← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 88

Sashe 21

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read

Juyi kawai nake yi na kasa barcin, na rasa abinda yake min dadi a cikin raina. In normal sense nasan cewa da ace wani ne ya min ihu da daga muryan da Abbu ya min yau sai naji bacin rai saboda ni fa na tsani kawai mutum ya dinga nuna he has control over me alhalin baya da, abunda nasan cewa koh a gida nake Daddy ba zai min kwatankwacin fada da tuhumar da Abbu ya min ba, yes! Daddy zai min fada amma ta cikin lumana da nasiha ba irin na Abbu ba. Amma me yasa? Me yasa ko kadan ban ji cewa Abbu bai kyauta ba a cikin raina?? Na juya daya gefen ina kallon wani frame, hoton mu ne ni da Hafsy, ni na dauke mu ya min kyau sosai shi yasa na kai aka wanke min shi. I was extremely confused a lokacin, kwata-kwata na ma rasa a wani matsayi na ajiye Abbu balle in yanke hukunci. I never, even in my dreams wai inyi mafarkin ajiye shi a cikin jerin abokan Baba na, to amma idan ba Abokin Baba na bane shi ba to waye?? Da wadannan tunanukan barci ya dauke ni cike da wadansu irin mafarkai marasa kan gado. Ranar har so nayi in makara sallar Asubahi, sai wajen karfe shida da rabi nayi sallah, ina gamawa na koma na sake kwanciya. Yatsun kafata naji ana ja, cikin barci na janye kafafuna na maida su cikin blanket tare da kara kankame pillow. Tafiyar tsutsa naji ana min a wuyana, da sauri na bude idanuna tare da hantsilawa kasan gado har ina dan buge kaina, na dago da sauri, yanayin fuskana ya canza daga harara zuwa na mamaki. Da mamaki nake kallon su, Ni'ima ne da Sa'adiya. Zaune suke a gefen gadon suna kallona, nayi tsalle a kansu muna shewa, sai da muka gama na zauna a gefen su nace "me kuke yi ne anan yammata?" ni'ima tace ziyara muka kawo, ko it's not allowed? Nace "ni na isa in ce? Amma da safe haka?" idanuna ya sauka akan agogo, karfe goma da rabi. Sa'adiya tayi murmushi tace "Abinci fa muka kawo wa babban Yaya." na Kalle su "Abbu?" Ni'ima tace "to da wa?? Funkasu ne da mijin taushe mai dadi wallahi, tashi kixo ki ci kafin ya huce" na sauka daga kan gadon ina cewa "yanxu kuwa" toilet na shiga nayi brush, na fito na bude wardrobe na janyo bakar BF jacket ta cotton na dora akan vest din dake jikina, na nannade kitson da aka min na daure da ribbon na saka hular beanie muka fita falon, dama nasan yara suna makaranta don haka ban yi mamaki da naga falon babu kowa ba, sai da muka shiga second falo ne na ga Any Mubeenah zaune akan kujera, muka gaida ta ni da su Ni'ima da alamun suma sai lokacin suka gaisa, ta amsa kamar ko da yaushe, babu yabo babu fallasa. Lamarin Anty Mubeenah sam ya daina bani mamaki, shi yasa bana ganin laifin dangin mijinta akan duk abinda zasu ce a kanta, tunda koma meye ai ita ta jawowa kanta. Ace kannen mijin auren ki wai kina amsa musu gaisuwa kamar wasu baki ko irin dangin nan na nesa? Kai ko dangin nesa ne ai ya cancanci ace ka dan nuna sanayya. Na saci kallon su Ni'ima da alamun su abun bai dada su da kasa bama. Muka nufi kan dinning muka zauna, har su na zuba mana funkasun muka fara ci muna er hira. Abbu ya shigo sanye da wata farar riga da farin wando, ya gyara sumar kan shi sai wani irin sheki take yi, da sauri su Ni'ima suka taryo shi suna babban bros! Da fara'ar shi ya tare su ya jingina kowaccen su da jikinshi yana kallonsu, "wato ku dai idan ba aiko ku aka yi ba ba a ganin ku sai a gida ko?" Sa'adiya tace "bros ai kasan halin Baba, baya bari muna yawo fa" yace "ba wani nan dadin baki, ai naji ance har weekend kuke zuwa gidan su Ameenah, wannan ba yawo bane ba kenan?" Ni'ima tace "kar ka damu bros, yau yini ma zamu yi anan" yace ban yarda ba, kwana zaku yi. Ni kam idanuna yana kansu, fadar irin burge ni din da suka yi bata baki da lokaci ne, ban san sun zauna ba sai dana ji muryar Ni'ima a saitin kunnena, "me kike kallo?" nayi firgigit na kalleta, "umh?? Babu komi" ta jefa min wani irin kallo alamun bata yarda dinnan ba, nayi saurin maida hankalina ga Abbu na gaida shi, fuska a cune ya amsa duk sai naji ba dadi, ba haka yake amsa min gaisuwa ta ba. Ji nayi abincin ma ya fita daga raina, na fara tsakura ina turawa a bakina ba don ina jin dadin abincin ba. Su Ni'ima kam hirar su suke yi da Abbu suna dariya. Sa'adiya ta dan tabo ni, na kalleta a sanyaye, cike da kulawa tace "you okay?" na gyada mata kai kawai, Abbu ya kalleni na dan lokaci kafin ya maida kallon shi ga Ni'ima. Anty Mubeenah tazo tayi joining dinmu itama, lokaci zuwa lokaci Abbu yana saka ta cikin hirar da suke yi da kannen shi amma bata cika maida hankali ba duk da nima suna sako ni amma sai dai kawai in danyi murmushi ko inyi nodding a haka dai muka gama cin abincin. Hirar su suka cigaba da yi, na tashi na hada kan kayan da muka 6ata na kai kicin. Kasa komawa inda suke nayi kawai sai na shige daki, Su Mommy na kira na hada mana video call, daddy ma yana gida don haka hirar mu muka sha sosai, na basu labarin bikin da muka je har hotuna da videos din da muka yi na tura musu. Ban yi kuskuren fada musu har dare nayi a wajen bikin ba wanda dalilin haka yasa Abbu ya mun fada kuma har yanxu yake fushi dani saboda nasan kuskurene hakan, kamar nayi kirari ne na dabawa kaina wuta. Su Ni'ima suka shigo dakin na wa su Daddy sallama, nan muka bude sabon shafin hira dasu.
Chapter 21 · 0% Book details