← Book details Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 88

Sashe 41

Ni Da Abokin Baba Na Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washegari aka yi Walimah anan farfajiyar gidan Anty Ameenah. Washegari kuma aka daura aure da dare muka tafi wajen dinner. Kamar da wasa ina juyawa daga seat din da nake zaune na hango Harith da Ikram a zaune, na zaro idanuna ina kallonsu daidai lokacin da shima ya juyo, na mishi alama da hannuna alamun "ya aka yi haka?" ya danyi shrugging kafadar shi. Wayata tayi kara a daidai lokacin da sauri na daga naga Ramlah ce take kira, na daga da sauri, tace in same ta a parking lot Fiancé dinta zai tafi mu gaisa. Nayi excusing kaina wajen wasu daga cikin abokan su Niimah da muke zaune a seat daya dasu na fita. A can parking lot na same su, muka gaisa da Ayan saurayin Ramlah, (Ban fa ce na Ummu Maryam da Ihsan ba... Don kar kusa Husna tayi daidai da naman jikina, tamm). Anan na baro su su gama sallamar su. A hankali nake tafiya saboda heel din dake kafa ta, gashi dinkin skirt din dake jikina ya dan matse ni somehow don haka bana iya daga kafata sosai inyi tafiya. Kawai ji nayi an ja hannuna anyi gefe dani, na daga baki tun karfina zan kwala ihu, aka sa wani tattausan hannu akan bakin nawa ta yadda babu yadda za ayi ihun da nayi niyar yi ya fita......

*♡Jeedderh♡*
[12/15, 02:34] 💖💖💖💖💖: *NI DA ABOKIN BABA NA....!*

*©°•Jeedderh Lawals•°*

*33*

"What the....... Harith meye haka?" na fada ina hararan shi, ya sake ni tare da jingina da mota. "ina so ne muyi magana in secret, can idanun mutane yayi yawa shi yasa" nace "shine kuma sai ka tsorata ni?" ya daga kafada, "sorry ok! Ikram tana hango mu fa, muje" muka fito daga wajen da yaja mu muna dan dariya muka tsaya a daidai inda zata dinga hango mu sosai, Harith ya kai hannun shi kamar zai yi cupping din fuskata., "Nafeesah?" Husky voice din Abbu ya sankame ni a wajen, bayan kamar sakan goma na juya a hankali kuma cike da tsoron irin fahimtar da zai mana. Tsaye yake a gefen mu sanye da shadda light brown da hula a kan shi, kallonmu yake daga ni har Harith din cikin alamun tambaya da kuma bacin rai. Take naji jikina yayi sanyi, na kalli Harith da a lokacin hankalinshi ya tafi da Ikram wadda ta juya zuwa cikin hall din kamar tana share hawaye daga karshe ma sai ya bi bayanta. Na kalli Abbu da har lokacin kallona yake yi, idanunshi suna fitar da wani irin tartsatsin abu cike da alamun bacin rai, ya dan matso kusa dani yace "me kike yi anan?" na dan ja baya kadan saboda kusancin dake tsakanin mu kafin in ce "umh, dama na fito ne zamu gaisa da saurayin......" wani irin kallo daya watso min ne yasa nayi shiru jikina ya dauki rawa, me ke damun Abbu ne yau? Na daure na karasa ".... Ramlah kawata" sai lokacin na ga ya dan sassauta muryar shi idan ban yi mistake bama har da sighing yayi softly wanda na lura dashi ta yanayin yadda kirjin shi ya sauka a hankali. Ya katse shirun da muka yi ta hanyar cewa "kin yi kyau sosai yau.... Kodayake kullum ma haka kike" nace "hmmm" kawai saboda gabadaya na rasa abin cewa it's really unlike him. Na sha jin kalmar yabo daga gareshi amma ban taba jin makamanciyar wannan ba don haka naji abun so strange. Yace "zaki koma cikin hall din ne??" na gyada kaina da sauri, yace "k, ni zan koma ne yanzu" na kalli agogon hannuna kafin in kalleshi, "karfe tara ne fa kawai Abbu zaka tafi tun yanzu" yayi er dariya data saka ni shagala da kallonshi, "ban cika halartar ire-iren wadannan abubuwan ba Nafeesah.... Wannan din ma ya zamar min dole ne, naso ganin wani very badly kuma babu hanyar ganin nashi sai ta nan shi yasa" na gyada kai kamar na fahimce shi, sai dai maganar gaskiya na kasa processing maganganun shi a cikin kaina, babu abinda nake fahimta a lokacin irin daddadan kamshin turaren shi dake tashi da yadda zuciyata take bugu. Ya zura hannu a cikin aljihu ya ciro rafar kudi sababbi kar dasu ya miko min, naki saka hannu in karba har sai da yayi magana, "kudin liki ne ba wani abu ba, karbi" da sauri na hau girgiza kaina, "ina dasu nima Abbu ka bar kudin ka" ya hade fuska "akwai abinda na taba baki a duniyar nan ba tare da kin min gardama ba kuwa?" nace "Abbu Allah ba gardama bace, kawai akwai kudin likin a wajena ne nima" yace "to tunda na baki ai sai ki amsa koh?" na bude baki zan yi magana ya sake hade muryar shi, "Nafeesah karbi kudin nan kafin raina ya baci fa" yana iya? Sai kawai na saka hannu biyu na karba har da dan dukawa nace "Nagode sosai Abbu Allah ya saka da alkhairi" yace "Ameen.... Go back" ba musu na mishi sai da safe na wuce, ina jin idanun shi a kaina har na shige cikin hall din. Na koma wajen su Ramlah na zauna, lokacin da aka kira amaren suka fita wajen rawa muma muka tashi muka je muka fara liki. Sai sha biyu saura aka tashi daga wajen dinner dinnan, an daiyi komi lafiya an gama. Kafin mu isa masauki sai wajen karfe daya aikuwa mun sha fada sosai wajen Anty Ameenah kamar me! Washegari aka kai Amaren gidajen su na aure, ita Sa'adiya tana Lamido Crescent Ni'ima kuma suna Zoo road. A gidan Sa'adiya ne muka hadu da Ikram, mun gaisa da ita sama-sama tana ta wani shan kamshi ni kuwa ina mata dariya a ciki don nasan dalilin hade fuskar, sai a lokacin naji ashe cousin din mijin Sa'adiya ce. A washegari naso komawa gida Anty Ameenah tace ina! Ai sai na cinye sati daya din da aka bani daga gida, ban yarda da gaske take ba sai data dauke min jakar kaya ta kulle a bedroom dinta, ni wallahi dariya ma ta bani. Dole haka nan na zauna, dama kwana biyu suka rage min. Naje gidan Anty Haleemah da Anty Raliya, washegari kuma direban gidan Anty Ameenah ya kaini gidan Abbu. Da yake ranar Lahadi ce na samu Abbu a gida, na ga tarbar data bani mamaki kam. Tun daga bakin gate su Hafsy suka taro ni suna ihun murna har cikin falo. Gidan yana nan kamar yadda na tafi na barshi, matar gidan tana uwar daka. Na shiga har ciki muka gaisa na koma falo wajen su Hafsy, nan suka fara ajiye min tarkacen kayan makulashe muka shiririce anan muna hirar mu har aka kira sallar Axuhur, Abbu ya fito daga dakinshi sanye da jallabiya ruwan toka da alamun masallaci zai je, na zamo daga kan kujerar da nake zaune na gaida shi, ya amsa tare da wuce mu su Abdullahi suka tashi suka bi bayan shi ni da Hafsy kuma muka shiga dakinta muka yi tamu sallahr.

Abbu ya mana odar abinci daga restaurant muka ci namu ni da Hafsy a daki. Ina nan a gidan har yamma tayi, direban Anty Ameenah ya dawo daukata, na je nawa Anty Mubeenah sallama muka fita zuwa inda direban yake jirana cikin rakiyar su Hafsy. Abbu yana zaune akan kujera da laptop a gabanshi akan dan karamin table yana ta danne-danne a ciki. Na fasa shiga motar da nayi niyar yi na taka zuwa gaban shi, ya dago ya kalleni yana murmushi. Na sadda kaina kasa cike da kunya, "Abbu zan wuce" ya gyada kai, "gobe zaki koma koh?" na gyada kaina, yace "nima ina so zan shiga Kadunar gobe in shaa Allah. I'll drop you off goben, that is idan tafiyar tana nan" na kalleshi fuskana dauke da alamun tambaya sai dai na basar, ai yace akwai abinda zai kaishi kuma ma cewa yayi sai idan tafiyar tana nan ne sannan zai ajiye ni. Nayi murmushi nace "to Abbu, na tafi" ya gyada kai yana jifana da murmushin nan nashi, "ok Nafeesah! Mun gode da dariya" na danyi murmushi tare da juyawa na tafi. Muka sake yin sallama dasu Hafsy na shiga mota muka tafi, daidai saitin Abbu na dan saci kallonshi, idanunshi suna kaina yana kallona da wani irin yanayi da kallo with so much affection, nayi saurin sadda kaina kasa ban dago ba har sai da muka bar layin.

*******
Chapter 41 · 0% Book details