← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 88

Sashe 45

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 5 min read

"So sai kawai kika yi rejecting din golden opportunity like that?" cewar Ramlah. Zaune muke a lecture hall dinmu bayan mun gama lectures. Kwana biyu bana cikin natsuwata, walwala ta min kaura kamar yadda fara'a tayi kaura daga fuskata., a duk lokacin dana samu na kebance babu abinda nake yi sai tunani, Ramlah ta kula da yanayin da nake ciki yau dai ta rike ni sai dana fada mata abinda ke faruwa, ko babu komi naji dadin fada mata din da nayi. Tunda abin ya faru babu wanda yaji maganar, ni kadai nake juya abun a cikin raina. Fadar irin mamakin da Ramlah tayi ma bata baki ne, data hangame baki sai dana cika mata shi da popcorn sannan ta rufe. Na kai popcorn bakina tare da gyada kai, "babu wani zabi daya rage wannan Ramlah, kema kin sani" ta kura min ido, "akwai so many and n much more choices Babe, ke ce dai baki so zaba ba". Muka yi shiru na dan lokaci, ta sake cewa "wai ba kince kina son shi ba?" na gyada mata kai, "then why did you do it? Bayan kin san zaki kasance cikin damuwa?" na kalleta sosai, "Ramlah, ina cikin rudani wallahi" ta girgiza kai, "no! Ki kike confusing din kanki dai, wannan abu ne mai sauki da cikin kiftawar ido zaki magance shi. Kina son mutum, then marry him mana, meye matsalar ki wai? You once fall for the wrong person yanzu kuma right person din yana sonki kina gudu da kafafun ki? Me kike so ne?" nace "so, kulawa, zaman lafiya Ramlah" tace "A cikin abinda kika lissafo wanne ne ba zaki same shi ba wajen Abbu?" nace "duka..... Ban sani ba ko Abbu yana so na ko baya sona ba. Ban sani ko dangin shi zasu karbe ni ko ba zasu karbe ni ba, ban sani ko iyayena zasu yi farin ciki da haka ko ba zasu yi ba...." ta katse ni, "wait don Allah. Shi Abbu da bakin shi yace baya son ki?" na girgiza mata kai, "ko Kadan. Yanayin acting dinshi towards me ne yake nuni da hakan. Ki duba ki gani tunda muka yi maganar nan dashi yau an wuce wata biyu amma koda wasa bai kira ni, bai taba nuna yana sona ba, bai taba furta cewa yana so na ba, a haka zan aure shi kuma? To ince nayi auren me?? Bayan haka alakar shi da matar shi is not in a good condition wanda hakan ya saka ni zargin cewa saboda ita yake so ya aure ni...." na zayyane mata duk irin yanayin zaman su dana sani da challenge dinsu akan karo aure, tayi shiru tana saurare na har na dasa aya. "shine nake jin tsoron na amince dashi kuma daga baya in zo ina dana sani" Ramlah hararata take yi kamar wata wadda na kashe mata da, tace "kin san Allah? Da ba don ke bace? Da sai na dalla miki mari. Wai me yasa ke kullum tunanin ki daban yake dana normal mutane?" nima na harareta, "kin fara ko? Meye laifina anan to?" ta dafe kai, "saboda kin kasa fahimta. Sai me idan Abbu baya son ki? At least yana so ya aure ki which means ko yaya ne yana admiring dinki., kuma ko ba jima zai fada tarkon son ki girl balle ma na riga dana san tuni ya fada" nace "me yasa kika ce haka?" tace "yadda ya dinga kallonki with so much tenderness and affection in his eyes ranar dinner din su Ni'imah, ke ko ba wannan ba kallon da mutumin nan yake miki da gaske na so ne" na girgiza kaina, "I doubt it Ramlah" wayana tayi karan shigowar sako, na ciro ta daga cikin jakata tare da bude sakon bakuwar number ce kuma har da karin alamun + wanda yake nuni da cewa sakon daga wajen Nigeria ne, cewa aka yi., 'Let's have a talk later please, I'll call you nine pm on dot in shaa Allah. -Galadanchi' hannu yana rawa nayi niyar maida mishi amsa Ramlah tayi saurin rike min hannu, na kalleta "meye?" tayi rolling idanu, "haba babe! Bashi kamar minti goma mana zuwa ashirin kafin kiyi reply?" nace "ban gane ba? He sent me a message, let me reply please" ta kwace wayar daga hannuna, "kin ce kin fada mishi baki son shi, then me kike so yayi tunani yanzu? Ya turo miki text, within a second kin maida reply as in you care dinnan, kinsan Allah mazan yanzu ba a musu haka koda kuwa wanda yake son ka ne balle ke da kike ikirarin kina son shi" na sadda kaina kasa, "Ramlah kin san halina sarai. Ban iya boye so ba kamar yadda bana iya boye ki, bazan iya yiwa Abbu haka ba" tace "at least try mana. Be like the classy girl you are, wannan yana da banbanci da son da kike yiwa normal mutane, ina gaya miki ta haka ne kadai zaki gane yana son ki ko baya son ki" na gyada mata kai a hankali. Ta dafa kafadata tana dan bubbugawa, "ban san irin son da kike mishi ba Nafeesah, amma zan baki shawarar ki dinga Addu'ah. In shi alkhairi ne a gare ki Allah ya baki shi, idan kuma ba alkhairin ki bane Allah ya canza miki da mafi Alkhairi" nace ina yi wallahi Ramlah, tace sai kici gaba dayi. Na gyada kai, "in shaa Allah, nagode sosai. Baki ji dadin da naji ba dana gaya miki wallahi" tace "kar ki damu, what are friends for after all? Naji ance BUK zasu fara registration da lectures dinsu next month, haka ne?" hirar mu ta koma ta makaranta, da yake ita university of Abuja zata koma, mun dan kara mintuna kamar ashirin muna hira kafin muka mike, na mata sallama na wuce gida ita kuma ta wuce hostel.
Chapter 45 · 0% Book details