← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 88

Sashe 26

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

Juyi yake yi akan gado, barci yake ji sosai amma ko kadan barcin yaki zuwa. Gadon da yake Kai ya mishi fadi, gado ne wanda a kalla zai iya kwashe mutane biyar ba tare da wani ya takura wani ba amma kullum ta Allah shi kadai yake murzar shi, yana Juyi a kanshi, yana jin shi kamar wani mara galihu. Disappointedly ya sauka daga kan gadon, kan sofa yaje ya kwanta, yafi jin dadin kwanciya anan duk da cewa kafafun shi suna kan hannun kujerar ne saboda tsawon shi. Wani modem daya shigo dashi ya tuna ya baro shi a parlour, wasu muhimman bayanai ne a ciki ba shiri ya tashi ya fita, babu kowa a Cikin falon, wutar falon ya kashe yayi amfani da wayar hannunshi ya dauko Modem din. Kan three seats ya koma ya kwanta a parlour na daya, Family picture dinsu ya kurawa ido yana kallo. Ya gaji haka nan, Ya gaji da jiran canzawar halin Mubeenah, Ya gaji da kasancewa kamar wani marar aure alhalin yana da mata kuma yana da right din karo guda uku kwarara, yana bukatar rayuwar aure irin ta kowane normal mutane, rayuwa mai cike da soyayya da girmamawa ba irin rayuwar auren gidanshi ba, rayuwar auren da ba zaka taba ganin murmushi ko kafar matar auren ka a dakin ka ba sai idan tana bukatar either kudi ko bukatar namiji ta motsa mata, kai kuma naka bukatun ko oho! Yana ganin lokaci yayi da zai maida komi inda yake, maganar gaskiya yana bukatar mace ya kuma gaji da bin kan Mubeenah tana yankwana shi kamar wani mara galihu, Allah ya gani yayi iyaka Kokari da hakurin da zai yi. Yana nan kwance Cikin zazzafan tunani zai iya cewa ma barci ya dauke shi yaji karan bude kofar daki, a hankali ya bude idanunshi yaga Nafeesah ta fito daga dakinta, da mamaki ya bita da kallo a cikin ranshi yana tambayar ko lafiya? Yanayin tsayuwar da tayi tana tapping kafafunta a kasa nervously ga waya a kunnenta ya sashi cikin tunani me ke damun Nafeesah ne haka? A hankali idanunshi suka fara yawo a jikinta, duk da babu wadataccen haske a falon amma hakan bai hana shi hango surar jikinta cikin gajeren wando da vest din data saka, wani irin tension yaji yana building a cikin jikinshi babu shiri ya rufe idanunshi da karfi yana hadiyar yawu yana gayawa kanshi it's not right! A hankali ya sake bude idanun yana kara kare mata kallo yadda jikinta yake swaying halittun jikinta suna motsi suna kara tada mishi hankali, yana so yayi motsi yadda zata san da wanxuwar shi a cikin falon, but hell! He couldn't. God Forgive him but he's enjoying seeing her in that attire, making him go mad, making him want to just drag her and kiss her senseless may be yayi wani abun worst than kiss.....! Maganar da tayi cikin fushi da daga murya ne ya dawo dashi daga tunanin da yake yi, "Muneer you evil bastard!" yaji duniya ta tsaya mishi cak kamar an tsaida kowane wucewar minti da dakika, may be he was mistaken, ba Muneer tace ba, kila ba sunan Namiji ta kira ba, kila Muneerah tace kunnenshi yake gaya mishi Muneer. Ya sake lafewa akan kujerar da yake yana kara kasa kunne, "kasan ina son ka Muneer!! You know it all along amma what?! Aure??!...." da sauri ya saka hannu ya danne kofofin kunnenshi yana girgiza kai, no! No way!! Karya ne!!! Kwatakwata ya manta a ina yake balle yace ga abinda yake yi, wani irin rugugi yake ji yana mishi ihu a cikin kunnenshi, maganganu mafi muni da daci daya taba ji an furta a gare shi, maganganun da suka girgiza shi suka yi turning rayuwar shi up-side-down, Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un ya dinga nanatawa har yaji nutsuwa ta saukar mishi, maganganun Nafeesah sun matukar girgiza shi, the fact that tana son wata halitta, halittar ma jinsin Namiji, abu ne da bai taba zato ba, bai taba zaton cewa tana da wanda take so ba, bai kuma taba zaton cewa abun zai yi affecting dinsa sosai kamar yadda yayi yanzu ba. Yana jin lokacin data tsuguna tana kuka sosai a tsakiyar falon, he wanted to man up yaje ya rarrasheta sai dai a halin da ake ciki shima rarrashin yake bukata, yana ji kamar shima ya fashe da kukan ko ya samu yaji sauki daga azabar zafin da zuciyar shi ta dauka, har ta gama kukan ta tashi ta koma dakinta bai iya tabuka komi ba sai bin ta da kallo helplessly. Lokaci mai tsawo yana cikin wannan hali kafin yayi karfin hali ya tashi zuwa dakinshi, alwala ya dauro ya kalli Al-Qibla ya fara jera nafilah yana mai rokon Allah akan ya mallaka masa Abinda ya jima yana kwatanta nashi ne.....!.

☆☆☆☆☆☆☆☆

A hankali na bude idanuna da nake ji sun min wani irin nauyi marar misali, na kai hannu na dafe kaina da naji yana sarawa kadan wuyana ya rike shima na kai hannu ina dan taba shi, idanuna suka sauka akan agogo, karfe shida ta wuce, da sauri na tashi tare da daddabar Hafsy ta tashi, muka shiga bandaki muka yi alwala muka fito muka yi sallah, dakinta nace taje tayi wanka ta shirya nima na shiga na watsa ruwa, nayi iyaka Kokari na wajen mantawa da abinda ya faru Jiya da dare, bana son tunawa ko kadan. Na fito daga toilet din daure da tawul a kirjina, na tsaya a gaban mirror ina tsane lemar jikina, idanuna sun tasa sosai sunyi luhu-luhu, ni dama nasan za a rina irin kukan dana sha jiya, kayan kwalliyata na janyo na shiga shafe-shafen abubuwa amma duk kokarin da nayi idanuna basu da alamun dawowa normal dama-dama ma fuskata swollen din da tayi ya rage sosai, tsaki naja na janyo wet tissue na goge kwalliyar da nayi, nayi simple one ko janbaki ban sa ba, riga da zani na saka nayi simple daurin dankwali, na dauki jakata na jefa wayata a ciki ba tare dana damu akan in kunna ta ba. Shades na saka a fuskata wanda ya rufe idanuna da yawancim fuskata, na zura takalmi flat na fita. Yaran ne kadai a falon suna kari iyayen basa nan, naja kujera na zauna a gefen Hafsy yayin da duk suka bini da kallo, dan murmushi nayi kawai, suka gaida ni na amsa Hafsy ta jefe ni da tambayar "Yaya Nafee me ya samu fuskar ki kika sa glass?" sai da nayi gyaran murya saboda dusashewar da tayi kafin nace mata "idanuna suke ciwo, bana so in goga muku ciwon ido ne" ta gyada kai tace Allah ya sauwake Yaya Nafee, Kai kawai na gyada mata. Muka fara cin abincin a nutse, ni kam caccakar abincin kawai nake yi duk yadda naso da inci abincin abun ya gagara, xuciyata a cunkushe take sosai, takaici da bakin ciki ya cika min ciki har babu wajen da abinci zai shiga. Suna gamawa muka fita, hango bakar Matrix da nayi nasan cewa yau Abbu ne zai kaimu kenan, mamaki ya kamani ko me ya hana shi yin break ne?? Muka shiga cikin motar, as usual a baya na zauna. Muka gaida shi ya amsa cikin wata hargitsattsiyar murya wadda tasa na kalli fuskar shi sosai kamar wadda take so ta gaskata Abbu ne ko ba shi bane? Ban taba jin muryar Abbu a hargitse haka ba, wani hargitsattsen kallo daya watso min wanda ya kada min yayan hanji babu shiri na sadda kaina kasa, ina jin Hafsy fadi ba a tambaye ki ba tana gayawa Abbu wai ciwon ido nake yi ina tsoron kar in goga musu shi yasa nasa glass, harara nake jefa mata a kaikaice sai dai wannan shine ainihin abinda bahaushe ya kira da 'harara a duhu' saboda ba gani na take yi ba. Har muka ajiye su a school dinsu ban dago kaina daga sadda shi din da nayi ba, suna fita na tashi na koma gaba kamar yadda muke yi, Abbu ya tashi motar muka wuce su Hafsy suna dago mana hannu. A hankali yake jan motar kamar ba tafiya muke yi ba, ya juyo ya kalle ni a karo na barkatai tunda muka fara tafiyar, gudun da zuciyata yake yi ya cigaba da karuwa a duk wucewar dakika. Kamar daga sama naji ya jefo min tambayar da nake tsoron ya jefo min, "Are you ok Nafeesah???!"

*♡Jeedderh♡*
[11/29, 21:20] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*23*
Chapter 26 · 0% Book details