← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 88

Sashe 8

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan satin ina gida ban je Kaduna ba saboda su Daddy sun tafi Malumfashi wajen bikin dan gidan Yayan Daddy din, ina zaune a daki ranar assabar da safe Hafsat ta shigo dakin, a shirye take tsaf cikin riga da siket na atamfa da dankwalin atamfar a saman kanta bata daura ba. Na kalleta da mamaki nace Hafsy ina makaranta ne yau baki je ba? Tace "hutu muke yi ai" na kalli kwalliyar da tayi nace "ina zaki je?" ta langwabar da kai, "Yaya Nafee ke da na gaya miki yau sunan Anti Raliya kanwar Daddy?" na dan dafa kaina, "na manta ne wallahi, har zaku wuce kenan?" ta gyada kai, "mu duka fa zamu tafi, idan kina so ki zo muje" cike da jin dadi na kalleta don dama gabadaya na takura da zaman hakanan da nake yi tun safe, nace "really? Can I??" tace why not? Bari in jira ki shirya. Dama ban dade da fitowa daga wanka ba, a gaggauce na shirya, na saka wata doguwar rigar material sky blue dinkin buba ne ta min tsaf a jikina, ban yi wata kwalliya ta azo a gani ba na shafa turare kawai na dauki gyale na yafa. Na kalli Hafsy nace "mu je?" dankwalin hannunta ta miko min tana turo baki yadda ta saba idan tana jin rigima, "dan Allah ki daura min irin yadda kika yi dinnan ranar nan?" ba musu na amsa na nada mata shi kamar gwaggwaro, ta kuwa yi kyau sosai wayata na dauka muka fara hotuna har sai da muka Ji karan horn sannan muka fita da sauri. Su duka suna cikin motar Abbu picnic yana zaune a seat din direba Anti Mubeenah a gefenshi su Abdullahi kuma a baya, ban san ko yaushe Abbu ya dawo daga tafiyar da yayi ba don tun ranar Laraba baya nan babu mamaki jiya da dare zai dawo. Gabadayan su suka bimu da kallo ni da Hafsy har muka shiga motar, a nutse na gaida Abbu. Thank goodness na daina jin wannan faduwar gaba da rikicewar idan ina kusa dashi, yaja motar a hankali muka bar farfajiyar gidan muka cilla kan titi. Muna baya ina nunawa su Abdullahi hotunan da muka yi ni dai Hafsy su Abbu kuma suna hirarsu shi da Anti Mubeenah kadan kadan Abbu ya kan juyo ya kallemu ko yaja Hafsy da hira har muka isa Gwamna Road inda anan ne ake sunan, ko shiga gidan Abbu bai yi ba yana ajiye mu ya juya tare da cewa bayan Magriba zai zo ya dauke mu.

*♡Jeedderh♡*
[11/6, 17:18] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*09*

Muna shiga gidan sunan su Hafsat suka yi nasu wurin ko dakin mai jego basu karasa ba. Ni da Anty Mubeenah muka karasa har uwar dakan mai jegon lokacin babu mutane ma sosai, aka dan yi en gaishe-gaishe Anty ta hakimce a gefen gadon ta janyo wayar hannunta ta fara danne-danne da kiraye-kirayen waya. Gabadaya naji na takura don bansan kowa a wajen ba gashi su Hafsat sun bace a cikin gidan kwata-kwata, wata farar mata ta shigo itama kana ganinta Kasan er uwarsu Abbu ce don ga kama nan kamar an tsaga kara, da dan saurinta ta shigo tana mitar ina su Ni'ima suka shiga ne sun barta da aiki ita kadai? Ta kalli sauran matan dake dakin tace ku taso muje mu gama aikin samosa din can don Allah kafin rana tayi mana, duk suka mimmike yayin da Anty Mubeenah ta kara hakimcewa akan gado, ni kam ganin zan takura na tashi na bi bayan wadanda suka tashi. A can BQ suke yin aikin, na shiga na kama musu muka fara aikin suyar Samosa, Anti Amina kamar yadda naji ana kiranta ta Kalle ni tana murmushi tace "kece wadda take IT a gidan Ibrahim ko?" na gyada kaina, tace ai last week na sha labarin ki wajen Hafsat har sai da kunnuwana suka gaji. Nayi er dariya nace Ai Hafsat Akwai surutu, ta gyada kai. Kafin mu gama aikin mun saba da Anti Amina sosai, su Ni'ima suka dawo dauke da plastic robobi wadanda za a zuba soye-soyen da za ayi a ciki, kusan dukan su sa'annina ne Sa'adiya ce ta girme mu sosai don ta bamu kusan shekara uku zuwa hudu, dukansu suna jami'ar Bayero ita Ni'ima a level two tana mass comm yayin da Sa'adiya take shekararta ta biyan karshe a BS. Kafin kace me mun saba dasu kamar wanda muka yi watanni da sanin juna, muna gama suyar samosa din muka fara shirya abubuwan a cikin robobi muna sawa a cikin Leda, abinci dama odar shi aka yo. Sai gab da la'asar muka koma cikin gidan, Anti Mubeenah bata nan wai ta tafi gidan wata er uwar su dake aure anan cikin unguwar, ina jin kananun maganganu na tashi game da halayen Anti Mubeenah din kun san taron mata ba a raba shi da kananun maganganu balle harka ta hado ku da dangin miji dama sai a hankali, ni dai nayi kunnen uwar shege dasu naki maida hankalina kansu don ba harkar shiga ta bace. Wanka muka sake yi Ni'ima ta bani wasu riga da siket na Swiss lace na saka saboda nawa na lalata su da abun fulawa sun yi fari tas. Bikin suna yaci gaba da gudana lafiya qalau, ina daga cikin masu kai da kawo na entertaining din baki, kawo abinci, dauke kaya, daukar gifts din maijego da wasu abubuwan. Duk Inda na motsa da sannun Anti Ameenah nake motsawa, naga alamu na shiga ran matar sosai. Anti Ameenah itace babbar Yayar su Abbu kuma babbar diya a wajen Alhaji Mad'udu Galadanchi, su shida ne wajen iyayensu kamar yadda Sa'adiya take bani labari, Anti Ameenah ce babba sai Abbu, sai Anti Rahina, Aminu Yayan Sa'adiya yana Bangladesh yana karatu sai Sa'adiya da Ni'ima auta. Family din sun burge ni sosai a gaskiya, na kula da hadin kansu kwarai da gaske abin ya burge ni ba kadan ba, ina son ganin yan uwa wadanda suke kula da zumuncin su sosai.

Bamu muka samu kanmu ba sai bayan isha'i, mutane duk an tattafi sai baki na nesa da dangin maijegon na kusa, muna wani daki dake kusa dana maijegon inda anan muke bidirin mu, hira muke dasu Ni'ima lokacin da Hafsat ta leko dakin tace in fito Abbu yazo zamu tafi, na dan hade fuska jin an katse min hira mai dadi da muke yi amma haka nan na tashi saboda bani da yadda zanyi na fito su Ni'ima suka biyo bayana, dakin Anti Rahina na shiga da niyar mata sallama. Abbu na zaune a cikin falonta kusa da Anti Ameenah yayinda maijegon take zaune a kujera daya rungume da babynta da alamun hirar en u want aka ce ake yi na durkusa na gaida Abbu tare da yiwa su Anti Ameenah sallama, Abbu ya mike nabi bayanshi. Su duka har maijegon suka fito mana rakiya, su Qaseem na jikin motar Abbu din suna jiran mu, duka muka shiga cikin motar. Su Ni'ima suka leko suna kara min sallama dama mun yi exchange din number waya dasu, Anti Ameenah ta miko min wata Leda mai dan girma tana kara min godiya tare da jaddada min in fa nemi maganin ciwon jiki in sha ina amsa mata da toh, Mai jegon MA ta leko tana min Allah huta gajiya da godiya sosai. Abbu kam baki a sake yake kallon en uwan nashi cike da mamaki, wannan shine karo na farko da suka fito wai da sunan mishi rakiya, sai daga baya ya kula ashe ma ba shi aka yiwa rakiyar ba, kulawar daya kamata ace matar shi ce suke wa sun kare da ba wata can, abinda yakamata ace matar shi ce tayi suke mata wannan yabawar wata can ce ta samu romon. Koda yake bai ga laifin su ba, Mubeenah ita tayi wasa da garinta har yayi ruwa, shi kanshi yaji haushin abinda tayi yau a wajen sunan nan, ance tunda taje ta gaida mai jegon bata kara yiwa kowa magana ba ko Anti Ameenah bata gaida ba, daga baya ma suka ce wai ta ajiye musu dubu goma ta tafi tun kafin ayi Azuhur abinda ya bata ran Anti Ameenah kenan, ya girgiza kai cike da takaicinta, duk iya kokarin shi na ganin Mubeenah ta ra6u da dangin shi don su saba abin yaci tura. Shi har bai san me zai mata ba kuma.

Sai da muka gama sallamar mu sannan suka koma gefe suka tsaya suna kallonmu tare da daga mana hannu har Abbu yaja mota muka tafi. Tunda muka fara tafiya babu wanda yayi magana, su Hafsy tuni tayi barci akan cinya ta. Muna isa gida na ciccibe ta muka wuce Abdullahi ya dauko min ledar da Anti Ameenah ta bani, dakin Hafsy na fara wucewa na kwantar da ita. Closet dinta na bude na ciro mata kayan barci na dawo na cire mata na jikinta na saka mata wadannan, addu'ar kwanciya barci na tofa mata tare da sauka daga kan gadon a hankali gudun kar in tashe ta daga barci, ina juyawa naci karo da Abbu a bakin kofa a jingine yana kallon mu. Na sadda kaina kasa na je zan wuce ta gefenshi, packet din magani ya miko min, nasa hannu na amsa ina kallon shi cikin alamun tambaya, yace maganin ciwon jiki ne Anti Ameenah tace in baki, ki sha kafin ki kwanta. Na gyada mishi kaina, "sai da safe koh?" ya fada yana kaucewa daga bakin kofar dakin, na bi ta gefenshi na wuce ya bini da kallo. Ina shiga dakina kayan barci kawai na saka na afa maganin a baki, sai dana bata mintuna kusan goma yadda maganin zai yi settling a jikina sannan na kwanta, babu dadewa barci ya kwashe ni, ni kaina nasan cewa a matukar gajiye nake saboda ba karamin aiki muka sha a gidan sunan nan ba.
Chapter 8 · 0% Book details