← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 88

Sashe 17

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read

Sai Washegari na ba su Hafsy doughnut din dana kawo musu, tare dasu ma muka cinye shi a cikin mota. Yau Daddy da kanshi yazo daukata, yazo duba jikin Abbu ne. Sai da aka yi sallar la'asar muka wuce Kaduna, bakin daddy bai yi shiru ba a hanya yana ta bani labarin kirki da mutunci irin na Abbu, bai san cewa yanzu bana cikin mood din sauraren labarin Abbu bane, ko sunan Abbu aka ambata sai naji faduwar gaba, shi yasa yau nayi duk kokarin da zanyi wajen ganin na kaucewa haduwa dashi, nayi, sai dai dole sai da na ganshi lokacin da muke mishi sallama ni da daddy. Kaina na jinginar da jikin seats din da nake kai na lumshe idanuna kamar mai barci, hakan yasa daddy ya kama bakinshi ya bame har muka isa Kaduna.

Da dare Ni'ima ta kira ni, bayan mun gaisa take fada min wai Fahad dinnan ne abokin Bashir ya dame ta akan ta bashi number na, na tabe baki nace "kada kiyi kuskure bashi Ni'ima" tace me yasa? Nace ban gane ba? Waye a cikin ku bai san cewa Akwai wanda nake dating ba? Taja tsaki, dallah dating ko crushing?? Waye bai san cewa crushing din Muneer kike yi shi baya son ki ba?? Na dan dakata kadan kafin inyi magana, "Ramlah mai bakin Aku!! Ita ta fada muku koh?" daga can tace that doesn't matter ko kadan ai, ni ai zan bashi number! Nace cikin gatse, "ki bashi din toh, zaki gani ne" na katse wayar tare da jifa da ita akan gado. Muneer!! Na maimaita sunan, it's kinda strange. Rana bata taba fita ta koma ga ubangijinta ba ba tare dana tunana bawan Allahn nan a cikin raina ba, amma har ga Allah yau dai, yau gabadaya na manta da existing dinshi a duniya, Anya lafiya ta lau kuwa??! Tashi nayi na koma falo wajen su daddy muka sha hirar mu, sai dana fara hamma sannan na musu sallama na wuce dakina.

Da safe na ba daddy waya na nace a canza min screen din, Koda ya tambaye ni dalilin tsagewar ta cewa nayi faduwa tayi, to me zan ce mishi? Kafin azuhur sai gashi da sabuwar Samsung edge plus, nayi tsalle, nayi ihu na rungume shi, wayar da nake masifar so kenan sai dai bana so in takurawa iyayena da zancen wayar da nasan kudin abincin wani na shekara daya ne, shi yasa nayi shiru, sai gashi yau Allah ya bani ba tare dana roka ba. Daddy kam yasha addu'a ranar kamar bakina zai tsinke, haka nake ni kam, idan aka min kyauta sai in wuni ina wa mutum godiya. Mommy na cewa ta bada ayi fura don na kula Abbu yana so sosai, duk ranar dana kai fura ranar ita ce abincin shi har ta kare. Washegari na doshi hanyar Kano cike da tsaraba don sai da muka shiga shago na saiwa Hafsy dasu Qaseem sannan muka wuce, cike kuma da wani longing, longing to see someone wanda na ma rasa a wane matsayi zan ajiye shi cikin raina., abokin Babana ko kuwa Abokin Rayuwata??!

Aunty Mubeenah da wata kanwarta Shakirah kadai na taras a gidan, ina ga Abbu ya fita zagaya unguwa kamar yadda yake yi lokaci zuwa lokaci da er sandar taimaka tafiya, na durkusa na gaida su, Anty Shakirah ta mun sannu da zuwa har tana tsokanata da ina tsarabar ta tunda Allah yasa tana nan nazo. Matar tana da kirki, duk tafi sauran en uwan Anty Mubeenah da suke zuwa gidan, wasu idan suka zo ko kallon mutane basa yi balle su amsa gaisuwar su, wasu kuwa kallon mutane suke yi kamar kiyashi shi yasa nima bana kula da kurar data debe su. Dariya na dinga yi tana tsokanata, na ciro chocolate din kit-kat babba na bata nace ta kaiwa yara, na ciro wani hadadden turaren wuta na asalin en maiduguri na ba Anty Mubeenah inji Mommy na, ta amsa babu yabo babu fallasa, babu godiya ba komi kamar wadda ta bani ajiya, naji haushin abun ba kadan ba, na mike daga zaunen da nake na dauki jakar hannuna na wuce dakina. Kayayyakina na ciro na shirya komi a inda ya dace, na ciro fura da nonon da aka wa Abbu na Kai fridge na ajiye, daga kicin ina jiyo hirar dasu Anty Shakirah suke yi saboda a falo na biyu suke wanda yafi kusa da kicin din, Anty Shakirah ce take tambayar Anty Mubeenah mai yasa bata son turaren? Tace to mai zanyi dashi? Idan baki so ki bani ai ban rasa wanda zan ba bane, da sauri naji tace ina so wallahi, turaren ne yana da tsada naga gashi yana da wahalar samu shi yasa! Nayi kwafa ina girgiza kaina, wato kyauta ma tayi da turaren wutar da babu yadda ban yi da mommy akan ta bani in kaiwa Anty Haleemah ba mommyn taki ita ala dole sai ita, to ga abinda ya faru nan ai!. Dakina na koma cike da takaici ban jima da shiga ba naji hayaniyar su Hafsy a falo, da sauri na fita. Suna gani na suka kwashi ihun murna duk suka rugo, kowannen su so yake ya rungume ni, ni kam dariya kawai nake ina ihun su sake ni daga cakumar da suka kin kar su kayar dani amma ina! Sai da suka gaji dan kansu sannan suka sake ni, Abbu yana bayansu ya jingina bayan shi da kujera yana kallonmu cikin murmushi, da sauri na zube a kasa ina gaida shi, can kasan zuciya ta wani irin farin ciki yake mintsini na. Yaran naja muka tafi dakina tun kafin inyi abinda zan zo ina dana sani don wani sashen na zuciyata wai rada min inje in rungume shi yake yi. A daki na baza musu tsarabar dana kai musu, nan muka baje muka ci wasu a gun wasu kuma suka diba suka tafi daki lokacin da aka kira Magriba, ni da Hafsy kuma muka yi tamu a daki.
Chapter 17 · 0% Book details