← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 88

Sashe 74

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Wannan yace a cikin abinci kamar miya ko fate zaki zuba mishi yaci, manta kowa kenan. Ina mai tabbatar miki da cewa idan har yaci wannan maganin to wallahi sai dai uwarshi ta sake haihuwar wani, kin dai ga yadda mijin Umaimah (er autar su) yake mata, uwar shi ma yanzu sai Umaimah taso yake ganinta balantana wata banzar bazara wai ita kishiya, kema to haka zaki mallakeshi..., wannan kuma...." Saddiqa ta fito da wani ruwa a cikin kwalba tana nunawa Mubeenah, “...a cikin ruwan wankan shi zaki zuba mishi, shi kuma zai sanya mishi matsanancin son ki ne, ya zama babu wata ‘ya mace a cikin idanuwan shi sai ke ina fada miki, boka Saddar ya bani tabbacin a ranar zai dankarawa ita waccar banzar kishiyar taki saki uku, shi da kara aure kuma sai a lahira. Don haka ki kula sosai, ki bi komi a hankali yadda ya dace don hakan mu ya cimma ruwa kin gane?" kamar wata kadangaruwa ta gyada kai, “yauwa, ina turaren dana kawo miki last week nace kiyi tsuguno dashi?" Mubeenah ta gyada kafada, “turare? Na ma manta inda na jefa shi" Saddiqa ta maka mata harara, “wai ke banzar wani gari ce? Duk inda yake ki lalubo shi kiyi tsuguno dashi yau ba gobe ba, yaushe girkin ki zai fita?" tace “gobe da safe" tace “bamu da lokacin batawa kenan, yau yakamata yaci maganin, yayi wanka kuma ya kusance ki kina jina? Abubuwan nan da muke yi is all for u Mubeenah, kin dai san kaf danginmu babu mai kishiya sai waccan banzar yarinyar (Shakira) don kishiyar Umaimah hoto ce, don haka kema ba zaki biyo sahu ba kin gane??" Mubeenah tace “ehh".
Tayi murmushi, “yauwa., kudin aiki dubu dari da hamsin tashi maza ki dauko min" Mubeenah ta zaro ido, “dari da hamsin?" ta harareta, “to meye dari da hamsin matukar an samu biyan bukata?" Mubeenah ta gyada kai, “hakane kam. Sai dae babu kudi a hannuna sai dai idan Ibrahim ya dawo sai in amsa a wajen shi" Saddiqa ta yago hakura, “to babu damuwa, amma to dari biyu zaki tura min tunda dai nasan kema in kika tashi ba a dari biyun zaki tsaya ba" suka kwashe da dariya.
Nan taci gaba da kitsawa Mubeenah abubuwa har yamma ta gabato sannan ta mata sallama ta tafi bayan ta kwashi manyan atamfofi biyu da lesuna cikin kayan da aka kaiwa Mubeenah na fadar kishiya bayan ta gama kwashe musu albarka, ji fa!. Mubeenah ta dawo daga rakiyar ta ta tsaya ta leka dakin Abbu, tun jiya daya dawo daga gidan Nafeesah ya leka ya gaya mata ya dawo tare da fada mata ya raba musu girki kwanaki bibbiyu bata sake ganin shi ba. Yanzu ma baya nan gashi akwai maganganu da take so suyi.

Dakinta ta koma, magungunan da Saddiqa ta kai mata suna zube akan gado, ta zauna a gefen gado tare da kura musu idanu kamar wadda take muhawara, ta saki ajiyar numfashi tare da tashi tsam ta dauki magungunan. Toilet ta shiga ta zazzage su a cikin masai tare da yin flushing, dama turaren data kai mata Harira ta ba ta jefa shi cikin kwatami. Daya daga cikin manyan abubuwa da Mubeenah bata so kuma bata ma yarda dasu ba shine bin malamai da bokaye, tana mamakin yadda mata suke yarda da karerayi da soki-burutsun bokaye da malamai, a ganinta in kura na maganin zawo to tayi wa kanta mana?? Shi yasa tasu ta matukar zuwa daya da Shakira kanwar su, sam bata cikin harkar bin malaman da sauran en uwansu suke yi, ta kan ce ita tafi ganewa tayi yaki akan abu ta yadda idan ta mallakeshi zata yi alfahari da cewa saida ta share zufa ta sha wahala kafin ta same shi ba wai a ruwan sanyi ta hanyar bokaye da yan tsibbu ba, kuma gaskiyarta.

Tunda gari ya waye take leke-leke da zarya daga falo zuwa dakinta. Ta kula kwata-kwata ya daina zama a cikin gidan, tana mamakin inda yake zuwa cikin kwanaki biyun daya mata. Tana nan zaune a daki taji tashin muryoyin su dasu Qaseem wadanda suke hutun makaranta ranar, Sai data ji shiru alamun ya shiga dakinshi sannan ta tashi tsam!.
“ok baby sai na iso, kar ki manta anjima da yamma dai zamu fita in fara koya miki tuki" na danyi tsalle daga zaune din da nake, “yeyh! Abbu na, sai kazo. Please ka taho da wuri fa!" yayi er dariya, “missing me that much??" dariya kawai nayi na kashe wayar. Shima dan murmushi yayi ya ajiye wayar yaci gaba da shirya takardu a cikin brief case din shi.
‘Baram!! Karan sautin turo kofar dakin nashi kenan kamar tashin duniya. Tun kafin ya juya yasan ko waye ya shigo, haka take shigowa dakin babu knocking balle sallama, kofar dakin ma haka take turo ta, duk ranar data shigo a hankali to ranar nema take a wajen shi.
Bata yi magana ba ta coge a bakin kofa, shi kuwa yaki daga kai ya kalleta yaci gaba da abinda yake yi har ya gama ya rufe brief case din. Wardrobe ya bude ya fara ciro kaya, ta kankance idanu cike da masifa ganin yadda yake abubuwan shi kamar bai san da Allah yayi ruwan tsirarta a cikin dakin ba.
“Ibrahim! Ina so muyi magana da kai!" ta fadi kanta tsaye cikin izza, ya juya a hankali tare da kallonta. Wani malulun bakin ciki da bacin rai suka kawo mishi wuya, wasu pyjamas ne a jikinta daga ganinsu sun dauki lokuta ba a wanke ba, ta kawo wata hular beanie ta maka a kanta fara ce amma tayi bakikkirin ta dafe alamun ta kwana biyu, gashin kanta da yayi cukus-cukus a cikin hular ya maida ta kamar irin sababbin kamun nan. Ya hade fuska sosai wadda tasa ta shiga hankalinta ba shiri amma hakan bai hanata yin dibar albarkar data kawo ta ba. “Ibrahim mai kake nufi da nine, an kawo amarya ban ga kalarta ba, ka kama ka killace ta a waje guda saboda ita er goal ce, er nasiha ta hadin kai da naji mazaje na hada matansu waje guda su musu kai baka yi hakan ba, ka dawo daga gidanta kaxo nawa amma har ka gama kwanakin ka amma sau daya na saka ka a cikin idanuna, anya Ibrahim baka dauko hanyar da amaryar ka zata raina ni ba kuwa??" ya jingina da jikin wardrobe din yana watsa mata kallon uku-taro, sai data dire aya sannan ya ajiye numfashi, “killace amarya kamar yadda kika ce nayi sabida ta kai matsayin a killace ta dinne, Nafeesah ba er gwal bace er diamond ce Mubeenah. Kawo amarya gidanki damka amana ni na hana saboda ban ga dalili ba, ke kanki ya kike kula da taki rayuwar balle har ki kula da rayuwar er wasu? Maganar rashin gani na da baki yi ina ji kin manta ne, dama can muna daukar satika ma bamu ga juna ba alhalin muna gida daya yanzun ma ina ga ai bata canza zane ba koh?" tayi tsuru tana zare idanu, maganar daya fada haka take, ita kanta bata san dalilin sako maganar ba, kawai maganar has been eating her brain ne dole ta fade ta ko ta samu sawaba.
Tayi gyaran murya tare da cewa “whatever! Amma kasan dai saboda Allah baka kyauta ba, kuma naji ance ka sai mata manyan motoci har guda biyu bayan ni ka bar ni da tsohuwa ina fama, tun kafin tafiya tayi nisa zaka fara shimfida rashin adalcin da ake cewa dama a jinin ku maza yake?" yayi murmushi cike da takaici, dama yasan duk inda zata je ta dawo dai maganar kenan. Ya daga kafada, “mota yeah, ni na sai mata daya Daddyn ta ya sai mata daya, ina ce kema lokacin da aka kawo ki an sai miki mota?" “karya ne!" ta fadi cikin hargowa, “karya kake yi kai ka sai mata, motar da kake fada ai Mahaifinka ne ya sai min da kudinshi ba naka ba mai ya hana kai ka saya min da kudin ka ko kuma yanzu daka sai mata nima ka sai min idan ba rashin adalci ba??"
Ranshi ya baci sosai, ya sha daukar fiye da haka daga wajen Mubeenah, ya sha jin munanan kalmomi daga gareta duk yana shanyewa amma yau baya jin zai iya shanyewa. Yana da hakuri sosai, sai dai duk ranar da aka kai shi bango akwai matsala. Tun daga tsawar daya daka mata Mubeenah tasan cewa ranar ta tsallake layin hakurin Abbu. Idanunshi sun juye saboda bacin rai, “enough Mubeenah! Ya ishe ki, ya ishe ni haka nan. Mota bani na sai mata duka biyu ba amma da ace idan nayi hakan Nafeesah zata karba happily da wallahi sai na sai mata fiye da mota biyu. Kin san saboda me? Saboda Ina Son Ta!! Saboda tana kula da farin cikina, saboda ita kadai nake kallo in san cewa yes! Ina da mata, in san cewa akwai wani da zan ba umarni kai tsaye yayi, akwai wadda bata zartar da komi sai da yawuna, akwai wadda zan bugi kirji ince Matata ce in kuma nuna ta a koina cikin duniyar nan ba tare da fargabar zata muzanta ni ba. Saboda ita kadai ce take bani hakkina ba tare da na biya ta ko sisi ba, saboda itace matar da nake sa ran zata haifa min yara ta kuma shayar dasu ba tare dana biya ta kudin shayarwa ba!! Saboda... Nafeesah itace komi nawa!! Zaki ga laifina idan na sayi jirgin sama na damkawa wannan matar kuwa?".
Chapter 74 · 0% Book details