← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 88

Sashe 36

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty Shafa tana ta shirye-shiryen komawa nan da kwana biyu don haka bata zama a gida, tana ta faman ziyarce-xiyarce da sallama gidan en uwa da abokan arziki. Ranar juma'ah karfe sha biyu muka gama lectures, muna fitowa ni da Ramlah daga lecture hall din na hango Harith jingine da motar shi hannunshi rike da lemun team yana sha, yana ganin fitowar mu ya dago mana hannu. Ramlah ta kalleshi ta kalleni tace "wai meke tsakanin ki da Harith ne?" na girgiza kai, "to wa ya sani Ramlah? Nima kin ganni nan ban sani ba wlh" ta tabe baki, "to Allah ya kyauta!" nace "ameeeeen". Daga nan muka yi sallama. Tun kafin in karasa ya bude min kofar motar, na shiga na zauna ya maida ya rufe. Yana shiga motar na fara jefa mishi korafi ko bari ya tashi motar ban yi ba, "Wai Harith ba nace na yafe zuwa dauka na da kake yi ba?" sai daya tashi motar muka fara tafiya kafin yace "I was just in the neighborhood ne, nayi dropping Sister gidan Amarya Murja ne, shine nace bari in biyo in dauke ki tunda nasan kin gama lectures dinki" nace "ni ban ga kana shirin komawa ba" ya juyo ya kalleni yana murmushi, "why?? Saboda kin gaji da ganina? To babu inda zan koma, na gama karatuna ai" na juya na kalleshi sosai, "woah! Da gaske?" yayi murmushi more like a grinning, "nayi kankanta koh?" kaina na gyada mishi ina kara kare mishi kallo, dariya ya saka har yana dukan sitiyari. Yayi parking a kofar gidanmu, na dauki handbag dina na rataya a kafada nace thanks fa! Ya gyada kai, "Anytime!". Kallona ya tsaya yana yi, har na saka kafa ta daya waje na juyo ina kallonshi, "meye kake kallona?" murmushi yayi ya kalleni fuskarshi na nuna yana shirin yin serious magana ne, yace "Nafeesah! How about We come together with a plan and help ourselves??" na kalleshi cike da mamaki, "mu taimaki juna? Me kake nufi??" ya daga kafada kamar maganar da zai yi ba mai amfani bace, "you see, there's this girl that I like....." yayi shiru yana kallona, ban ji mamaki ba haka babu shock din da naji saboda maganar shi, to ma akan me zan ji mamaki? Hankalina na mayar kan shi gabadaya ina sauraron shi, ya cigaba "she likes me too, sai dai bata son muyi aure nan kusa. Tana karatu a Turkish ne a Abuja and sai nan da shekara biyu zata gama, ni kuma na kosa... U know....!!" ya daga min gira ni kuma na Harare shi, ya kauda kai. Gyaran murya nayi a hankali bayan na gama digesting maganganun shi, nace "to daka gaya min mai kake tunanin zan yi ne??" ya juyo yana fuskanta ta sosai, "I want us to just play a game ta yadda zamu samu wadanda muke so Cikin sauki." nima na kara gyara zamana, "so??" yace "we will pretend to be lovers infront of them, I mean idan muka yi haka kishin mu zai sa su dawo kan hanya daga kaucewar da suka yi, zamu fara da Muneer ne ko menene? Tunda Ikhram 'Cara Mia' sai nan da two months zata zo gida" na hade fuska sosai, take naji raina ya wani baci, a xafafe na harare shi nace "idan har saboda Muneer kake zaton I'll be your partner in this game then you are wrong Harith, Muneer has become 'a past' ya daina existing a duniyata!" ya sadda kanshi kasa embarrassingly, nace "But we can play it with someone, not Muneer dai" ya dago yana kallona fuskarshi dauke da murmushi, "Really Nafeesah? Oh you're really going to save my life, thank you! But waye wanda zamu bugawa wasan?" nayi rolling idanuna, "just..... By the way meye ma'anar Cara Mia din da kace?" yayi murmushi sosai, "it means My Darling in Russia" na tabe baki nace "wani fi'ili!! Ni kam bari in shiga gida toh!" muka bude motar a tare muka fita yana cewa bari ya shiga ya gaida Mommy.

A hankali rayuwa tana tafiya tana juyawa, cikin Ikon Allah minti yake shudewa ya zama awowi, awowi su koma raneku, raneku su koma satika kamar yanda satika suke juyewa su koma Watanni. Kimanin watanni biyu suka zo suka shude, ni da Harith mun yi developing wani irin shakuwa a tsakaninmu, da yawan mutane suna cewa soyayya ce a tsakaninmu ciki har da su Mommy da Ramlah, mu kadai dai muka san menene Ainihin Akalar mu da juna.

A matukar gajiye muka shiga gidan ni da Daddy a safiyar ranar Sunday kenan muna ajiye numfashi daya bayan daya, Gym muka je wanda yake a cikin unguwar mu kamar yadda muke yi a cikin weekends. Muna shiga falon kicin na wuce na dauko mana ruwa mara sanyi na mikawa Daddy daya, nima na fara shan dayan. Sai da muka dan huta kafin muka wuce dakinmu, ruwa na watsa a jikina na saka kaya kawai na fita falo. Su Mommy har sun fara breakfast don haka nayi joining dinsu, a nutse muke cin abincin, ina jin Mommy tana gayawa Daddy bikin diyar wata Kawarta da za a fara cikin satin, tunda suka fara maganar na sha jinin jikina, a gaggauce na fara tura abincin ina so in tashi in bar musu wajen. Kamar daga sama naji Mommy ta jefo min tambayar da nake gudun tayi, "Ummiey Ke kam yaushe zaki gabatar da naki Mijin ne?" sau biyu kenan tana min maganar turo da wanda muke soyayya wanda nasan Harith take nufi, na turo baki tare da kara cusa fried plantain a cikin bakina, Mommy ta kalli Daddy tace "Habibty kana jin mu fa!" Daddy yayi dariya yace "ina jin ku, kina bukatar bakina ne?" Mommy cike da jin haushi tace "Allah Habibty hakan bai dace ba fa! Yarinya kamar Nafeesah saboda Allah ace har yanzu tana gabanmu babu zancen aure, ina mata zancen ta fitar da miji kuma wai ka wani dinga wani tambaya na ko bakin ka nake bukatar ji?? Anya Habibty kana ma so Nafeesah tayi aure ma kuwa?" Daddy ya kalleta a hankali, duk da cewa maganar Mommy ta taba ranshi amma bai nuna hakan ba, he was very calm. Yace "kema kin san ba abunda nake nufi ba kenan Habibty, naga shi auren nan nufin Allah ne. Duk iya kokarinmu da tursasawar mu a gare ta idan Allah bai nufa ba babu yadda zamu yi. Nima ina son in ga auren Uwata saboda nasan Martaba da Mutunci 'Ya Mace suna gidan auren ta ba gidan Iyayen ta ba sai dai kin san bana so in tursasawa Uwata ko kadan. Kema din you are just desperate ne, amma duka-duka nawa Nafeesahr take? She's just Twenty Two Habibty!!" Mommy ta dafe kanta, "Ya Allah meke damun ku ne Kun kasa gane abinda nake nufi?" Daddy ya dafa hannunta cikin sanyin murya yace "mun fahimta Habibty, sai dai muma ki fahimce mu mana. Na fada miki Auren nan...." tayi saurin cewa "naji, naji Habibty ba sai ka maimaita ba!" yayi murmushi, "ki dinga mata addu'ah kawai Habibty, amma tursasawar ki ba shine zai sa ko ya hana ba, only your prayers will" ta gyada kai gami da yin sighing cikin saddakarwa, "To Allah ya zaba mafi Alkhairi!" yace ameeen ko Ke fa Habibty? Na saki ajiyar zuciya a sace, muka ci gaba da cin abincin mu. Can kuma Mommy ta sake dagowa ta kalli sashin da nake, "amma meke tsakaninku ke da Harith ne?" na kalleta, "Mommy, sau dubu nawa kike so in gaya miki babu komi?" Mommy tace "to ku ne na rasa gane inda kuka sa gaba" ni dai na samu na lallaba na bar musu teburin kafin wata maganar ta sake bullowa. Wayata na cire a jikin Caji na shiga cikin whatsapp, dp din Abbu na daga, ya canza shi daga wani hoton shi daya dauka cikin suits bakake ya maida shi zuwa wanda suka dauka shi da 'ya'yan shi kamar a wani restaurant ne ma, na kura musu idanu ina kallo ina murmushi, precious memories dinmu dasu suka dabaibaye ni, take naji wasu irin kewar su ta cika min ciki, har na latso lambar shi zan buga sai kuma na fasa, na sake latsawa na fasa, a tunanina idan Abbu shi yana namiji ya iya kauda kanshi daga gareni why not ni mace? Tun ranar da muka yi waya dashi bamu sake wata wayar ba sai kimanin sati biyu da suka wuce, shima tambayana yayi wai ko ina da muradin zuwa BUK inyi D.E ni kuma nace mishi A'ah, daga ranar bamu sake waya ba sai dai muna exchanging din text messages dashi. A hankali nayi tsaki tare da ajiye wayar. Littafan makarantana na dauko na fara karatu ko na samu in daina tunanin Abbu. Gabadaya lamarin shi ya fara daure min rai, idan ya kira ni a waya ko ya min text, kulawar dake cikinsu sai su sa inyi zaton so ne yasa hakan, amma yanayin yadda mu'amalar mu take ko kadan bata yi mun kama da wani abu mai kama da so ba. Yatsun hannuna na nutsa a cikin gashina ina jan tsaki ganin har lokacin dai tunanin Abbu ne a cikin raina. Tashi nayi tsam na fara canza tsarin dakina gabadaya bayan na cika dakin da sautin music har sai da Mommy ta leko ta min magana sannan na rage.

Ranar Laraba a gajiye muka baro makaranta saboda Defense din IT da muka yi, da kyar na iya kai kaina bakin gate saboda gajiya inda nayi shatar tricycle zuwa gida, Harith baya Kaduna kwana biyu kenan, yaje New York wajen hado takardun shi saboda zai fara aiki. Na tura kofar gate din gidan na shiga, yamma tayi likis lokacin. Malam Idi maigadin gidanmu yana zaune a kan dan benci yana sauraron radio, na gaida shi ya amsa da fara'ar shi gami da min sannu da zuwa kafin na wuce falo. Ina shiga sallamar dana fara yi ta kakare a makogorona sakamakon Halittar da nayi ido hudu da ita..........

*♡Jeedderh♡*
[12/9, 18:27] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*30*
Chapter 36 · 0% Book details