Sashe 57
Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read
Suka kalli juna kafin suka kalleni, Sadiya ta dage gira daya "me kenan?" "me fa??" na tambayeta ina wani fuskewa ni ala dole ban fahimceta ba. Tace “ki wani daina fuskewa malama, mun san abinda ke faruwa tsakanin ku biyun nan" na kada mata idanu innocently, “ni da wa??" ta kai min duka a kafada, “zaki sani ne maras M, ace kamar mu kuna cikin relationship da Yayan mu mu kasa sani?" na kallesu su duka biyun ina so in karanta yadda suka amshi zancen, ban karanci komi ba sai dai murmushin dana gani kwance akan fuskar su na farin ciki ne bana embarrassment kona takaici bane, naji sanyi ya lullube min zuciya, at least abotar mu dasu tana nan. Ni'imah tana murmushi tace “Sady ke kike wani tsayawa ma kina neman karin bayani, ni fa dama tun ba yau ba na harbo jirgin su ita dashi, they were making it obvious shi yasa ni ban tsaya jira a fada min ba nayi jumping into conclusion" na dan harareta cikin wasa nace “ni kar ki mun sharri wallahi" tace “ba wani sharri sai gaskiya. Irin kallon da kuke wa juna dama tun ba yau ba be it kuna cikin mutane ko ku kadai ne wallahi na soyayya ne, ai Anty Rahina tace an kusa yin auren" na dafe kirji ina zaro idanu, nace “su Anty har sun sani??" dariya suka saki suna kallona kamar wata kuntacciya dinnan, “Allah kina kwafsi matar Babban Yaya, tunda har muka sani ai dole su Anty su sani kuwa" na rufe fuskana ina diddira kafafuwa a kasa, “Ya Allah! Da wani idanu zan kallesu ni kam?" suka sake kwashewa da dariya har da tafawa, na hade fuska ina kallonsu, “this is not funny fa!" na fada in a serious tone don su san ba wasa nake yi ba, amma ko a jikinsu sai ma wata dariyar da suka kara sawa. Ganin zasu sa min ciwon kai naja Hafsy data fara gyangyadi a zaune muka koma kan spare gadon dake dakin na zauna ita kuma ta kwanta kanta a kan cinyoyina. Hira nake janta dashi duk don in janye hankalina daga shakiyancin dasu Sady suke min, cikin dan lokaci barci ya dauketa. Na maida hankalina wajen buga game bana ko kallon inda suke, har suka gama shiriritar su da tsara yadda bikin zai kasance suka yi shiru, dinner ma sai da aka tsara kala biyu, luncheon da parties kuwa wai har da Tea Party, fruits party, Arabian nights dasu Fulani day da tarkace, ina jinsu dai ban saka musu baki ba sai dariya da nake musu kasa-kasa, da alamu wani noti a kansu ya kunce kila saboda murnar auren Yayan su ne ko wani abu? Muna nan su Abbu suka dawo daga masallaci shi da Bashir, sallama ya musu ya matso inda muke ya dauki Hafsy a kafadanshi ni kuma na kara gyara zaman gyalena na kwashi wayoyin shi nabi bayan shi. Ya bude seat din baya ya kwantar da Hafsy, ya maida seat din ya rufe tare da jingina da motar yana kallona, na sadda kaina kasa ina dan tapping kafafuna a kasan, akwai wadataccen haske sosai a wajen shi yasa naji na kasa sakewa in kalleshi, tunda maganar auren nan ta shiga tsakaninmu na kasa sakewa in kalleshi sosai koda yake ko a da can dinma idan muka yi kallon ido da ido sai dai by mistake, balle yanzu. Yace “gobe in Allah ya kaimu zan samu Alhaji Babba yayan Alhajinmu da maganar zuwa a tambayo min auren ki, zasu kai kudin na gani ina so za kuma a saka ranar auren gabadaya” nayi shiru kaina a kasa, me zan ce mishi? Shi Abbu bai san irin matsananciyar kunyar shi da nake ji bane da zai dinga zama yana tattauna maganar aurena dani ba. Ya kara jingina da jikin motar yayi alamun tagumi, “ni ai shikenan tawa ta same ni kuma. Son maso wani nake yi ko kuma ba a shirya aurena har yanzu bane?" na saci kallonshi, ba karamar dauriya nayi wajen danne dariyar data taso min ba, ya wani yamutse fuska kamar yaron dake shirin fashewa da kuka, nace “me nayi ni kuma?" yace “baki son maganar auren mu mana. Da nayi sai ki wani hade fuska kamar wadda ake tursasawa, ji yanzu ma na gaya miki magana maimakon ko ameen ki ce shine kike wani sadda kai kasa" na girgiza kaina ina dan murmushi, Abbu da rigima yake wani lokacin kamar karamin yaro haka yake. Kwanan nan haka yake, gaba daya ya zama very open to me, baya shakkar fada min duk maganar data fito bakinshi, wata rana ta saka ni jin kunyar shi duk da cewa abin yana burge ni kuma na kula hakan yana kara ja na zuwa gare shi. Nace “to ameen Abbu" yayi murmushi, “datz you my Amour.... Amma tsaya...." na kalleshi, yayi frowning face “yaushe ne kika ce kin daina kiran sunana da wani Abbu? Na gaya miki Abbu na yara na ne ba naki ba" nace “ai nace zan daina fa! amma ba yanzu ba" ya wani langwabar da kai, “har sai yaushe?" nayi shiru, ya sake cewa “ko sai mun yi aure?" na gyada mishi kai, yace “ba laifi, ni ai bawan Allah ne I can wait" nayi dan murmushi, “datz you kaima.... Wai don Allah meye ma'anar Amour?" yace “Love in french" na sadda kaina kasa ina blushing, da gaske ni Love dinshi ce? Nace “amma sauran messages da kake tura min shima French ne? Me suke nufi?" ya girgiza kai, “naaa! Ba zan gaya miki yanxu ba, zan dai koya miki French din sai ki karanta da kanki. Idan muka yi aure ma a Kasar Faransa zamu yi honeymoon dinmu ai, kila kafin mu dawo sai kin koyi yaren sosai, sai mu dinga canza yare a gaban mutane abinmu koh?" na kai hannu ina rufe fuskata ina dariya, can kasan zuciyana kuwa fata nake ina ma zan bude ido in ga har watannin da suka rage in zama mallakin Abbu sun zagayo? Ya kara jingina da jikin motar yana murmushi “ke da kunyar nan taki kuna birge ni, sai dai it's way too much gaskiya, kiyi kokari ki rage ta ko kuma ni da kaina inyi wannan aikin...!" na kara dukunkune fuskana wannan karon a cikin gyale ma. Yayi dariya son ranshi kafin yace “ina tunanin raba muku gida ke da Mubeenah, me kike tunani?" nace “idan hakan yayi maka bani da damuwa da hakan nima" amma a can kasan raina ba karamin dadin hakan naji ba, har ga Allah dama can bani son zama gida daya da Anty Mubeenah har yanzu ina jin kaina guilty wani lokacin, har yanzu kuma ban san da wane ido zan kalleta ba balle har inyi tunanin zama a gida daya da ita, duk lokacin da nayi tunanin na kan ji hankalina bai kwanta da hakan ba. Yace “hakan ya min perfectly, zan samu inci amarcina cikin dadin rai da kwanciyar hankali abina. Amma na dan lokaci ne fa, don tuni an fara mana sabon gini" nace “sabon gini kuma?" yace “yeah, inda zamu koma da zama mu dukan mu har yaran da zamu haifa nan gaba. Da wancan gidan na gina shine a matsayin inda zan rayu da matar aurena ne, ban taba kawowa raina kara yin aure ba sai da kika shigo cikin rayuwata sannan na fara samun second thoughts. A yadda nake so kuma ki cika min gida da yara inda muke zaune yanzu ya mana kadan. Ina so iyalina su tashi da hadin kai ba tare da banbancin komi ba Nafeesah, ina fatan zaki bani goyon baya wajen ganin hakan ya tabbata?" muryar shi ta tabbatar min da cewa da gaske yake, tausayin shi ya kama ni Allah sarki Abbu na! Da haka yaso ya karasa rayuwar shi cikin takaici da rashin kulawar matar aure? Ta wani fannin sai na tsinci kaina da godewa Allah daya kawo ni cikin rayuwar su, ko babu komi nasan zan kawo haske cikin rayuwar Abbu kamar yadda name tabbata cewa shima zai kawo haske a tawa rayuwar. Nasan cewa shawarar daya yanke is not a bad idea, ni kaina nasan ba zan juri ganin rabuwar kan yayanmu ba kuma da yardar Allah ba zan bada gudunmawa wajen ganin rabuwar kansu ba kamar yadda wasu iyalan suke, na gyada kaina nace “In shaa Allah Abbu, zan yi iyaka bakin kokarina" yace “Nagode sosai Nafeesah. Allah ya bani ikon faranta miki rai kamar yadda kike iyaka bakin kokarinki wajen ganin cewa kin faranta nawa ran" na sadda kaina kasa ina murmushi, daya daga cikin halayen Abbu dake matukar burge ni kenan, saukin kai da saurin fahimta. A kasan raina kuma na amsa Addu’ar da yayi da “Ameen”.