Haka kika je gidan mutane dama kina musu tallar halittar jikin ki?" da sauri na girgiza mata kai, "A'ah wallahi Mom, bana yi a can" tace sai anan koh saboda kin raina ni ko" nayi saurin girgiza kai nan ma "Allah Mommy ba haka bane, ni fa ban ma san lokacin dana cire rigar ba" tace "rufa min baki nan uwar en zagin baki tun yaushe nake miki fada game da haka Ummiey? Amma saboda taurin kai saboda kin maida ni abokiyar wasan ki baki ji koh?" tuni hawaye suka ciko min ido abinda nasan Mommy bata so kenan, cikin shagwaba nace "Allah Mommy da gaske nake. Nima fa ban san lokacin da nake cirewa ba, kawai ji nake yi kamar rigar ta na shake ni sai in kasa numfashi shi yasa nake cire rigar kuma fa na daina Allah da gaske, ban san ya aka yi na cire jiya ba" ta kalleni kafin ta kauda kai ta juya zata bar dakin, "sai ki tashi ai kiyi sallah koh? An kira tun dazu" na bita da kallo har ta bar dakin, sighing nayi a hankali tare da lalubo rigata da nayi jifa da Ita a kasan gado na zura, saukowa nayi daga kan gadon na fada bandaki.

*♡Jeedderh♡*
[12/2, 22:16] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*25*
Chapter 29 · 0% Book details