← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 88

Sashe 7

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai wajen karfe biyar da rabi na yamma na tashi daga barcin, toilet na shiga nayi wanka na fito na kimtsa jikina cikin wasu simple Pakistan riga da wando marasa nauyi, turare kadai na fesa a jikina da yake bana yin Sallah sai na koma kan gado na fara sana'ar chatting da kallace-kallacen film. Babu wanda ya leko dakina sai bayan isha'i Hafsat ta leko wai inje mu yi dinner, ina jin yunwa amma jin muryar Abbu a falon yasa nace mata a koshe nake, tayi tayi dani naki fita dole ta juya ta tafi tana gunaguni. Can kuma sai gata ta dawo dakin, "wai Abbu yace mai kika ci?" nace ban ci komi ba, Tun lunch ne amma ciki na a cike yake. Ta juya ta tafi, mintuna biyu ta sake dawowa, "Abbu yace ki fito ki ci abinci ko ran ki ya baci!" nayi shagaraaaa da baki ina kallonta cikin rashin abin cewa, ganin bani da niyar tashi yasa ta juya tana fadin "bari inje in gaya mishi kin ce ba zaki zo ba" da sauri na tsayar da ita tare da tashi tsaye na lalubi hijabi dogo har kasa na saka, Hafsatu ta saka ni a gaba kamar wadda zata gudu har gaban dinning table din Inda suke zazzaune bayan ta gama mitar wai gidan wa zan je dana saka hijabi, ban tanka mata ba, fargabar yadda zan zauna a teburi daya da Abbu ta cika min ciki, tsakani na da Allah ina jin kunyar shi. Naja kujera daya na zauna a hankali kamar wadda tayi laifi, daga Qaseem sai Abdul a wajen sai shi Abbu din Anty Mubeenah bata nan ban sani ba ko bata gidan ne? Tun kafin in gaida Abba ya tare ni, "wasa da cin abinci ko Nafeesah??" na sadda kaina a kunyace nace "Abbu na koshi ne" ya girgiza kai, "that's not an excuse, dokar nan gidan ba a skipping meals uku ko da wasa, idan ma mutum bai jin yunwa sai ya tsakura, idan kuma ya ki dura muke mishi koh?" ya kalli su Qaseem kamar yana tambayar su, yaron ya gyada kai yana er dariya wadda ta fito mishi da goyen hakoran shi, ni kaina I couldn't help it sai da nayi er dariya jin abinda yace, yace oya ci abinci. Babu musu na dauki spoon na jefa cikin jollop shinkafa da aka yi an kawata ta da nama, kifi, coleslaw da wainar kwai. Kamar dazu da safe abincin yayi dadi sosai kamar kunnen mutum zai tsinke, ga zobo mai sanyi a gefe ya sha kayan kamshi an yanka kankara, apple, cucumber da wasu nau'i'kan fruits dana kasa tantance ko menene. A nutse muke cin abincin, su Hafsat suna hirarsu da Abbu jefi-jefi su kan Sako ni a ciki ina amsawa da uhm ko a'ah, tun dai ina nodding har na dan sake na fara maida musu amsa sosai, Abbu yake tambayana game da karatu na ina bashi amsa a nutse. Muka gama cin abincin na kwashe kayan duka na kai kicin, sauran abincin da drink din na saka su a freezer su kuma kayan na wanke su tass. Falon na koma na zauna don Hafsat tayi kini-kini ta hana ni tafiya dakina dole na zauna a cikin su, su Abdullahi game suke yi a laptop din Abbu ita kuma Hafsatu na canza channels, bayan dogon lalube muka tsaya a mbc 3 suna hasko Despicable Me part 1. Muna cikin kallon muna kwasar dariya ni da Hafsat, gabadaya mun hade falon da hayaniya. Abbu ya fito daga dakin da yake fuskantar dakin Anti Mubeenah sanye da bakar jallabiya a jikinshi, take nayi tsit kamar bani ce nake ihun dariya ba. Ya zauna a kujera tare da daukar Hafsat ya dora ta akan cinyar shi tare da kallona, "are u a kindergarten kike kallon cartoon da girman ki??" kafin inyi magana Hafsat tayi caraf tace "Abbu tana dasu da yawa a cikin system dinta, har dasu na Disney princesses da fairy tales da......." ta fara jero mishi sunayen films kala kala ni wasu ma ban rike su ba, Abbu sauraren ta kawai yake yi yana gyada kai amma fa idanunshi suna kaina, hakan yasa naji gabadaya kamar wadda aka zare mata duk wani kuzarinta. Sai data gama lissafin sannan ya magantu, "wato dama saboda fina-finai kika sa aka sai miki laptop ba don karatu ba koh?" nayi saurin girgiza kaina, "a'ah Abbu! Ina yin karatu fa. Akwai text books a ciki da yawa da videos dinsu kuma Akwai docs da dama duk a ciki, da gaske ina yin karatu" ya kalli Hafsat, wai?? Ta gyada kai da sauri ehh Abbu, watarana ma tana koya min, kuma har Assignment take koya mana ni dasu Yaya Abdullahi. Ya daga gira daya, "Ohh really? A wani mataki kike a Islamiya?" kaina a kasa nace "nayi saukar Al-Qur'ani mai girma, na gama harda watanni biyar da suka wuce, na sauke littafin Umdatul-Ahkam, Riyadussaaliheen, Tafseerul-Jalalaini da Tafseerul-Ibn-Khatheer, da littafai da dama. Na fara Annissa'u war-rijaalu fil jannah amma ban gama ba har yanzu" yace "Mashaa Allah! I am impressed gaskiya" na sadda kaina kasa ina murmushi zuciyata cike da kaunar iyaye na da suka tsaye min na samu karatu mai inganci, tun ina primary six na sauke Al'Qur'ani mai girma, ban fara harda ba sai dana sake yin wata saukar sannan na fara tare da wasu manyan littafai na addini nasan ko a haka na tsaya Alhamdulillahi bani da matsala amma ban tsaya din ba, har yanzu ina cigaba da karatu na duk da cewa har gida Malamin yake zuwa yana koya min. Ganin ban yi magana ba yasa ya cigaba, "da alamu nima zan kawo nawa littafan ki dinga koya min don cikin wadanda kika ambata Akwai wadanda har yau ban gama su ba, zaki koya min?" mamaki ya matukar Kama ni, duk cikin saukin kan mutumin ne haka ko kuwa wani abu daban? Dana rasa abin cewa sai kawai nayi murmushi na maida kallona ga TV ba wai don ina fahimtar abinda ake yi ba anymore, sai don in janye yawan tambayoyin Abbu wanda nasan da kyar ne in samu amsoshin su. Ina ji yana tambayar Hafsat karatun ta tana gaya mishi abinda suka yi a Islamiya ranar, ta karanto mishi Hadisi da Qur'an ya saurara tare da gyara mata Inda ta kuskure.

Karfe tara da rabi suka gama film din da muke kallo, Abbu ya umarce mu da muje mu kwanta saboda makaranta. Sai da safe muka mishi kowa ya wuce dakin shi, anan muka bar shi yana danne-dannen laptop. Ina shiga daki su Mommy na kira don gabadaya ranar bamu yi waya dasu ba, muka gaisa dasu mun jima muna hirarraki kafin na musu sai da safe muka kashe wayar. Bayi na shiga na kimtsa jikina nazo na kwanta.

Washegari abincin mu marar taste da armashi ya dawo, Ashe wanda muka dinga ci daga gidan su Abbu aka kawo shi. Ni dai na tsakuri iya wanda zan iya ci na tashi, suma yaran haka nan dai suka tsattsakura muka tashi muka tafi makaranta. Ranar juma'a kamar satin daya wuce, ina dawowa naci karo da direba yana jira na, sallama nawa Anty da Hareera na tafi Kaduna wajen Mommy da Daddy na.

●●●●●●●●●●

Kimanin wata na daya da zuwa Kano, na riga nayi adopting da garin da yanayin gidan da nake zaune. Abbu bai cika zama a gida ba, it's hardly yayi sati daya cur a gida, yawanci zuwa seminar ko kuma harkokin shi na kasashen turawa, na Ji Malam Bala ne ranar nan yace wai suna shirye-shiryen bude wani kamfanin kirar kayan sawa ne a China shi da abokan shi. Anti Mubeenah ma dai bata cika zama a gidan ba, yawanci ko tana gidan ma bata cika zama a falo ba shi yasa har zuwa lokacin bamu wani shaku da ita ba, tsakani na da ita gaisuwa ne kawai. Abin yana matukar daure min kai, ban taba ganin wani daga cikin dangin Abbu ba a gidan, amma nata da abokanta suna yawan zuwa har yini suna yi, daya daga cikin nasihun da Mommy ta min lokacin da zamu taho Kano shine kada in kuskura in shiga harkar da babu ruwa na, banda shisshigi da sa ido a rayuwar mutane, don haka na kauda kaina daga rayuwar su, koma meye ke faruwa dai rayuwar su ce ba tawa ba.
Chapter 7 · 0% Book details