Sashe 55
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 6 min read
"Dr. Ibrahim baka tunanin lokaci yayi da xaka yi recognising din soyayya ta zuwa gare ka? Kana sane da halin da ruhina yake ciki saboda kai, soyayyar ka na azabtar da zuciyata a kowace rana amma kayi kunnen uwar shegu dani kana nuna kamar baka san komi ba, haba Ibrahim, ka tausaya min mana please!!" kafafuna suka shiga rawa na kasa yin knocking din da nayi niyar yi, a hankali na matsa ta jikin tagar office din da yake a bude take. Abbu yana tsaye ya juyawa tagar baya, ya rungume hannayen shi a kirji yana fuskantar ta yayin da ita kuma take fuskantar tagar duk da cewa dai bana iya hango fuskar ta amma yanayin shigar da tayi m not satisfied with it. Ko dai tayi kwalliya ne don tayi seducing din Abbu na ko kuma ta saba yin tambadaddiyar shiga ta marasa mutunci kamar yadda tayi yanzu. Abbu yace "Dr. Luba Ina ga wannan abu ai yana gare ki ne, ba tun yau ba na riga da na fada miki cewa Ina da aure har da 'ya'ya...." ta katse shi, "nima ai nace maka zan iya aurenka a hakan, meye hadina da matar ka ni? Kai zan aura ba ita ba!" yace "am getting married, in the next two months in shaa Allah!" ta laulayo wani ashar ta maka, "says who? Karya ne Dr Ibrahim, wallahi Karya ne! Babu 'ya macen data isa ta aureka Ina tsaye Ina kallo, idan ma wasa kake yi tunda wuri ka fadi kafin in aikata abinda ran mu ba zai mana dadi ba" yace "me yasa zan miki wasa? Ba tsoron ki nake ji ba kuma ba shakkar ki nake yi ba, ban san ko sau dubu nawa kike so in fada miki cewa bana son auren ki ba, you are not my type Ramlah" tace "but you are my type, and there's no way da zan zauna ina kallo a gaban idona wata ta dauke abinda nake so ba, Karya ne wallahi...." ta kara taku zuwa gaban shi ta kai bakin ta daidai kunnen shi, ban san me ta rada mishi ba, naga dai taja da baya yayin da Abbu yayi shiru kawai, can kuma naji yace a hankali, "get out please Dr Luba" tace "ba kai kace in zo ofishinka ba ra'ayin kaina ne, don haka idan zan fita ma yanzu sai nayi ra'ayi, gashi kuma ban gaji da ganin fuskar ka ba, ya za ayi kenan?" na hangame baki cike da tsananin mamaki, lallai duniyar Allah mai fadi, xaka ga mutane daban-daban masu hali iri-iri, ita kuma wannan wacece? Zuciyata ta hau wani suya kamar zata fito daga kirjina, ji nayi kamar in banka kofar ofishin in shiga in jawo ta by her hair in fada mata Abbu nawa ne, in ma ta kai ga tofa mata yawu a fuska duk zan yi matukar zata fita daga cikin rayuwar Abin sona. Na koma ga kofar na fara knocking da karfina kamar zan balla ta, Abbu ne ya min izinin shiga. Na tura kofar na shiga with full of attitude and Charisma, so that wadda take ikirarin mallakar Abbu na ta karfi da yaji taga cewa am not the type of people da ake musu kwacen abinda suke so, abinda suke Jin cewa ba zasu rayu ba tare dashi ba right in front of their eyes ba tare da sun yi abu ba. Abbu ya juyo yana kallona, murmushin daya saki kadai yasa naji wani irin kwarin gwiwa ya mamaye ni, naji duk wata fargabar kada fa matar dake gabanshi ta kwace min shi ta tafi ta barni a take, tabbas Abbu shine mahadin rayuwata. Nima na mayar mishi da martanin murmushin wanda yake kunshe da zallar so da nuna tsananin kewar shi da nayi kafin idanuna suka sauka akan matar dake ikirarin claiming din abinda yake nawa. Ta sha uwar kwalliya a fuska saboda tsabar kwalliya ba zaka tantance ainihin kala ko kamanninta ba, tasha adon izgar doki wanda ya sauko a kafada da gadon bayanta, wani material ne a jikinta an mishi wani irin watsattsen dinki na Allah wadai wanda ya fito da shafaffen kirjinta kamar shafaffen silifas, dinkin ya matse ta tun daga kirjinta har cinyoyinta, ta wani kalleni tun daga sama har kasa yayin da nake kallonta disgustingly cikin nuna kyama kamar wadda taga abin kyankyami wanda na tabbatar da cewa sai ya kada mata 'ya'yan hanji. Abbu ya katse mana kallo-kallon da muke wa juna ta hanyar cewa "Dr Luba meet my dearing wife, Nafeesah. Nafeesah she's my co worker" nace "sannu, ya kike?" ta tabe baki tana wani yamutse fuska, "wannan abar ce dama kake wani tada jijiyoyin wuya kana cewa wai zaka aura? Me ta fini dashi?" Abbu yace "ko zaki iya bamu waje, Ina son sirri" ta buda kofofin hanci har suna naso, "ko baka ce ba yanzu zan bar maka ofishin ka kafin ka wulakantani a gaban wannan er yarinyar, sai dai kada kayi tunanin na hakura ne, ko ta halin yaya sai na mallake ka Ibrahim saboda kai nawa ne!" ta warci jakar hannunta ta fita tana murguda kugu kamar wani shafaffen plate saboda rashin cikowar shi, na bita da kallo Ina murmushin mugunta, matar nan ta rainawa kanta hankali da yawa, ni ta kira da yarinya koh? Allah ya kara hada ni da ita wani lokacin, ni kuma nayi alkawarin nuna mata aikin yarinta. Na maida kallona ga Abbu lokacin data fita daga office din ta maida kofar tayi banging kamar tashin duniya. Murmushi na sakar mishi softly, duk da cewa har zuwa lokacin zuciyana tana itching game da Luba ce ko Bana yace sunanta? Bana so in sani. Yaja kujera ya zauna a kusa dani tare da nuna min wata kujerar nima na zauna, yace "kiyi hakuri da abinda ya faru, kada kuma ki sa maganar ta a cikin ranki, ta saba irin wadannan maganganun duk burga ce da tauna tsakuwa don aya taji tsoro" nace "wai wace? Ni ban ma fahimci abinda take fada ba balle in saka shi a cikin raina...," ya kura min idanu yana murmushi, "kin san abinda yasa nake kara jin ki a cikin raina kenan? Nafeesah my other being" na sadda kaina kasa Ina dan murmushi, Abbu with his flirtations, a hankali nace "sannu da dawowa, ya hanya?" yace "it was tiresome, amma yanzu na dawo normal dana gan ki, my wife!" wayyo kunya! Na rufe fuska ta da hannuwana ina er dariya, shi kuwa dariya ya saki sosai, a tausashe. Nayi shiru Ina jin dariyar da yake yi, he sound so relieved and happy, and I feel proud knowing that ni ce sanadin farincikin da yake ciki.