Sashe 13
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read
Hankalina gabadaya ya tafi ga tsame doyar da nake yi daga cikin frying pan naji motsi a bayana, da sauri na juya har mai na fallatsan min a hannu na danyi kara kadan. Abbu ne sanye da wandon Jersey me layi layi irin na sport navy blue da top grey, gaban rigar zuwa tsakiyar kirjinshi ya jike da sweating alamun daga exercise yake. Yadda kayan nan suka mishi kyau suka mayar dashi kamar wani matashi at his Twenteth, you might even mistook him da wani modeler a babban kamfanin nan dake saka kayan sports, ko kuwa..... Ban san cewa na dulmiya cikin tunani ba sai dana ji saukar tattausan hannunshi a dantsen hannuna, tingling feeling din dana ji bashi da maraba da irin wanda naji ranar nan da nayi mistaking taba hannunshi. Na zabura nayi tsalle gefe guda tare da sakin matsamin dake hannuna ya fadi a tsakiyar kicin din, Abbu ya dube ni cike da mamakina, "hey! Are you ok??" cikin zaro idanu da rawar murya nace "ehh?" yace mai ya fallatsan miki a hannu, are you ok? Baki kone ba?" sai lokacin na tuno, sai kuma a lokacin naji zafi a wajen. Na dago hannun na kalli Inda man ya taba, thankfully bai yi komi ba sai dan ja da wajen yayi, nace "lafiya lau babu abinda ya same ni.... Ina kwana Abbu?" na fada ina dan dukawa, ya amsa, tare da dorawa da, "ya aka yi kike girki tun da safe?" na duka na dauki matsamin dana yar a kasa ina cewa., "Harirar ce bata jin dadi, shine tace in kama mata" ya gyada kai. Nace Akwai abinda kake bukata ne? Ya zuba min ido kamar mai tunani, "abinda yake bukata?" me yake bukata exactly? Shi dai yasan yana cikin yin exercise dinshi yaji kamshin girki mai dadi yana bi ta cikin hancinshi, kamar maganadisu haka yaji ana jan shi har cikin kicin din..., ganin bai amsa ba yasa na juya na fara kwashe doyar dake cikin kaskon na fara tsoma mata. Yayi gyaran murya tare da fitar da dan sautin tari, "ehhhem, ruwa nake so" na bude fridge na dauko mishi mara sanyi na mika mishi da hannuna biyu ya amsa idanunshi na kaina. Na sadda kaina kasa saboda wasu particles da naga suna fita daga cikin idanunshi nashi suna shiga ta nawa kamar mashi, dan murmushi yayi ban san me yake nufi da hakan ba. Sai daya shanye ruwan tas ya miko min goran, na amsa na jefa ta cikin dustbin. "What can I help you with?" na jiyo muryar kamar daga sama, da sauri na dago ina kallonshi cike da mamaki, ta wani bangaren kuma ina tantamar Anya shine ya furta maganar? To amma waye zai furta idan bashi ba? Mu biyu ne kadai a kicin din. Kai na girgiza mishi a kunyace, ya daga kafada, "k! Let me go and take a shower then" ya juya ya bar kicin din, ni kuwa me zanyi ba kallonshi ba? Har ya fita daga kitchen din. Na maida bayana na jinginar da canter, idanuna a lumshe ina kokarin tantance abinda ke faruwa da jijiyoyina, kwalwa da zuciyata.
Bakwai saura na gama shirya komi akan dinning table, a gurguje na watsa ruwa na fito. Yau kam ban tsaya yin kwalliya ba balle bata lokaci wajen ciro kaya, simple kwalliya nayi daga hoda sai janbaki, na janyo wata atamfa English maroon color, dinkin rigar fitted ne sai zani 6-pieces, na kashe saurin dankwali kaman inji ne yayi ba hannu ba, na fesa turare tare da daukar jakata na zura flat din takalmi baki naja gyale na fita falon. Gabadaya kowa ya hallara akan dinning, nima sahun su nabi. Naja kujera kusa da Hafsy kamar yanda nake yi na zauna, Anty Mubeenah na gaida wadda yau er kwalliyar safen ma da take yi ba tayi ba da alamun ba zata leka wajen aikinta ba yau kenan. Shima Abbu sai dana sake gaida shi, shi kam a shiryen shi yake cikin Kaftan riga da wando ruwan madara bai san hula ba amma fa yayi kyau kamar ka sace shi, su Qaseem suka gaida ni kafin muka fara cin abinci a nutse. Abbu ya kaimu makaranta yau, sai da muka ajiye su Hafsy kafin muka wuce. Ina zaune a gaban motar kaina a kasa, a darare nake kamar ace kyat! In zura da gudu, kira'ar Sheik Sudeis ce take tashi a cikin motar cikin suratul-Anfal, munyi nisa sosai babu mai yin magana a cikin mu. Ya kalle ni yayi dan murmushi, "me yasa ba kya sakewa ne idan ina kusa dake Nafeesah?" ya tambaya idanunshi akan titi kamar ma bashi ne yayi maganar ba, na kara sadda kaina kasa, Ya Allah! M I making it too obvious?? "umh?!" ya kara tambaya jin nayi shiru ban amsa ba, "ko kina jin tsoro na ne Nafeesah?" da sauri na girgiza kaina, yace to meye? Da kyar na iya cewa "babu komi Abbu?" ya kalleni sosai da idanuwanshi masu kama da wanda yake jin barci, da sauri na janye idanuna daga cikin nashi, yace "anya kuwa Nafeesah?" na gyada kaina da sauri, "da gaske nake Abbu, ba tsoronka nake ji ba" ya tabe baki yace "koma dai menene Nafeesah kiyi kokari ki rage shi, bana son hakan ko kadan kin gane?" na gyada kaina, yace good! Daga haka muka yi shiru har cikin makaranta, na bude murfin motar zan fita ya miko min kudi yan dubu dubu sabbi kar da ban san adadin su ba, kallonshi nayi cike da alamun tambaya, yace karbi mana! Na dan girgiza kaina, "amma Abbu me zanyi dasu?" yace ki badda mana. Na girgiza kaina da sauri, "no Abbu. Akwai kudi a hannuna wallahi, nagode sosai" ya dan hade fuskar shi, "to dama nace dake babu kudi a hannunki ne? Karbi nan tun kafin raina ya baci mana!!" a kunyace nasa hannu na karba, nace nagode Allah ya saka da alkhairi Abbu. Yayi murmushi kawai, sai dana ga bacewar motar shi daga idona sannan na shiga cikin lab. Ranar kam muka shiga shopping complex a cikin makarantar, sai da muka ga karshen 10k din daya bani tas ni da Ramlah, tarkacen kayan kwalam dana shafawa kamar zamu bude tireda.
*********
Na maida littafin na rufe bayan nayi striking din date din ranar, calender ta ce wadda nake lissafin iyaka ranakun daya rage min in koma ga daddy na, in bar gidan Abbu. Gabana yayi wani mummunan bugawa dana tuno ranar da xan bar gidan? Me zai faru?? Nasan zan yi kewar su Hafsy sosai, I will miss them very VERY much! Zan yi kewar girkin da nake musu, yana saka ni jin cewa yes! M the controller, sai abinda na girka zasu ci.... Oops! Tunanin abinci da nayi yasa na kalli agogo da sauri, karfe hudu da mintuna ashirin, Abbu yaje Lagos, naji Ramlah tana cewa wai kamar wani event ne, Dr. Zai dinga zuwa makarantar da ba anan yake ba yana lecturing dalibai, yau dai kwanan shi hudu da tafiya tun ranar assabar, nasan dai duk yadda aka yi sun taso don tun dazu naji yana gaya mata bayan La'asar zasu taho. Na mike na fara kokarin cire riga da wando na kamfala din dake jikina, girki nake so inyi mai dadi wanda zai sanyaya mishi rai ya warware mishi duk gajiyar daya kwaso. Na saka wani blouse baki da riga turtle neck purple, na sakaye kaina cikin hula na fita daga dakin. Karan shigowar text a waya na yasa na dakata daga bude kofar da zan yi, na dawo da baya na daga wayar. Wow! Abbu ne!! Wani irin tsallen murna zuciyata ta dinga yi tun kafin inga abinda ke ciki., "on my way to the airport, me kike so in sayo miki a hanya?" nayi murmushi a hankali kamar wata wawuya, kwana biyun nan dai sai da Abbu yayi kokari yaga na saki jiki dashi, haka kawai zai saka ni a gaba da hira, wancan satin daya wuce ban samu naje gida ba, ranar Saturday ya dauke mu muka je Gidan Zoo muka yini a can, Washegari ya kaimu gidan Makama daga can muka shiga jifatu, siyayya iri-iri ya mana har sai da muka rasa abinda zamu dauka, daga nan muka wuce Golden Stars restaurant muka ci abincin lunch kafin muka koma gida, wannan satin naje gida ya kira daddy suka gaisa daddy ya bani wayar nima muka gaisa mun kwashe kyawawan mintuna talatin muna hira, ni kaina nasan cewa yanzu na sake dashi sosai, yana yawan yi mun text kwanan nan, idan ya min juma'a text ya kan hada da tambayar "hope kina lafiya? Babu matsalan komi koh?" idan kuwa yana gida watarana zai min text yace yana son abu kaza, zan dafa in dora mishi akan dinning, ko kuma in an yi girki bai mishi ba zai ce in dafa mishi wani abu, tun ina dar-dar har na daina tunda naga daga matar tashi har mai aikin da take girka abincin abun bai dame su ba.