Sashe 47
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read
High waist blue jeans, shabby coffee color T-shirt, black veil rolled, black and white kimono, jakar poshter rataye a kafada, one last look a jikin mirror na tabbatar dana fita yadda nake so. Yau ne ranar da zan zana exam dina na karshe a Kasu, probably rana ta karshe da zan taka kafana zuwa cikin makarantar idan ba da wani dalili ba dai. Na saka sneakers a kafada baki tare da daukar wayar hannuna na fita, karfe tara lokacin dana fita bakin titi, kafin in isa Kasu tara da rabi tayi already don haka exam hall dinmu kawai na wuce. Kyawawan awanni biyu suka wuce kafin mu fito, daga nan bankwana muka yi da abokanan nan mu muka wuce gida, Ramlah tun a ranar ta wuce Kano zata je ta fara shirin wucewa Abuja. Nima nasan lokacin da nake dashi a Kaduna ba mai yawa bane kafin in wuce Kano saboda BUK tuni sun fara lectures dinsu tun kimanin satika biyu da suka wuce. Na koma gida na samu tarba ta musamman a wajen Iyayena, wata kwaryar liyafa suka hada min inda en uwa suka taru wajen taya ni murnar kammala karatuna, I didn't expect it but I was happy and touched. Soyayyar da Iyayena suke min abu ne mai matukar wahala in iya fayyacewa masu karatu irinta. Kwana biyu ina gida bana fita ko nan da can ina aikin barci da relieving din stress din exams. Bayan na huta completely na fara shirye-shiryen wucewa BUK tare da iyayena. Ranar Lahadi da misalin karfe hudu na yamma, tafe muke a kan titin daya dauki hanyar fita Kaduna zuwa Kano a cikin motar Daddy Hillux, tare da Mommy, Anty Uwani da Sultan. Duk wasu abubuwa da zan bukata suna bayan motar da muke ciki, komi game da karatuna ya riga ya hattama a waje guda, abinda ya rage kawai shine shiga dakin daukar lacca a gobe litinin. Anty Uwani da Mommy bakinsu yaki rufewa wajen bani lecture Akan zamantakewar cikin makaranta, rayuwa ce da zan hadu da mutanen da ban sani ba kuma inyi rayuwa dasu, nasihohi da shawarwari dai. Mun shiga cikin BUK da misalin karfe biyar da rabi. Mommy da Anty Uwani suka taya ni shirya dakin da aka kaini, mun samu occupant daya a dakin luckily musulma ce kuma bahaushiya da alamun kuma zata yi kirki. Su Mommy suka taya ni gyara kayana da hattama su waje guda. Sai bayan sallar Magriba sannan suka juya, ni da Firdausi roommate dina muka musu rakiya har parking lot. A gabanmu Daddy yaja motar suka tafi muna daga musu kallo, ina kallon su har Motar ta bace mana daga gani. Iyayena suka tafi suka barni a bakon gari, bakon waje, again, for the second time. Na kai yatsa na dauke siririyar kwallar data tarar min a ido, wannan yana daya daga cikin challenges da 'ya mace take fuskanta a rayuwarta, wannan temporary ne ma fa, zan iya zuwa in gansu a duk lokacin dana ga dama kuma na bushi iska, to ina ga nayi aure kuma? Muka juya muka koma cikin hostel Firdausi na min dariyar kukan da nake. Sallah muka yi naci abinci na jira aka kira isha'i nayi kafin nayi shirin kwanciya barci na kwanta. Sai dana janyo wayata kafin naga alamun shigowar sako, ban san yaushe ya shiga ba amma ina tunanin lokacin da nake sallah ne. Zuciyata ta shiga bugu da tsallen murna lokacin dana ga sakon daga Abbu yake, yaushe rabon da inji muryar shi? Tunda muka fara exams ya daina kirana sai dai yana turo min text akai-akai. Yau ma kamar koda yaushe ko ince ko wane lokaci, ya nake? Ya su Daddy na? Ya kara da min lale maraba da zuwa makarantar BUK sai abu d'aya daya kara, cewa yayi; "Kar in saba da zaman hostel dinsu da wuri, saboda soon.... Very soon zan bar hostel din, saboda yana dawowa zai dauke ni daga hostel din" na turo baki kamar yana ganina, "wai ya daukeni kamar wata er tsana" sai kuma na kwashe da dariya ina birgima akan gadona, Abbu bai san cewa nima jiran dawowar tashi nake yi ba ne kome? He kept bragging about it, koda yaushe cikin zancen in jira dawowar shi yake making me go curious akan me zai faru idan ya dawo din. Ina lissafe da kwanan wata, ya daura akan wata hudu din da yace zai yi. Mommy ta kira ni muka gaisa tare da tambayata yanayin wajen nace mata lafiya, bamu yi wani hira ba saboda yadda nake jera hamma tace inje in kwanta kawai, nan muka yi sallama tare da kashe wayar. Addu'ar kwanciya barci nayi tare da lumshe idona, a tunani na barci zai kwashe ni a take saboda yadda nake a gajiye amma ina! Rayuwata a gidan Abbu, iyalinshi dashi kanshi, tun daga ranar dana fara ganin su har zuwa yau ta fara min yawo a idanu, nayi juyi akan gadona a karo na barkatai ina tambayar kaina tambayoyin dana kasa samun amsar su suma a karo na barkatai, will it be okay? Zan iya kuwa?
*****
Zama a makarantar sam bai min wahala ba kamar yadda nayi zato, everything was simple and easy. Rana ta farko dana fara shiga lectured na ziyarci department din su Ni'imah, da kyar na iya gane matar nan. Ta kara fari, tayi kiba Masha Allah da ganinta kaga wadda take cikin afuwar rayuwa kila kuma har ma da albarkar aure. Ta jefe ni da harara lokacin dana yi maganar, "dallah ke har kina da bakin yin magana ne ma? Ai banyi niyar neman ki ba saboda naga kin manta da mutane. Wai Nafeesah kamar ni ace zaki zo Kano amma bamu samu labari ba, bayan nan yaushe rabon da muyi waya dake??" na dan rungumota ina dariya, "haba Amaryas tuba nake, bana so in katse muku amarcin ku ne shi yasa bana kira, kuma ma lately abubuwa ne suka min yawa wallahi shi yasa" ta janye jikinta daga nawa, "ke ai dama ba a kama ki da laifi, kullum kina da abun kare kanki" nayi dariya tare da kamo hannunta, "kin fa kara kyau wallahi, da alamun dai Bashir ya iya kiwo" tayi fari tana murmushi, "ai kawai ina shawartar ki ki tsunduma cikin auren nan kema Nafeesah, only then ne zaki fahimci abinda rayuwa take nufi. Nasan cewa sai kin nunka yadda kike da kyau yanzu wallahi" na sadda kaina kasa cikin tunani, 'ko yaya zata ji idan ta samu labarin Yayanta nake so, kuma yake so ya aure ni? Kila fa zumuncin mu ya tsaya koh?' ta zunguro ni, "lafiya?" nayi saurin girgiza mata kai. Nan na zauna na jira ta gama lecture kafin muka je wajen Sa'adiya, ita dinma dai ta kara kyau da haske da kiba. Daga nan muka wuce hostel, a can muka yi la'asar muka ci abinci kafin muka dasa dandalin hira sai wajen biyar da rabi mijin kowaccen su yazo ya dauketa suka tafi. To haka rayuwar cikin makarantar ta kasance min, kullum idan bana daki to ina lecture hall, daga lecture hall kuma sai daki. Cikin sati biyun da nayi a can tuni na saba da mates dina duk da dai har lokacin ban yi sabbin abokai ba don bani ma da ra'ayin yi, Ramlah ta ta ishe ni rayuwa. Nayi sighing a hankali tare da rausayar da kai lokacin dana tuno ta, kwana biyu ma bamu yi waya da ita ba, kewar ta na taba ni da..... Nayi saurin katse tunani na. Na tashi daga kan seat dina na fara gyara zaman jakata a kafada ta, Zakiyyah ta kalleni "har kin gama assignment din?" na girgiza mata kai, "na gaji ne, I'll finish it anjima" ta gyada kai, na mata sallama na fita daga cikin class din. Sanye nake da da riga da zani na atamfa, dinkin zanin single ne kamar yadda rigar take fitted, ban tsaya wani daurin dankwali ba na dora hijabi akan kayan wadda ta kusan sauka har gwiwa na. Yanayin garin na yau aka rana kuma da zafie, kowa dai yasan yadda Kano take idan damina ta fara shigowa. A hankali nake takawa ba wai don yanga ko wani abu ba, saboda tsabar gajiyar dake tattare dani, yau tun karfe bakwai muka shiga lacca, gashi yanzu har to five amma ban saka abun kirki a bakina ba tun karin safe. Sai dana fito daga farfajiyar da classes dinmu suke na bi wani dan karamin corridor da zai sada ni da gate din fita daga cikin department dinmu, a bakin gate din can inda aka tanada saboda ajiye motoci, wata farar Picanto ce anyi parking dinta ta yadda duk wani wanda zai fito daga wajen da nake fitowa zai yi ido biyu da motar. Yeah motar ta hadu karshe haduwa ta kuma cancanci kallon da jefi-jefi din mutanen dake wucewa suke jifanta dashi. Sai dai a gareni ba motar bace ta dauki hankali na ba, mamallakin motar ne da yake tsaye a gefen motar ya juya min baya yana amsa waya. Sanye yake da baggy pants da shara-sharan farar T-shirt don har ana iya hango farar singiletin dake jikin shi, na ja na tsaya a hankali idanu na kafe akan mutumin. Well I didn't want to jump into conclusion din ko waye duk da nasan cewa halitta ce da ko mutuwa nayi na dawo zan shaida ta. Sai dai wannan ta banbanta da wanda na sani, yadda fatar jikin mutumin da bakar sumar kanshi suke sheki a cikin hasken ranar ya saka ni doubting Anya shine? Kamar Wanda yaji wasi-wasi da tantamar da Zuciyata take ciki, a hankali ya juyo ya sauke idanunsa a kaina, and there He is, Abbu Galadanchi standing right in front of Me......
*♡Jeedderg♡*
[12/23/2017, 13:52] Beluvd Zee: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*
*©°•Jeedderh Lawals•°*
*38*