← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 88

Sashe 28

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ana kiran sallah Mommy ta leko dakina tace in fito Daddy zai ja mu sallah, sai lokacin na tashi daga kwanciyar da nayi na shiga bayi na dauro alwala na fito, dogon hijabi na dauka na tafi dakin Daddy. Wani dan karamin dakine a cikin dakin shi wanda yake aiwatar da ibadojin shi a ciki, dakin lullube yake da darduma sai tashin kamshi yake yi, shelves shelves na littafan addini a gefe a shirye gwanin ban sha'awa. Daddy ya ja mu sallah, muna gamawa ni da Mommy muka dauko littafin Arrijalu Wan-nisa'u fil Jannah Daddy ya ja mana karatu har aka kira sallar Ishai muka yi. Muka fita zamu yi dinner amma abinci fa yace sam bai ga wajen zama a cikina ba, Mommy ta kalli yadda nake ta juya cokali a cikin Irish Supper data mana wanda yana daya daga cikin favorites dina, na tabbata saboda ni tayi shi amma na kasa ci, tace "Baby lafiyan ki lau kuwa kin kasa cin abinci?" Daddy ya dago yana kallona, cikin sauri na girgiza kai nace "m fine Mom, cikina ne a cike kawai" Daddy ya tsiyayo Pineapple and coconut juice da Mommyn ta hada ya miko min, na amsa tare da kaiwa bakina na kur6a, aikuwa har da lumshe idanuna saboda gardi da sanyin daya ratsa ni, da taimakon lemun na dan samu na kara tura abincin haka nan kafin na musu sai da safe na tafi dakina. Ina shiga na fara kokarin kimtsa kayana cikin wardrobe duk a kokarina na kauda tunanikan dake dankare a cikin raina. Na janyo handbag dita ina kokarin rataye ta a bags rack naji nauyi a ciki, cike da mamaki na zura hannuna ciki na fito da karamar jakar da Abbu ya bani da safe, a hankali na zauna a gefen gado tare da janyo dan karamin purple akwatin dake ciki, cike da mamaki na fiddo shi ina jujjuya shi a hannuna. Ina budewa na zaro idanu sakamakon wata siririyar sarka dana gani a ciki da dankunnenta har da zobe, sarka doesn't look that out of ordinary but daga ganinta kasan ba karamar sarka bace. Hannuna rawa ya shiga yi na rasa abinda zanyi, tashi nayi da dan akwatin a hannuna na fita falo, su Daddy suna zaune suna kallo duk suka bini da kallo, na zauna a gefen Daddy tare da mika mishi akwatin nace Abbu ne ya bani dazu, da mamaki Daddy ya karbi akwatin yana jijjiga shi a hannunshi yace "Shi Ibrahim din ne ya baki wannan sarkar?" na gyada kai a hankali, ni kaina na kasa yarda da hakan gani nake kamar a mafarki, Daddy yace "amma me yasa?" na jijjiga kai "nima ban Sani ba Dad kawai bani yayi" Mommy ta karbi sarkar itama ta dudduba, ta kalli Daddy tace "da alamun sarkar Babba ce fa Habibiy, Anya zamu karba kuwa?" Daddy yace "abinda nake tunani kenan exactly..." yace min "ki je daki ki kwanta, da safe zan tuntube Ibrahim din inji" nace "toh" na musu sai da safe na wuce dakina. Ina kwanciya barci ya kwashe ni, after all it has been one exhausting and stressful day.
Washegari Daddy ya dawo min da sarkar da Abbu ya bani, ban tambayi abinda ya cewa Abbu ba ni dai yana bani na bude na zura zoben a cikin yatsa na. A ranar sai ga Anty Ameenah ta kira ni, korafi ta min akan na tafi ba tare dana musu sallama ba, hakuri nayi ta bata akan cewa Lokaci ne ban samu ba, bata hakura ba sai dana dauki alkawarin cewa zan je gidanta musamman sannan. Bayan mun gama wayar shiru nayi ina kallon wayar a raina ina tuhumar kaina akan ba mutane false hope na ganina da ziyartar su bayan nasan cewa ba haka bane a cikin raina.

Nayi shiru akan gado duk kadaici ya ishe ni, a raina na raya da ace a gidan Abbu nake da war haka ko dai muna hira dasu Hafsy, ina kicin ina girki ko kuma muna wasa a gym kamar yadda muka saba kwanan nan idan bama aikin komi. Wayata na janyo na latso lambar Abbu, sai kuma na kasa danna mishi kiran, a raina ina mamakin kaina me zan ce mishi ne idan ya dauka? Me zan ce mishi ne dalilin da yasa na kira shi?? Kawai sai na maida akalar wayar zuwa ga Anty Mubeenah, ta shiga tayi ta ringing amma ba a dauka ba, shiru na bata mintuna biyar ko zata kira amma bata kira ba sai na kira wayar Abdullahi, cikin ikon Allah ya dauka, cike da doki muka gaida dashi. Nace ya bani Hafsy mu gaisa yace ai tana gida yau bata je makaranta ba, nace me yasa? Yace ai Tun jiya take kukan Ita lallai sai an kawo ta wajena shine yau ta tashi da zazzabi, a raina naji ba dadi don haka nace idan sun koma gida ya kira ni yace toh. Yana kashe wayar na kira Ni'ima, muna gama gaisawa tace "yanzu kuwa Babban Yaya ya bar nan" nayi jim ina kokarin yin maraba da sunan shi da naji ta ambata, haka kawai naji zuciyata ta dauki bugu da karfi, "umh ya su Mama?" nayi Kokari na kauda hirar Abbu da take kokarin sakowa amma duk da haka ban tsira ba, "next week ne bikin bude kamfanin shi a Beijing, how I wish zan samu zuwa" na hangame baki cikin mamaki nace "Da gaske?" tace wallahi kuwa. Nace "Masha Allah! Lallai zan kira shi in taya shi murna, na dade da jin labarin bude kamfanin wajen Bala Malam, ni nayi zaton ma an jima da budewa ashe har yanzu?" tace "kin san dama bude kamfani a kasar waje is not something easy musamman ga wanda yake ba dan kasar ba, don ma abokin aikin nashi haifaffen Beijing din ne shi yasa" na gyada kai. Tace "Hajiyar mu tayi mamakin tafiyar ki fa dazu da Babban Yaya yana gaya mata, tayi ta korafin baki masu bankwana ba" a raina naji babu dadi, sai lokacin naji ban kyauta ba, haka na baro Kano bayan Iyalan Abbu da Anty Haleemah babu wanda na wa sallama, nace "in shaa Allah duk ranar dana kara shigowa Kano zan zo in gaishe ta" tace better! Muka dan kara hira kafin muka yi sallama. Later in the evening Daddy ya dauke mu muka fita yawon gari, shiga nan fita nan har gidan Anty Uwani muka je acan ma muka yi sallar Magriba kafin muka juyo gida.

Sai dana gama shirin kwanciya barci misalin karfe tara na dare sannan na turawa Abbu text message, *"Abbu naji ance zaku bude kamfanin ku next week, Allah ya sanya Albarka da Alkhairi. And thank you for the necklace, it's beautiful, I like it!"*.
Chapter 28 · 0% Book details